WATA SHARI'A CHAPTER 5 WATA SHARI’A CHAPTER 5 A lokacin mun zama ‘yan mata cikakku masu jini a jika, Ba yabon kai ba ni kyakkyawa ce koda yake ba saina fada miki ba saboda kema kin gani da idonki, Sai a wannan lokacin diri na ya sake Iitowa sosai, Samari suka fara kawo min hari amma ni duk basa gabana, Babban burina bai wuce inyi zurfi a karatuna ba, inaso in zama wata mai matsayi a b’angaren education, hakan yasa ko a jamb dita na cike Bsc ed. Biology a Talent University Jalingo, Itama Gentle shi ta cike dukda ba shine burinta ba, amma kuma saboda taga hakan nakeso yasa itama tacewa mamanta lallai irin karatu daya take son muyi. A duk family d’inmu babu waada baisan Gentle ba, haka itama kaf family’nta kowa ya sanni, Maganarta d’aya dai Aisha Abubakar, kullum Ummimah, har wasu daga cikin danginsu itama suke kiranta da Ummimah sabida yawan fad’ar sunan da takeyi. Afrah da Amrah kuwa an girma, yanzu sune suka shiga ss3, mu kuma muna jiran sakamakonmu na jamb ya fito. Bayan sati biyu kuwa ya Iito, Alhamdulilla…