WATA SHARI'A CHAPTER 10 WATA SHARI’A CHAPTER 10 Washe gari ta kama ranar lahadi babu aiki, Hakan yasa da sassafe Sultana ta gyara gidanta ta bad’e ko’ina da kamshi, D’akin su Hafsa ta shiga ta samu Haydar baya nan sai Hafsa kwance a gadonta, hakan ya tabbatar mata da yana d’akin Safiyya. Kai tsaye d’akin Safiyya ta nufa, Ta samu Haydar zaune bisa cinyar Safiyya sai zuba mata surutu yake ita kuma tana dariya. Ganin Sultana yasa Safiyya ta sauke Haydar daga kan cinyarta ta tsuguna har k’asa tace “Ina kwana momy?”. Da fara’ah Sultana ta amsa da “Laflya kalau Safiyya, an tashi lafiya?”, “Laflya Aunty, ya gajiya?”, “Ba gajiya, naje dakin su Haydar ne na samu bayanan, na tabbatarda nan yayo”, “Ehh kuwa nan yayo kam, cikin magagin barci ma yazo, Haydar” ta miyarda kallonta ga Haydar. Hakan yasa ya fahimci inda ta dosa, “Good morning momy” ya fad’a bayan ya duk’a har k’asa. “Morning my boy, ka tashi lafiya?”, “Lafiya momyna” ya bata amsa yanayi yana wasa da warwaron hannun Safiyya. “My boy anyi sallah kuwa?”, “Ehh mo…