WATA SHARI'A CHAPTER 13 WATA SHARI’A CHAPTER 13 Bayan sun koma gida sukaci gaba da tattaunawa inda Rabiatu da Zarah suka ringa tsinewa Gentle bayan Ummimah ta basu kaf labarin abubuwan daya samesu har mutuwar Baba, da kuma ta Afrah, ga Amrah maras lafiya bama asan inda take ba. Sunji haushi sosai kuma suma sukayi fatan samun nasara a wannan shari’ar da ake, saidai kuma a yanda sukaji labarin dukiyar mahaifin Gentle, da kuma babban Barrister din daya daukarmata, sun shiga kokonton samun nasararsu, saidai kuma sunyi fatan Allah yasa dukiyarsu kar ta amfanesu. Da wannan firar har yamma tayi Sultana da Umar suka dawo gida cike da gajiya, Su kansu a mota firar shari’ar kawai yakeyi, amma shi yanaji ajikinshi next zaman da za’ayi insha Allahu zasuyi nasara bama sai ansha wahala ba. Koda suka shigo gida Hafsa ta taresu, murna fal a ranta ta gaishe da iyayen nata sannan suka k’arisa daga ciki inda suka samu haryanzu su Zarah basu daina firar abunda ya samu su Gentle ba. Bayan sun natsu sosai Umarya kira Dr. Rafiq, ya…