WATA SHARI'A CHAPTER 6

WATA SHARI'A CHAPTER 6
WATA SHARI’A  CHAPTER 6 Fitilar hannuna na ringa haska motocin gaban gate din, amma kuma duk wadda na duba babu Gentle a cikinta,  Dan haka na kara matsawa daga gaba ina hashaskawa still dai babu ita,  Cike da tashin hankali na kashe fitilar wayar tawa, na latsa kiranta saidai kuma naji ana shaida min da babu kudi kona flashing a wayar,  Hankalina ya kara tashi, kamar zautacciya na ringa kwala mata kira amma shiru ne.  Har kusan Faculty of Humanities naje da yake shine daga gate din hostel babu nisa saishi amma babu ita,  Motoci biyu na hanga daga can nesa aikuwa babu shamakin komai na doshi wurinsu,  Dalle fitilar nayi ata farkon amma sai samari matasa na gani cike da motar, zasu kai kimanin mutum takwas zuwa goma, harma mamakin yanda motarta daukesu nayi,  Hakuri na basu sabida naga kamar basuji dadin haskewar ba.  “Ke ubanme yasa kika haskemu da fitila? Ko mu sa’anninki ne?” Wani daga cikinsu ya  tambayeni cike da muryar maye, alamar yasha ya bugu sosai.  “Kuyi hakuri ‘yar uwata na fito nema n…