*Father of soldiers*
*π₯TAKUN ΖARSHEπ₯*
_Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buΖata zai tura mun message ta whatsapp Ιina (08103884440) kada ku bari abaku labari sannan a kula wannan itace numbar wayata,Wasu suna Ιaukar numbar Wanda suka bani tallarsu kayansu suna kiransu a matsayin ni,bayan ni ga numbar dana bada nan itace numberta_
*Nagode sosai da addu'o'inku agare ni,da kuma uzurin da kukayimun,har zuwa wannan lokacin,Allah yabar zumunci a tsakaninmu daga nan har gidan aljannaπ*
*nace ba Masu satar littafi suna fitarwa ta bayan fage,mai yasa baku Ζarasa masu labarin ba?kuma kenan saida kuka jira ni?ae nayi tunanin cewa zaku Ζarasa masu labarin ne ashe dai sai anjira Boss*ππ€£π
Bismillah
Kai tsaye sautin ringing Ιin wayar ya daki dodon kunnan Aunty babba dake baje saman gadonsu tana Bacci,a lokacin ko yatsanta bata jin xata iya motsawa saboda baccin dake a idanunta,yatsina fuska tayi alamar an takura mata,
Ishaq dake tsaye agaban mirror yana gyara jikinshi ya Ιan gyara murya tare da cewa"Madam ki daure ki tashi ki Ιaga kiran nan!da alama kira ne mai muhimmanci tun Ιazu wayar ke ta ringing,"
Uban tsoki Aunty babba ta buga tare da yunΖurawa daΖyar ta tashi daga zaune,jikinta na sanye da sleeping dress,riga da wando purple colour,
Fuskar nan tayi suntum kamar wadda aka nausa,hannu takai tare da Ιaukar wayar dake ajiye saman bedside drawer,duba screen Ιin wayar tayi ganin sunan Hayaam ya bayyana yasa ta Ζara tamke fuska kamar ta shanu,Ιaga kiran tayi tare da kara wayar a kunnanta,rai a6ace tace"Meyasa kika kirani fitsararra!ko kin kira ne don ki Ζarasa yimun rashin kunyar taki don ubanki,"
on the other hand hayam tace"haba aunty laila,ni harna manta da abunda ya faru atsakanin mu.....'tunkan hayaam ta Ζarasa maganar Aunty babba ta katse mata hanzarinta da cewa"Idan kin manta ae ni ban manta ba,Ki faΙamun uban miyasa kika kira ni,idan ba haka ba ni zan kashe wayar,
Zuba mata ido Ishaq yayi yana kallonta aransa yace"Zagi kamar Ζ΄ar maguzawa,ko kunyata bata ji,sae faman Ιura ashar take yi,ni dae Allah ya haΙani da Guyaba,'
cike da damuwa hayaam ta sassauta muryarta,tare da cewa"Aunty laila,na shiga uku,ko ince mun shiga uku,Akwai gagarumar matsala,Gaba daya duk wani plan Ιinmu ya tashi aiki,'
Tunda Aunty babba taji hakan,gabanta ya faΙi rasss,Ζasa Ζasa da murya tayi tace"Hayaam meya faru?wata irin matsala kike magana akai?
"Aunty laila,Ashe yarinyar nan mai aikin gidansu,Ιiyar uncle Ιinsu ce Abusufyan!!!!!" tamkar saukar aradu haka aunty babba taji maganar Hayaam aikuwa a matuΖar gigice ta miΖe tsaye tana cewa
"kutumar uba!inji ubanwa!yaushe Abusufyan ya ta6a aure,Wlh Ζaryane koma wani Ιan Ζaniyar ne ya faΙi maki hakan babban maΖaryaci ne....'
