YAR SHUGABA CHAPTER 24

YAR SHUGABA CHAPTER 24 Bayan sun kaishi asibiti likita ya duba shi, ya tabbatar musu da damuwa ce ta haifar masa da suma “amma yanzu ya farfad’o, nayi masa alluran barci domin kwakwalwansa ya huta, zuwa anjima inya farka, komai zaiyi dai-dai insha Allah”  Bayanin da likita yayiwa su Yaya Ahmad kenan sai ya wuce, zama suka yi suna ta zancen zuci, Yaya Ahmad, Yaya Naufal, da kuma Yaya Jamal sune suka kawo shi asibiti. A can gidan kuma sun k’ara shiga damuwa fiye da damuwar rashin Basma, Dadsy ya shiga tunanin ina yasan Aryan, lallai fuskansa tayi masa kama da wanda ya sani da dad’ewa, amma ya kasa tuna komai, matsantawan da yayi ma kansa da tunani ne ya haifar masa da ciwon kai, dole ya yakice abin a ransa dan gudun matsala. Awa biyu Yaya Aryan ya farka, sai dai bai iya furta koda kalma d’aya ba, idanun sa sun masa nauyi da kyaryake iya bud’esu a hankali ya rufe, hawaye mai zafi ya gangaro masa a kefen idonsa, Yaya Ahmad ya matsa kusa da gadon cikin sanyin murya da tausasa zuciya yace,  “Ar…