TSANGAYAR MATI CHAPTER 5 TSANGAYAR MATI CHAPTER 5 Inna ta d’aga hanci sama taja iska, sai kuma ta furzar ta baki tana hararar kwanukan da Nene ta aje gabanta. “Uhm ni wai da mushe kikai miyar ne Nene?” “Me kika gani Inna?” Nene ta fada tana so sa kai. “A‘a gani nayi tunda kika doso gurinnan ya cika da tsami da k’arni tamkar wacce ke aiki a kwata k0 mutuware.“ ‘Ai fa, komai na yi ban burge ba, to ai sai dai ki mutu, aikin na Mati ne, mallaka kuma tawa ce, sai shegen kinibibi da wani bakinta kamar na bakar Akuya…‘ Ta fada da gunguni “Me kike cewa ne?” “A’a cewa na yi Binta Sudan ne na balbala ajikina saboda kiji kamshin.” “Ko kuma Binta Maliya ba? To wanann dai karni yake sai a sake lale, ki kwashe kwanukan nan daga gabana, anjima zansa Mati ya karbomin Abincin daga gidan Larai.” “Uhm gaba ta kaini, dama kena tsamewa kai da kafar kazar.” Ta fada da ‘kun’kuni tana tattara kwanukan. “Bakiji ba” Inna ta fada “Inaji Inna” Ta fad’a tana gabda barin d’akin. “Idan gyaran zaki yi ki fara gyara can cikin, shi ne ko da ki…