RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 11 RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 11 Ture Suraj yayi tare da zuwa ya dauko rigarsa ya nufi sassan su, duk suka bishi da kallo, Tsoho ya kalli Samirtare da miqa mai wayarsa yace kiramin Dr Munnir, hannu na rawa Samir yayi dialling no din, ringing daya ya dauka ya miqa ma tsoho, Allah ya qara ma tsoho tsawon rai, Dr muna lpy? Ya amsa, yauwa dan Allah kazo ka duba min yaran nan, yace toh gani nan zuwa, Tsoho yace kowa ya tafi sashensa. Zayyad ya kama suraj ya kaishi dakin Ama, aka watse. Ba ajima ba Dr yazo, ya duba Suraj, ya bashi pain reliver Tsoho yace aje a duba Jawad, ko da Dr yaje sashen hajia Babba korarsa tayi tace basa buqatar likita munufukan banza.. Har kwana 2 shiru kakeji, kowa yayi zaton Tsoho zaiyi magana akan fadan shekaranjiya qala bece ma kowa ba, kamar baayi ba, Be qullaci kowa ba, ko da Zaid yazo gaisheshi be nuna mai komai ba faramfaram, yana mai wasan kaka da jika, har suna sa ran Tsoho zai masu magana amma be ce komai ba. Hajia Babba ji take da Zaid, duk cikin jlkoki tafi y…