WATA SHARI'A CHAPTER 22 KARSHE WATA SHARI’A CHAPTER 22 ‘K’ARSHE’ “A bisa shaidu da hujjojl’ da suka gabata, kowa yaji yanda mai laifi ta amsa laifinta da bakinta, sannan kuma…” shiru alk’ali yayi kasantuwar tari da yaci karfin YB, Sosai yake tarin hardajini ke fita daga bakinshi, Cike da tausayi kowa ke kallonshi, Baifi minti goma a wannan halin ba rai yayi halinshi, Da k’arfi iyayenshi suka d’auki salati had’e da kuka, dama sun san haka na zuwa saboda yanayin ciwonshi babu alamar zai tashi ko kad’an. An d‘auki kusan awa d’aya da mutuwar YB harma an tafl da gawarshi Jalingo sannan kotu ta sake zama. “Kotu ta tabbatar da cewa Salmah ita ce ta saka akayima Aishatu fyad‘e, bayan nan kuma tasa an kashe mata ‘yar uwa wadda a dalilin haka babanta ya yanke jiki ya fad’i ya mutu, Indiyawa sunzo zasu duba lafiyar dumbin al’ummah wanda a cikinsu harda Amrah k’anwar Aishatu, dalilin saceta da Salmah tasa akayi yasa harlikitocin suka k’araci zamansu suka koma k’asarsu, Salmah tasa an sakawa gidansu Aishatu wuta har ya k’one k’ur…