YAR SHUGABA CHAPTER 25

YAR SHUGABA  CHAPTER 25 A hankali ya juyo ya fuskace ta, ido cikin ido suke kallon juna harna tsawon minti biyar, Yaya Aryan ya katse kallo tare da sauke ajiyar zuciya a hankali, fuskansa babu yabo ba fallasa, bai furta mata komai ba ya juya zai cigaba da tafia, cikin sauri ta sha gabansa tace “haba Yaya Aryan ya zaka wuce baka ce min komai ba, yanzu na sauka ajirgi dawo wata kenan, ko gida banje ba naji sha’awar zuwa wurin nan, zuciyata ce ta jawoni ashe kai ne zan gani, dan Allah kace wani abu ko baka farin ciki da gani nane” saita k’arashe maganar cikin shagwab’a. Kallonta yayi sama da k’asa sai ya yatsine fuska yace “ke wacece ban ganeki ba fa?” damm Basma taji zuciyarta ta buga, tace cikin tsoro da sark’ewar murya “Haba Yaya Aryan nice baka gane ba, Basma ce fa” ya d’aure fuska yace  “Malama kiyi hak’uri ni ban ganeki ba, zaki iya tafiya” ai Basma cikinta ne taji ya murda, tayi sauri ta dafe tana ambaton Allah, kuka ta b’arke dashi mai k’arfl, cikin kuka tace “haba Yaya Aryan dan Al…