Gaba daya hankalin ishaq ya dawo kanta,maganar dayaji tana fadi ta tsaya mashi aranshi,
"Wani abusufyan din kuke magana akai,"
Firgit Aunty babba tayi tare da ware ido tana kallonshi sam ta manta da cewar yana acikin Ιakin,
Hankali a matuΖar tashe ta miΖe tsaye da nufin ta fuce daga cikin Ιakin,Saboda tsabar ruΙu ta nufi hanyar shiga toilet,
gyaran murya ishaq yayi mata tare da cewa"kada fa ki shiga toilet da waya a kunnanki,'
A zabure ta juya ta kuma nufi wardrobe da alama ruΙu yasa ta manta hanyar fita daga Ιakin,zuba mata ido yayi yana mai mamakin irin kiΙimar da tayi,to ko lafiya?ya tambayi kansa,
Bata ankara ba sae da goshinta ya bugi jikin wardrobe din kayan nasu,sannan ta gane inda ta dosa,Rai a6ace ta kama hanya ta fuce daga dakin,saukowa downstairs tayi ta miΖi hanyar wannan tsohon store Ιin data ta6a garΖame su hosana aciki,anan corridor Ιin ta tsaya tana sauraran Hayaam,
"Wlh Aunty laila da gaske ne,Ni shaidace,Naji komai lokacin da Uncle Ιin nasu yake korama junaid bayani,bama haka ba Aunty azmee da kanta ta gasgata mun hakan,Babban abunda yafi rikitar dani Yaran fa triplet ne ashe,kuma dukkansu Mata ne kyawawan gaske,kamannin su sak iri Ιaya,Kuma kina kallonsu zaki gane cewa Ζ΄a'Ζ΄anshi ne......'
Hannu Ιaya Aunty babba tasa ta dafe tsakiyar kanta,yayin da dayan hannun ke ruΖe da wayarta data kara a kunnanta,
"Hayaam bazan ta6a yarda da zancenki ba,Taya hakan ma zata faru!mutumin da bai ta6a yin aure ba,Shi za'ace yana da Ζ΄a'Ζ΄a har Ζ΄an uku!Cikin shege kenan ya ta6a yima wata harya same su!Ni ban yarda da kalamanki ba,Hayaam kinsan cewa babu kyau tsoratar da musulmi,Idan wasa kike mun ki daina!!!!!
6acin raine yasa hayaam ta kashe wayar
Fashewa da kuka tayi saboda Ζululun baΖin cikin daya tokare mata maΖoshinta,ga zuciyarta dake ta faman tafarfasa,Gaba daya bata jin daΙin jikinta,
Zubama wayar ido Aunty babba tayi tana kallonta,
Tsoki taja tana jinjina kai tace"dama saida raina ya bani cewa Ζarya take yi mun,tayi mun hakan ne saboda ta tsoratar dani don in saukko,Shashasha kawai,
"Mommy kin farka kenan"
Muryar hafsat ce ta katse mata zancen zucin nata,
Juyowa tayi tana kallonta,atsaye take fuskar nan Ιauke da murmushi jikinta na sanye da riga da wando na jeans,ta Ιaure sumar kanta da ribbom,yayin da hannunta ke ruΖe da Cup mai Ιauke da Tea mai zafi sai faman tiriri yake yi,
Tunda Aunty babba taga hafsat na murmushi tasan cewa akwai matsala,hakanan dae ba zakaga fuskar hafsat da murmushi ba tunda farar safiya,
ΖaΖalo murmushin yaΖe Aunty babba tayi tare da cewa"Lafiya naga kina murmushi"?
"Lafiya lou mommy,kawai wani abun farin ciki ne ya faru,nasan cewa muddin kema kika ji,zaki yi farin ciki sosai,'
Murya asanyaye aunty babba tace"FaΙamun daughter har na Ζosa naji wannan abun farin cikin?halan an Ζara maku albashi ne?ko matsayi aka Ζara maki wurin aiki"?
Dariya hafsat tayi tana girgiza kai tace"Mommy baki canka dai dai ba,wannan albishir Ιin da nakeso inyi maki yafi Ζarfin duk waΙannan abubuwan da kika lissafo,kar6i tea Ιin nan ki fara korawa kafin na faΙa maki,"
Hannunta na kerma ta kar6i kofin da hafsat take miΖa mata,a hankali takai cup din bakinta ta kur6i Tea Ιin,kusan sau uku tana kur6arsa,kafin ta Ιan jinkirta bayan ta janye kofin daga bakinta tace"daughter dan Allah ki faΙamun wannan wani abun farin ciki ne!wlh duk na Ζosa naji,'
"Zan faΙa maki mommy amma mu shiga daga cikin palour mu zauna,'
"Ba inda zanje,idan zaki faΙamun ki faΙamun kawai,Sae ja mun rai kikeyi," tayi maganar tana faman tamke fuska,
Hafsat tace"bada jimawa ba,Na kira Aunty azeema,don in gaishe da ita,Anan take sanar dani cewa Ζ΄a'Ζ΄an uncle abusufyan Sun bayyana...!
