SAWUN BARAWO CHAPTER 1

SAWUN BARAWO CHAPTER 1
SAWUN BARAWO CHAPTER 1 Da fiiito ya shigo gidan kamar kullum, haka nan kuma ba tare da ya dubi kowa dake falon ba yanemi matsugunni a gefen kakar su yazauna, kasancewar ta halitta d’aya dake k’aunar shi a duk fad’in gidan nasu. 1 “Kukus ya akayi neh”? Naga fuskar ki a da’kuneh”? Ya jere mata tambayoyin sakamakon ganin yanda tai jigum takasa koda shafo kan shine kamar yanda ta saba matuqar suna zaune guri guda. Ganin takasa koda kallon shi neh yasaka shi watsa idanuwan shi ga sauran halittun dake zaune a k’aton falon gidan nasu. Tab’e bakin shi yayi cike da halin ko in kula bisa alamun tashin hankali daya fuskanta daga dukkanin rayuwakan dake zaune a falon. Ganin atmosphere (yanayin) da gidan ke ciki yasaka shi mik’ewa da niyyar komawa inda ya fito, ba tare da yak’ara kallon kowa ba yamik’e da niyyar ficewa daga falon. “Mara mutunci ina kake tunanin tafiya”? Ya tsinkayo muryar mahaifiyar shi na fadi cike da masifa. Batare da ya kula da maganar ta ta ba yak’ara sauri domin ganin ya fice daga…