NAYI GUDUN GARA CHAPTER 8

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 8                      MONDAY Ranar ta monday da farin-ciki ta tashi, ji take kamar an wanke mata zuciya, bata san me ya saba,ko dan adduoin da tai ta yine, kan Allah ya bata dangana,tabbas zata iya yarda da hakan, dan tun da suka samu sab’ani da Ramadan takejin ba dad’i a rayuwarta,tana jin koda mijin nata shine mai lefi, to sai ta kejin kamar awajen Allah tana cikin lefi,tun da mijinta na fushi da ita, shi,isa da suka shirya taji sauyi a ranta. Tana mamakin kanta sosai. Tun daya fita aiki sai ta tsiri gyare gyarenta, sanin cewa za tai bak’uwa sabuwar fuska, duk ta tanadar mata kayan tarba. Karfe goma-shabiyu Sallamar Salma ya karad’e falon. Ladifa da ke kitchen ta fito,murmushi ta sanya ta ce “bak’uwa mu kai?.” Salma tai murmushi, sanye take da bak’in lece mai yarfin fulawa green, ta yafa mayafi green,da bak’arjaka da takalmi,ta yi kyau sosai. Kallonta lad’ifa tace ga guri zauna..” Zama su kai suka gaisa. “Matar Abdallah ko?.” “Ni ce wallahi,” ta fad’a tana murm…