TSANGAYAR MATI CHAPTER 12 TEND QARSHE

TSANGAYAR MATI CHAPTER 12 TEND QARSHE
TSANGAYAR MATI CHAPTER 12 THEND QARSHE BAYAN WATA GO MA Rayuwa ta mika a gidansu Mati, abubuwa da yawa sun faru ciki harda dawowarsu Nene bayan sunyi Bikon Mati sau kusan goma. Wanda Nene sai da ta koma yini a gona gun Mati tsaban son ta koma dakinta. A rana sai tai wanka sau hudu ko biyar. Goge hakora kuwa masu sai da gawayin kauyen sai da suka shaidata, haka ma masu Gishiri. Saboda tsabar tsafta sai da ta koma yawo da tsumma tana gage kafarta idan tai kura. Wannan fa duk shawarar kawarta shafa ce. To haka ma ga Abule itama sosai ta nutsu dan har dan abin kwalama take kaima Mati gona. Musamman ma Kundun Kaza da ta san yana so. Karshe dai ya mai dasu. A daren Inna ta tarasu da tata nasiharta nunamusu laifinta ne tare da neman gafararsu. “Haba Inna, ta ina kika zama mai laifi? Mu keda laifi mu yakamata mu nemi gafara.” Fad‘in Nene kenan tana mai k’arashewa da sheshshek‘ar kuka Fuskar Inna cike da damuwa ta girgiza kai bayan ta k’aremusu kallo gaba daya har Matin tana mai shafa kanjikanta…