WATA SHARI'A CHAPTER 20 WATA SHARI’A CHAPTER 20 ‘KOTU’ Kotu ta cika mak’il dan zan iya cewa duk zaman da sukeyi babu wanda al’ummah suka halarta sosai kamarshi, Saboda sosai Alhaji Abu Abu ya gayyato mutane dan ya tabbatar dasu zasuyi nasarah, tunda dai yasan su Barr. Umar basuda wata shaida saisa suka canja salon shari’ar, kuma ma canjin salon da sukayi bai amfana masu komai ba saboda gashi sunyi takarda wacce taci uwar original one d’in. Mai gabatar da k’ara ne ya tashi ya gabatar sannan alk’ali yace “Kotu najiran Barr. Sultana domin taci gaba daga inda ta tsaya”. Tasowa tayi bayan ta gyara daidaituwar rigarta ta iso inda Ummimah da Gentle suke, “Kotu na son ganin Dr. Khalid idan yana kusa, ya fito da takardar asibitinshi kamaryanda yayima kotu alk‘awarin zai kawota yau”. Tasowa yayi cike da confidence, takardar ya mik‘ama Sultana ta duba sosai, saida gabanta ya fad‘i saboda babu wanda zai ganta yace bata kirki bace, Ganin reaction d’in fuskarta yasa Barr. Sa’eed sakin murmushin mugunta sannan ya kalli Barr.…