Tunkan ta Ζarasa maganar a gigice Aunty babba ta saki kofin dake hannunta,Ya tarwatse Ζasa,Ruwan tean dake ciki ya fallatsar masu a Ζafa,
ja da baya hafsat ta Ιanyi tana kallonta tace"haba mommy,so kike ki Ζonamin Ζafa ta,daga faΙin abun farin ciki?
Rai amatuΖar 6ace tace"Ki 6ace mun da gani sakarya kawai,MaΖaryatan banza,bazan ta6a yadda da kalamanku ba,duk bakinku Ιaya da Hayaam,'
Ta faΙi hakan tare da kama hanya fuuuuu kamar zata tashi sama,ranta duk a jagule,bin bayanta hafsat tayi da kallo harta haye upstairs,ta6e baki tayi tare da watsa hannayenta tace"I don't care, Ni dae farin ciki nakeyi,Daddy ma nake jira in tambayeshi yaushe zamu je gidan saboda a qagare nake dana ga Ζ΄a'Ζ΄an uncle Ιinmu Abusufyan,tunkan na gansu har naji ina sonsu sosai,in ma na tashi tafiya hada tsaraba zan tafin masu dashi,'
Cike da farin ciki hafsat take maganar,zuΖunnawa tayi tana tattare kofin da aunty babba ta fasa,
Lokacin da Aunty babba ta Ζarasa bedroom Ιin nasu,har ta Ιaga Ζafarta zata zura acikin Ιakin taji muryar ishaq yana cewa"Alhamdulillah!Alhamdulillah!Alhamdulillah!Abba nayi farin ciki sosai,Meyasa tun jiya ba'a sanar dani ba,ae da tunda sanyin safiya zanyi maku dirarr mikiya,Amma ina taya uncle murnar ganin Ζ΄a'Ζ΄anshi,kuma ina tayamu murnar samuwar Ζ΄an uku acikin zuri'ar mu,gaskiya bazan ma iya jurewa ba,Zan shirya nazo ne kawai,saboda na qosa naga Ζ΄an ukun mu bayin Allah....
Abba yace"wani abun ma sai kayi tozali da yaran,kyawawan Ζ΄an mata dasu,Yadda kasan photo copy Ιin abusufyan haka suke,kamanninsu sak iri Ιaya da nashi,'
Murmushi Ishaq yayi tamkar yana agabanshi yace"Abba kafin na Ζaraso,dan Allah a isar musu da saΖon gaisuwata,Ace yayansu General ishaq yana gaishe su sosai da sosai,kuma saboda suma zaiyi zuwa na musamman,'
"Insha Allah zan sanar masu yanzun nan,Allah ya kawoka lfy,"
"Ameen Abbana,"
Sun jima suna waya kafin sukayi sallama ishaq ya ajiye wayar,
tashin hankalin da ba'a sama shi date!!!!!!!
Magana dae ta tabbata da gaske ne zancen da hayaam da hafsat suka faΙa mata,TabΙijancan,
Dakyar ta iya shiga cikin Ιakin,lokaci guda ta rasa kuzarin jikinta kamar wadda tayi Zazza6i na sati Ιaya,
Jin takun tafiyarta yasa ishaq juyawa yana kallonta fuskarshi a washe har ya kammala shiryawa cikin haΙaΙΙiyar shadda,
Ganin yana ΖoΖarin buΙe baki yayi mata magana yasa tayi saurin katse shi da cewa"Naji abunda ya faru,Hafsat ta sanar dani komai,ina tayaku murna,'ko amsar shi bata tsaya ji ba,ta faΙa cikin toilet,
Tana juyo muryarshi daga cikin bedroom Ιin yana cewa"Ni yanzu zan wuce Abuja ne,inyaso kun biyo ni daga baya ko zuwa gobe ko jibi haka,duk dae yanda kuka yanke shawara keda hafsat,
daga cikin toilet tace"Allah ya sauke ka lpy,in anje agaishe mana da mutanen gidan,"
"zasuji insha Allah," ya amsa mata tare da kama hanyar fita daga Ιakin.
