RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 7 RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 7 Sun gama exams qarfe 12 suka dawo gida, Maysah ta shiga wanka, taci abinci, ta fito da sauri tana yana gyalenta na afta dress, ta kalli mamarta tace Amma naje gurin tsoho, cikin hausarta, akwai dambun name a kitchen ki kai mishi, da sauri ta shiga kichin ta dauko, ta nufa Sassan tsoho.Ta shiga dakin da Sallama, aka amsa ta, ba shi kadai ke dakin ba su biyu ne. tace tsohona ina wuni ya ce cikin sake fuska, Ruma kina lfy? Ya exams? Lafiya Alhamdulilahi, ta kalli wanda suke tsaye tare tace Yazayyad ina wuni yace lfy lau Ruma tayi murmushi, Tsoho yace ki diba bedside na nan tun da safe babanki ya kawo man newspaper nace sai kin dawo zaki karanta man, ta miqe cikin yanayinta ta nufi dakin Tsoho, Zayyad ya bita da ido, ta dauko jaridar ta matso da sofa ta zauna ta shiga karanta mai newspapern nan cikin qwarewa da muryar ta mai dadi. Lumshe ido zayyad keyi sakamakkon jin muryar ta dake ratsa jinin jikinshi cikin kwanyar kansa.Nan take zuciyarsa ta kamu da son Rumays…