SHIMFIDAR MIJINA COMPLETE
SHIMFIDAR MIJINA LITTAFIN Princess Eshat Aysm ?????????? ?????????? *SHIMFID'AR MIJINA* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* _We dont just entertain and educate we also touch the hearts of the readers_ PML . Writen By Princess Eshat Aysm . . Page 1 . _K'irk'irarren labarine banyi don cin zarafin wani ko wata ba_ . . Kuka take shek'awa da iya k'arfin ta, ANWAR ya dafe kanshi yarasa wani irin rarrashi zai mata ta fahimce shi, a duniya bayan iyayen shi babu abunda yake so kamar Maryam, Kukan nata har cikin ranshi yakeji. "Maryam kema kinsan ina sonki bazan tab'a cutar dake ba, wannan aure zanyi ne kawai amma ki yadda kece muradina Maryam, idan har baki so abunda nake so ba nayadda kin daina sona, na fad'a miki ke kad'ai nake so auren ne kawai yazo bawai don kin rageni da komai ba". kukan tad'an sassauta ya jawota jikinsa yafara share mata hawayen, ta saki ajiyan zuciya ta ce "Anwar kishiya abun tsoroce banaso a rabani dakai". Ya dad'a rungumo ta yafara ki…