WATA SHARI'A CHAPTER 4 WATA SHARI’A CHAPTER 4 A gajiye na koma gida, da hanzari Mama ta tarbeni ta karbar min jakata ta makaranta kamar yanda ta saba koda yaushe itace take karb’ar jakata idan na dawo daga School. “0yoyo Aunty Ummimah” shine abunda ya fito daga bakin Afrah cike da farin cikin ganina. Murmushi na miyar mata dashi, “Sannu Afrah, ‘yan JSCE, ya jarabawar? lnce dai tayi dad’i” “Tayi dadi sosai Aunty Ummimah, ashema babu wahala jarabawar haka nan ake sakamu jin tsoro”, “Ai dama na fada maku babu wahala, ina Amrah ne?” Na tambayeta saboda ban ganta ba. “Amrah na daki batada laflya, kinsanta ita kingin ciwo ce, kullum daga wannan ciwo sai wancan ciwo”. “Subhanallahi! Ina zuwa barin dubata” kai tsaye na shiga dakinmu. Sosai hankalina ya tashi saboda yanda na ganta sai rawar sanyi take, Kusa da ita na zauna har inajin gumin jikinta, “Sannu Amrah, ashe bakida Lafiya”. Muryarta na rawa da k’yarta iya furta “ehh Aunty”, “Ayyah sannu kinji? Kinsha magani kuwa?”, “Nasha paracetamol sauran wanda nayi amfani…