NAYI GUDUN GARA CHAPTER 42 THEND KARSHE NAYI GUDUN GARA CHAPTER 42 THEND KARSHE Wata biyu da haihuwar Twins custome suka saki kayansu ramadan. Fari Clki kamar me ramadan keji. Cikin wata daya komai ya fara dawowa suka fara farfadowa. Gidan ramadan ya zamo gida na fahimtar juna da kwanciyar hankali ga matansa Dashi kansa. Ladifa twins basa bata wahala sosai! saboda an samo wata babbar mace mai kulawa dasu, tana zaune a falon safna data tashi. Wanda a lokacin kuma yar uwan hajiyarta ta tafi. Ramadan da ladifa soyayya suke sha kamar basu suka ajje su fuad da twins ba. Dan yanzu ramadan har so yake ya nunama ladifa kulawa, dan ya dada wanke kansa Akanta, bangaren laila ma suna zaune lafiya tana mai ladabi yanzu, kuma itama yana ji da ita yanzu, saboda tayi hankali tana yin abinda yake so tabar kuma wanda ba yaso, sai dai zafin zuciya da dan fada wannan kuma halayyar tane. Ladifa na tsaye a falon ramadan tana fesheshi da air freshener . Tana sanye da doguwar riga yadin cotton mai kyalli Kalarja. Zip din rigar agaba aka yi shi, aka…