WATA SHARI'A CHAPTER 15 WATA SHARI’A CHAPTER 15 A Katsina kuwa Umar ya gama maganar komai yanzu sunajiran ranar shiga kotu ne kawai, Ummimah yanzu ta dan samu kwanciyar hankali amma ba sosai ba, Saboda gani take yanzu wannan itace damarsu ta karshe idan har basuyi nasarah ba tofa shikenan, Addu’ah ta rika sosai sannan kuma mamanta ma tana tayata. Ana gobe za’a shiga kotu ne Haydar ya fara zazzabi, Sosai jikinshi yayi zafi sai rawar sanyi yakeyi, Matukar tashin hankali Sultana ta shiga saboda tunda take da Haydar bai taba yin zazzabi mai zafin wannan ba, ya makalewa Safiyya da ita kawai yake yarda, Harta da ita Sultana d’in baya yarda k0 Umar babanshi. Hakan yasa daren ranar ya nacewa Safiyya yace lallai sai tare da ita zai kwana, Babu yanda Sultana batayi dashi ba akan ya kwana tare da ita amma sam yaki yarda harda su hawaye, Ganin yana neman ya fasa mata kuka yasa ta mikawa Safiya shi tace ya kwanta tare da ita. Har sun kwanta Sultana taje d’akin Hafsa ta d’auketa saboda bai kamata Hafsa ta kwana ita kadai a …