WATA SHARI'A CHAPTER 14WAT

WATA SHARI'A CHAPTER 14WAT
WATA SHARI’A CHAPTER 14 Saurin mikewa Umar yayi ya tari gabansu babu haufin komai haka kuma babu ko alamar tsoro a tattare dashi, Kallonshi daya daga cikin matan tayi tare da kara bata fuskanta. “How dare you malam? Ka barmu akan aikinmu muke” ta fada cikin hausarta da bata kware ba kasantuwar ba bahausa bace, mini skirt din dake bisa makeken kugunta kawai ya isa ya tabbatar da cewa ba musulma bace. “Hukunci bai yanku ba saboda zamuyi apeal, idan baki yarda ba zaki iya zuwa ki samu alk’ali kuyi magana dashi, bakida hurumin da zaki wani kwaso jiki domin kama Ummimah ku kaita prison, so you better to leave this place because you are just wasting your time, babu inda zaku tafi da ita” Umar ya fada cike da zafin rai. Jin maganar da Umar yayi yasa ta sauke hannun dake rike da handcuffd’in, Juyawa baya tayi hakan yasa suma sauran suka juya, tunda suka tafi basu sake dawowa ba. Ummimah kuwa har yanzu bata farfado ba, tana mamaki baki daya hankalinta ya tashi, bata fatan ta rasa ‘yarta kamar ya…