NAYI GUDUN GARA CHAPTER 41

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 41
NAYI GUDUN GARA  CHAPTER 41 Ta dade tana kuka sannan ta tashi ta shiga hada kayanta.  Ladifa ta dade a zaune sai da taji daidai sannan ta hau samanta, laila kuma ta shiga dakinta..  Duk wasu muhimman kayanta saida ta hada sannan ta tafi.  Tana zuwa gida ta shiga dakin mamanta. Allah yaso babu kowa a tsakar gidan. Maman na zaune tana kulla wasu abubuwa a leda ta ce “safna daga ina haka?.”  Safanar ta zauna ta fara hawaye “ya sakeni.‘  Wani irin zabura tayi, taja da baya tace “kalu innalillahi wa inna ilaihi rajuun,‘ yau naga ta kaina, shi kenan makiya sun sakoni a gaba, yanzu wannan ma sai da kika kashe shi ya mutu.‘  ta kalleta tace “mama kiyi kasa da muryarki karsu ji dan dariya za ai mana.” Zama tai tace “to ke meya hadaku?.”  Ta gaya mata komai karya da gaskiya tace ‘cabdi yanzu akan matarsa ya sake ki? Ai da kin hakura kin zauna talaucinsa ai ba lalle ya dore ba.‘  “Mama ni ba zan iya zama ba wallahi na taso cikin talauci kuma na koma masa ba.Gaba gaba ma gidan sai mun barshi, dan fa baki g…