WATA SHARI'A CHAPTER 12 WATA SHARI’A CHAPTER 12 Zama tayi a kusa dashi jin wayar da yakeyi, hakan yasa ya kalleta ya mata murmushi kafin yaci gaba da wayarsa, Ganin wayar bata k’arewa bace yasa Sultana ta mike ta bud’e wardrobe d’inta, Ta samu kaya wanda zasuma Mama daidai harda supopinta da lasuka masu tsada. Har ta fita ta kaima Mama kayan ta dawo Umar bai gama wayar ba, Kwanciya tayi akan k’irjinsa tana wasa da ‘yan yatsun hannunta tana kara tuno da gobe ne fa zasu shiga kotu. Tashi daga jikin Umar tayi jin ya gama wayar, “Ya kukayi dashi honey?” Ta tambayeshi. Tashi zaune shina d’in yayi yace “Munyi magana dashi yanada kirki sosai, Ya shaida min cewa sai next week Friday zai dawo, Ya min bayani cewa wallahi shi kanshi baki daya kanshi ya daure da wannan maganar, Saboda yasan ya ajiye takardar asibitin Ummimah wadda ta nunar da cewa fyade aka mata sannan kuma tana dauke da cutar hawanjini. Amma kuma wai daga baya ya nemi takardarya rasa, Saidai wai yaji magana ta fito cewa ciki aka zubar mata, Baki daya ya…