WATA SHARI'A CHAPTER 8

WATA SHARI'A CHAPTER 8
WATA SHARI’A  CHAPTER 8 Ganin kallonda ake bina dashi yasa duk na tsargu, nayi tsaye a kofar gida kasantuwar babu hanyar shiga,  Ganin nayi tsaye yasa wanda ke bakin kofar duk suka daddare kowa yana kallona, Saurin shigewa gidan nayi gabana sai faduwa yake hankalina ya matukar tashi, Da sauri na shige naci karo da Baba yana kuka sosai kamar karamin yaro,  Hakan ya kara tasar min da hankali matuka,  Wurin Baba na isa tare da gurfanawa k”asa ina kuka,  “Baba meyafaru? mesa kofar gidanmu yake a cike? Mesa kake kuka?” Duka a tare na jefa  masa wannan tambayoyin.’ Bakinshi na rawa yace  “Aishatu ‘yan fashine sun…” ya kasa karisa maganar kasantuwar kuka da yaci karfinsa. “Baba me ‘yan fashi sukayi? Dan Allah kamin bayani ka daina kukan nan” na fada hankalina a tashe.  Hannunshi ya daga ya gwada min inda aka harbeshi, sai kuma raunuka dake bisa kanshi wanda ban kula dasuba tun shigowata tsabar tashin hankali sai yanzu.  “Na rasa mesa sukazo wurinmu, ni nayi zaton ko sai masu kud’i ‘yan fashi ke zuwa ind…