YAR SHUGABA CHAPTER 23
YAR SHUGABA CHAPTER 23 ‘Etopia’ Basma ta sauka a jirgi, sai rarraba ido take ko za ta ga wanda zata iya tambaya, jikinta yayi sanyi ganin tazo garin da bata tab’a zuwa ba, tsoro da fargaba ne ya cika ta, runtse ido tayi ta bud’e tace a fili “Hasbunallahu wa ni’imal wakil, laa ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazza zalumin, astagfirullah wa’a tubu ilai” abinda tayi ta maimaitawa kenan a zuciyarta, a hankali ta somajin k’arfin gwiwa da natsuwa, fitowa tayi bakin hanya ta tari taxi, cikin harshen turanci tace “Hotel mai kyau nake so ka kai ni” cikin harshen turanci ya mai da mata da “to shigo mu tafi”. Ya kai ta babban hotel mai kyau, ta biyashi kana ta wuce ciki, kud’in d’aki ta biya, saitaja trolley d’inta, wata daga cikin ma’aikatan Hotel d‘in suka yi mata jagora har d’akin data kama. Wanka tayi ta gabatar da duk Sallolin da ake binta, bata jin zata iya cin abu mai nauyi, telephone ta d’auka ta kira cikin Hotel d’in da a kawo mata coffee da kuma Burger, haka suka kawo mata, ta som…