NAYI GUDUN GARA CHAPTER 33 NAYI GUDUN GARA CHAPTER 33 Al’amarin duk ya sanya zuciyarta ta shiga wasi-wasi,anya kuwa ba ta d’aukowa kanta dala ba gwambo ba. Ganin babu sarki sai Allah ta share hawayen fuskarta ta mik’e da sauri ta shige gidan, innarta na tsaye ta kasa tsuguun! sai farin-cikki take tana wassafa yanda za ta tsakuri abubuwan dan ta mikawa mak’ota, dan su san cewa fa ‘yar tata ba tai zuwan birni a banza ba. Hansatu ta zauna gefen d’akinsu tace “inna ni abinda nake san ki gane kinki fahimta. Maganar surajo fa, kina gani ko jiya yazo fa.” “Ke dallah can matsa wawiya, wa ya ke ta wani surajo? ni ce dai nan ke d’awainiya da ke, dan haka babu wanda zai d’aga min hankali. ” Hansatu ba ta k’ara cewa komai ba ta shiga d’aki. ***** Yana tafe a motarsa yana jin kira’a, tunani kawai ya ke yanda zai tunkari hajiya amma yasan babu ja tunda ta san dai ba haramun ba ne. Wajen 3 ya karasa gida. Babu kowa a felon haka ya sanya ya yi b’angarensa dan ya huta, yasan yanzu laila za ta zo ta dameshi. Wayarsa ce tai k’ara,…