YAR SHUGABA CHAPTER 26
YAR SHUGABA CHAPTER 26 Murtuke fuska tayi ta galla masa harara sai ta kauda kai, Yaya Aryan yayi murmushi ya kura mata ido, gaba d’ayaji tayi ta takura a gurin, mik’ewa tayi zata bar wurin, garin sauri takalminta ya turgud‘e saura kiris ta fad’i, da sauri Yaya Aryan yace “subhanallah” juyowa tayi idonta ya ciko da kwalla ta kalle shi tana ya mutse fuska alama taji zafi murmushi ya sakar mata, murguda masa baki tayi ta wuce,wannan karan murmushin da yayi har fararan hak’oransa saida suka bayyana. Anyi taro an washe lafiya kowa yaje gida lafiya. Basma tana zaune a d’akin Momy suna hira da Momy, sai ga Yaya Shureym ya shigo,ya risina ya gaida Momy kana ya zauna, Momy ta mik’e ta basu guri, shuru suka yi na mintuna, Yaya Shureym yace “Basma dan Allah ya kamata ki tausaya min, ina son ki son da bana yiwa kai na, ki yafe min my Basma” fuskarta tamau tace “ina Anty Safeena?” tambayan yazo mishi a bazata, har yakan manta da yana da Safeena, cikin sanyinjiki ya bata labarin barinta gidan da koma…