TSANGAYAR MATI CHAPTER 1

TSANGAYAR MATI CHAPTER 1
TSANGAYAR MATI CHAPTER 1 Buguzum-buguzum ta sanyo kai cikin gidan tana waka.  “Ahayye iye nana…”  Difta dakata gami da sakin baki adalilin abinda ta hango a tsakar gidannasu. Maigidansu Mati a kofar dakin kishiyarta Abulle zaune suna hira da dariya. Ganinta ya sanya Mati yin tsuru da idanu yayin da ita kuwa Abulle ta washe baki, cike da dabara ta fiddo takardar naman data boye a bayanta ta warware ta dauki tsoka dayan da ya rage ta jefa a baki tana tauna gami da fadin.  “Maigida kana burgeni, kana kawomin irin wanda na keso.”  Mati ya watsamata kallon muguwar mace, shaf a tunaninsa dagaske ta yarr da takardar tsiren, ashe makirar abinda ta shiryamasa kenan. Ya numfasa gami da share zufa yana duban Nene batare da yace uffan ba.  Nene wacce zuciyarta ta gama kaiwa bango ta fisge mayafin kanta ta hadiye miyan daya taru a bakinta tsabar na ranta ya biya ta ci damara ta hau tafa hannu.  “Allah na godemaKa daka nunamin abinda ke faruwa a bayan idona! Ashe daman cuta ta ake yi ana dawowa idan bana n…