NAYI GUDUN GARA CHAPTER 40NAY

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 40NAY
NAYI GUDUN GARA CHAPTER 40 Yau ramadan yasan girkin safna ne yaki dawowa da wuri har saida tai bacci yana shigowa yayi samansa ya kulle. Ya zauna ya shiga tunani ya zama dole ya sanya tsaro a dakinsa,  domin dauke dauken da ake mai yayi yawa.  Da asuba da safna ta tashi ta tuno fa ramadan a wajenta yake amma shine bai dawo da wuri ba. Tsaki tai tace “ai yana sane yayi min hakan,” wanka tai ta tafi dakinsa. Alokacin ya tafi”: masallaci, domin ladifa ce ta sanya mai alerm irin na bakin gadon nan, dan tasan baya tashi da asuba, amma da yaji alerm zai mike. Dakin ta shiga ta dade akan gado, Iokaicin bai  dawo daga masallaci ba, yana shiga dakin yaganta sai ya dan kauda kai. Ya kwanta, tace ‘shine jiya ko nema na bakai ba.‘ Ai kinyi bacci lokacin.”  Yasan abinda take rara gefe, shi fa wallahi yanzu ta isheshi, sam ma saboda damunsa da take yasa ma ya daina jin wani mararinta, abubuwan da dama ya kwallafa rai akanta duk sun fice mai arai, saboda rashin hutun da bayayi ya sanya yake jin haushinta …