NAYI GUDUN GARA CHAPTER 37

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 37
NAYI GUDUN GARA  CHAPTER 37 Lalla na shlga d’aklnta ta zauna ta shlga raira kuka, ace Ita za ai wa kishiya! Abar da take gudu gashi gaba da baya tana da ita. Kishiyar ma a b’oye. Ta tsani kishiya ko sunanta ba ta son ji, amma wai yau ita ce aka yiwa. Lad’ifa ma dan kawai ta zo ta sameta ne babu yanda  za tai ne, amma sam! tanajin ba za ta iya zama a gidan ramadan ba, musamman wulakancin da yayi mata gaban amaryarsa. Wani irin haushin ramadan ne da kishin yanda amaryarsa ke wani gantsara agabansa shi kuma ya susuce agabanta ya tokare wuyanta, dan ji take ko ganinsa ba ta son sake yi, da sauri ta shiga had’a kayanta, dan ba za ta iya ci gaba da zama agidansa ba, dan za ta iya murgud‘e kugun amaryarsa in ta shi ga gonar ta, domin abinda yake mata ya kai intaha, yayi aure bai sanar da su ba, ga kuma salon wulak’anci.  Lad’ifa kuwa na shiga shashenta ta kwanta tai rubda ciki, babu abinda ke yawo a zuciyarta sai abinda ta gani kuma ya faru, da ta runtse ido safna take hangowa ajikin ramadan da …