MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 39 THEND MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 39 THEND Tun a cikin mota suke yin fada kasa kasa yadda ba kowa ne zai gane ba bare aji. lNdo mita kawai take masa sabida tsabar ta gaji da zama bata taba yin tafiya irin me nisan haka ba gashi tun a cikin motarta fara ganin ban-bancin kano da inda za suje domin duk cikin motar yare ne basufi su shida bane hausawa kuma suma ba wai zaune suke a guri daya ba kowa yana kan kujerarsa. Wani yare dake kusa dasu yana ta kallon Ayman ya zuro hannunsa yana shafar kanshi tare da tambayar INdo ya sunan dan cikin yarbanci kirjin lNdo ya dinga bugawajin bata gane abinda yake nufi ba, sai kallon mutumin take shi kuma yana faman kuma tambayarta. Kallon Sadeeq tayi kawai taga yayi tamkar baya jinsu yana karanta jarida tasa hannu ta zunguro shi ya kalleta sannan ta kawar da kai tare da cewa. “Ana maka magana fah.” Kallonta yayi yana kumshe da dariyar sa kafin ya kalli bayeraben sai taji ya gaya masa sunan Ayman bayeraben ya jinjina kai bakinsa a washe ya cewa Sadeeq yaron yana da…