NAYI GUDUN GARA CHAPTER 35 NAYI GUDUN GARA CHAPTER 35 Laila kuwa tana komawa shashinta ta saka CD ta shiga turkar rawa, saboda tsabar Jin dadin da takeji na fasa auren nan. Jin kida ya sanya ladifa ta fito ta shiga shashenta tace “laila kinajin dadi kam.” “Yo ba dole nai rawa ba da murna, da tuni an kwaso mana yar aiki matsayin kishiya oh! Ni laila da ina zan sanya kaina.” Dariya ladifa tai tace “to Allah ya kara farinciki. Ai ba don wani abuba da nazo na taya rawa.” “Aiko dai ga fili nan.” Ta fada tana ci gaba da rawar. Haka dai al’amuran rayuwar gidan ramadan taci gaba da gudana kowa ya fuskanci abinda ke gabansa. Ogan kuwa ya maida dukkan lamuransa ga harkokinsa. BA YAN SHEKARA DA YA Laila ta saki jiki, domin tasan cewa ramadan ita yake shayi shiisa ya saduda. Don taga bai kara batun sako wata macen ba. Duk da hakan ta sanya mai ido saboda kar ya kuma jajubo wata a cewarta. Shi kuwa ta bagarensa Tsoron ma ya tunkari mace yake, saboda ‘yan kananun matsalolin da ya fuskanta, kawai ya rigada ya maida hankalinsa …