WATA SHARI'A CHAPTER 9

WATA SHARI'A CHAPTER 9
WATA SHARI’A  CHAPTER 9 Duk kukan da mukeyi baisa mutanen sunji tausayinmu ko daya ba, Cike da rashin imani suka ringa watsi da baki d’aya kayakinmu, Ga gawar Afrah cikin buhu ga kuma Baba da yake kwance baya ko alamar numfashi,  Kukanma nemanshi nayi na rasa, sai mama daketa ambatar sunan baba amma har yanzu ko alamar motsi bayayi.  “Ku tashuwa min daga k’ofar gida bana son ganinku, idan ba haka ba kuma a  wulakantaku cikin unguwar nan” mutumin mai gidan hayar ya fada cike da izgili da gadara.  Mutanen da suka kawo gawar Afrah d’aya daga cikinsu yace  “Kai kuwa bawan Allah ka tausaya masu mana, bakaga hakinda suke ciki ba? Ka barsu suji da d’aya mana, tunda dai kasa an fitar masu da kaya ai sai ka shafa masu lafiya haka, tunda mai gidan nasu ma gash!” nan kwance bama asan halin da yake ciki ba”.  A wulak’ance yace  “Babu ruwana da halinda suke ciki, gidana kawai na sani kuma na basu minti goma  subar harabar nan, idan kuma basu bari ba duk abunda na masu su sukaja”.  Cikin rashin tsoro na tashi…