NAYI GUDUN GARA CHAPTER 34

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 34
NAYI GUDUN GARA  CHAPTER 34 A fusace ya shiga gidan, tun daga soro yake cewa “ladidi fito, rashin mutuncinki yayi yawa.”  Fut ta fito ta tsaya tana fadin”yakuba menene ya kaika shigowa cikin gidana?.”  “Ke ladidi hawainiyarki ta kiyayi ramata, wallahi ba damuwata bane na mangareki, ke har kina da gidane ladidi? mutuniyar da jahilci yayi miki katutu ina kika taba ganin an yi neman aure kan nema? ke mace ma kin taba ganin ta aurar da ‘ya‘ya.”  “Ka gama? Nace ka gama, to ka saurareni kaji, wallahi idan naci, sunana ladi to ba a isah asanya yarinyar nan a lalle ba indai da surajo ne, nice nan ni ce mahaifiyarta, ni nake kula  da ita, kuma nice nan zan aurar da ita, uban me kake yi mata na ce uban me kake yi mata?.”  “Ba nayi mata komai, amma nine nan mahaifinta. Bayan kaita birni aikatau da kikai shekara da shekaru ban magana ba, sai yanzu za ki wani zo ki nuna rashin hankalinki, to yanda kika tufka haka za ki warware.”  Adaidai lokacin hansatu ta shigo gidan, tana ganinsa ta tsugunna tana gaidas…