TSANGAYAR MATI CHAPTER 3

TSANGAYAR MATI CHAPTER 3
TSANGAYAR  MATI CHAPTER 3 “To ai saiki kauce daga samanmu tunda dai shegen bakin cikinki yajawo kinji abinda Tsohonki ke aikatawa a waje.” Mati ya fadi yana hararar Abule da tayi tsaye hannu bisa kugu tana jinjina maganar ‘Yar Magaji.  “Oho dai, dadin ta Bazawari aka ce ba ‘Barawon Jakai ba.” Ta fada tana hararar Nene dake yatsine-yatsine.  “Kyale kinji Nene uwargidan Mati, muje na raka ki daki ki kwanta, daga yau ko tsinke ban yarda kin dage a gidan nan ba, wanda ba zai iya gani ba yayi zuciya mu gani a kasa.” Ya fada cike da lallami.  lta dinma mikewa tayi cike da kwarkwasa har da rike rigar Mati. Gab da zata daga labulen kabar ta ne ta waigo ta kalli Abule fuskarta dauke da murmushin kadan kika gani.  Dogon tsaki itama taja tana hararardakin bayan shigewarsu. “Wai Kura ce ta samu damar mike kafa, ayi dai mu gani, muna nan za kazo kana min ‘yar murya. Haryaushe ma akai daren?” Jin shiru ba su amsata ba sai tashin dariyarsu da takeji ne ya sata juyawa a fusace zuwa na ta dakin.  Kwana biyu g…