TSANGAYAR MATI CHAPTER 9 TSANGAYAR MATI CHAPTER 9 “Ke dadina dake jahilci kwarankwatsa dubu, haba ai ko karamin yaro yasan ruwa ba a sheka mai Zobo a zuba Sugar shi kenan ya zama lemo, batun lalle kuma kin manta Inna da shegen san fadanci kamar matar Bawan Sarki?Ai kawai kururuta mata kai zakiyi harta sake ta baki kafar ki kunsa. ” Nene tayi shiru kamar mai nazari, sai kuma ta gintse fuska ganin Fadime ta Fito zuwa makewayi. “Shegiya kai da wata fuskarta kamar taunanniyar gyada, Allah Abule yadda naki jinin Matar nan banki a cemin karta fito raye daga makewayin nan ba , bani zoban ki gani duka gidan zan hada idan yaso in bata gani sai najuye maganin” Ta fada tana wartar ledar zobon da Abule ta riga ta siyo. “A’A hankali dai Nene dan kadan yace a zuba saboda karfinsa.” Ta balla mata harara “Wallahi duka zanjuye idan za a sha giya asha ta dubu Abule!” Ta fada tana mai ficewa daga d’akin. Kai tsaye madafi tayi ta dauko kwanon sha tajuye zobon, ta tuttulo ruwa daga tulu ta sheka bisansa ta zuba Sukari wadatacce ta…