MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 12
MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 12 Washe gari Abubakar ya yafi abuja danyin abinda Abba yasa shi. Tunda kuma ya dawo daga abuja kullum akwai inda zashi sam baya samun zama gashi yayi-yayi Sadeeq ya d’aukar masa amana da alk’awarin nemo INdo ya kula da ita amma Sadeeq yak’i shi adole idan zai tayashi toh saidai ya canza wata amma ba INdo ba, da haka sukayi bankwana baram-baram kowa najin haushin d’an uwansa. INdo kuwa wayyo Allah tazo saye kauyanci da k’arin abubuwa duk sun dad’a k’aruwa ta zama tamkar ‘yar garin duk inda kaje sai kaji labarinta kaf kauyan sun-santa dan akwai shiga jama‘a. Da mutum d’aya ne basa shiri wato yakumbo tsahare, sam basa jituwa da juna ko a layin band’aki. Ranar da lawisa ta haihu kuwa su INdo sune masu jigo, anyi ruwa anyi tsakl’ tazama tamkar itace mejegon dan ta kanainaye komai lawisa kuwa sai kawaici take bata magana. Ranar suna aka sanyawa yarinyar Raihanatu suna kiranta da Ladi kasan cewar ranar lahadi aka haifeta. Watan INdo biyar a garin saye ta kuma irin waye…