TSANGAYAR MATI CHAPTER 8

TSANGAYAR MATI CHAPTER 8
TSANGAYAR MATI  CHAPTER 8 Kamar wasa cikin Fadime ya tabbata, Inna har Asibitin Kauyen ta mika ta tare da Abule da Nene wadanda suka tike akan sai sun bisu sun ji da kunnuwansu. Itama Innar ba tayi gigin hanasu ba don tafi so suji abinda zai hana su bacci.  Ranar kam sun riga suyin gaba, zagi da tsinuwa ba irin wanda Fadime da Inna basu sha ba.  Tun daga wannan lokacin kuma sai sabon tashin hankali da makirci ya kara ballewa a gidan. Akwai ranar da Nene ta shigo da Kuliya cikin gidan, sanin cewa Fadime ba taso. Hakanan ta lallaba ta dora mata ita bisa gadonta tana cikin barci. Allah ne ya tsare da kwallayenta na jere basu zubo bisanta ba, saboda yadda ta dinga razana tana bige»bige a dakin. Karshe dai Inna ta cece ta da fitsari ya fiddo ta, ta juyo motsi barin Fadimen. Shi kuwa Mati yana can ya saki ganɗa dakin Abule. Sai washegari ne Inna ta sanar masa, karshe dai tayi maganin abin da cewa duk wacce ta kara kawo wani Abu gidan ko da ‘Bera ne, k0 tajewa Fadime ko Mati da bak’ar magana to …