WATA SHARI'A CHAPTER 3 WATA SHARI’A CHAPTER 3 Yau ta kasance Friday ne, dan haka tun karfe sha biyu Umar da Sultana suka tashi daga aiki, Kai tsaye suka wuce Gobarau Academy suka dauko Hafsa sannan suka wuce gida. A cikin motar Hafsa tace “Abbah yau ina cikin Class Teacher Nasir ya kirani, bayan naje yace min wai wani mutumi ne yazo nemana amma bazai barni in tafi wurin mutumin ni kadai ba dan kar aje wani abu ya sameni kuma laifinsu ne, shine na bishi mukaje wurin mutumin a bakin Head Master’s Office, Na gaisheshi ya dafa kaina yace min “kece Hafsa ko?”, “Ehh nice Hafsat Umar Muhammad” na bashi amsa, Shine yace min wai dama sakone zai bani wurinku, “Hafsa ki jaddadawa iyayenki cewa taimako yanada matukar muhimmanci, idan Allah ya baka damar taimako to kayi kokarin aikatashi tun kafln damar ta kufce maka” ya kuma ce min “karki manta ki fada masu wannan sakon”. Yana gama fadin haka English Teacher dinmu yazo harda bulala a hannunshi “Hafsa you are speaking vanacular ba? Hmm!” Naji tsoro sosai Abbah dan nasan …