TSANGAYAR MATI CHAPTER 4

TSANGAYAR MATI CHAPTER 4
TSANGATAR MATI  CHAPTER 4 Assalamu Alaikum mutan gidan.” Fadin ‘yar doguwar dattijuwar kuma tsamurmura mai sharba-sharban tsagu a gefen bakinta, baka ce wuluk kamar danta Mati. Mati ne a gaba d’auke da k’aramar akwatin kayanta, ita kuwa tana biye da shi a baya. Abule ta soma fitowa daga d’aki sai Nene daga bandaki suka saki baki suna kallonta. ‘lkon Allah, wai na kwance ya fadi.‘ Cewar Abule kenan a kasan ranta ganin shigar da surukarta su tayi, wata karamar Atamfa Super ce ajikinta an mata dinkin riga da siket sai wani babban mayafi data yafa a kafada ba rufin kai ba. Fuskarnan tasha farar hoda, ba’a gane wa sakamakon bakin fatarta da ya ciza saidai kuma kana gani zaka rantse yanayin hunturu ne wanda yayi sanadin da fatar fuskar nata ya bushe yayi furu-furu, ga uban jan janbaki data lafta a lebbanta masu tudu. A hankali Nene ta maida dubanta ga Abule, akayi sa’a itama ta kalleta sai kuma suka sauke ajiyar zuciya kam kowaccensu ta shiga rububin tarbarta da amsa sallamarta. “Waalaikumuss…