NAYI GUDUN GARA CHAPTER 32 NAYI GUDUN GARA CHAPTER 32 Dakyar laila tai bacci, saboda bakin» ciki da kishi, hade da takaicin da ya rufe mata zuciya, in banda ma namiji da bai raina abin kunya ba, ace ‘yar aikinka yana kula ta, sai ta sanya tsaki sai kwafa Washegan’ da safe. Laila bata nuna komai ba,jira kawai take ramadan ya sanya kafa ya fice ita kuma ta fara aiwatarda kudirinta, dan tasan tabbas zai iya zama ramadan ya hanata. Sai data bari hansatu duk ta gama aikace -aikacenta sannan ta dumfari dakin ta turo hansatu,ta na tsaye tana gyara jakar kayanta taji saukar bulala a bayanta, sai ta gantsare ta fasa kara “wayyo.” Da sauri tajuyo kafin ta kara magana laila ta kuma shaula mata, nan fa hansatu ta gigice ta shiga kuka wiwi, “dan Allah Anty kiyi hakuri, me nai miki.?.“ Cikin tamke fuska tace “wato ke ga ‘yar iska ko ga maha,incinya mai bin mazan mutane ko, wato ke gaki mai wayo ko?kinzo a bagar kina iskanci da mijina ko? to wallahi yau sai na lahira sai ya fiki jin dadi ke idan akace ki kuma kula mijina ba za…