❤π€❤
Acan 6angaren kuwa har lokacin suna a falon kan junaid da Uncle abusufyan ya gama fahimtar dashi game da Su Hosana da jahad,
jiki asanyaye yace"Amma meyasa su ba suyi rayuwa atare damu ba?meyasa Abba?uncle why?cike da tuhuma yake maganar yana kallonsu,yayin da fuskarshi ke Ιauke da damuwa,
abban su ne yace"Junaid,mu kanmu bamu san dasu ba,da ace munsan da zamansu da bamu bari hakan ya faru ba,Ζaddara ce kawai ta riga fata,"
Shiru junaid ya Ιanyi yana Ζare ma su Jahad kallo,yaso ace tun fil azal tare da yaran ya taso,da ba Ζaramin kulawa zasu samu a wurin Ζ΄an uwansu ba,Allah sarki rayuwa kenan,Rashin sani yafi dare duhu,su kansu su Sehrish sae dama dama suke da sun san cewa suna da wannan family Ιin daba abunda zai hana su nemi danginsu,Tabbas an cuci rayuwarsu Ζiri Ζiri an rabasu da Ubansu kuma an hanasu danginsu,wata shari'ar dae sae a lahira,
"Nasan yanzu kowa yana jin yunwa,saboda halin da muka shiga jiya babu wanda ya samu damar cin abinci acikin mu,Yakamata yanzu komai ya wuce,Lokacin farin ciki ne,Za'a shirya gagarumar walima saboda Ζ΄an ukun mu,munaso su manta da duk wani abu da ya faru a rayuwarsu kuma su Ζaddara cewa tamkar yau ne suka faΙo duniya,ko ba haka ba"? Ya yi maganar yana kallon matasan gidan dake atsaye,Kowannansu fuskarshi asake,su fawan ne suka haΙa baki wurin cewa"Wannan haka yake Abba,In sha Allah zamu nuna masu soyayyar Ζ΄an uwantaka,har sai sun manta da dukkan wani Ζunci da suka fuskanta na rayuwarsu,' murmushi kawai Abusufyan ke saki don ba Ζaramin daΙi yaji ba,
Marshal Omar yace "Sannan kuma muna Ζara baku haΖuri game da halin da kuka tsinci kanku,duk da ba laifin mu bane,amma mun Ιaura ma kanmu laifin,Muna neman afwarku,Hosana Sehrish and Jahad,forgive us pls,'
gaba Ιaya jikinsu yayi sanyi,lokaci guda kuma sukaji wata irin soyayyar Ζ΄an uwansu ta kamasu,
Jahad ce tayi ΖoΖarin cewa"duk wani abu daya faru damu dama can rubutaccen ne!Allah ya riga da ya Ζaddara faruwan hakan,mun gode ma Allah da muka cinye wannan jarabawar,da juriya kuma da haΖuri,yanzu gashi gaba Ιayanmu muna farin cikin wannan rana da Allah ya haΙamu da danginmu,Babban abun farin cikin ma da ya kasance Uncle abusufyan shine mahaifinmu ba waccen fasiΖin mutumin ba.......'kasa Ζarasa maganar tayi saboda kukan daya zo mata,Janyota Abusufyan yayi tare da rungumeta ajikinshi,yana Ιan bubbuga bayanta,
"Ya Omar," hosana ce ta ambaci sunan shi,tana faman kumshe dariya abakinta,gaba Ιaya suka mayar da hankalinsu akanta,nuna shi tayi da yatsanta sannan ta nuna kanta,kafin ta haΙe yatsun wuri guda ta Ζullasu,Alamar ita dashi sun zama Ζ΄an uwan juna, Ζayataccen murmushi Marshal ya saki yana kallonta,
Duk wannan abun dake wakana akan idon Sgr dake atsaye,ya goya hannayenshi asaman wide chest Ιinsa,Har lokacin bai sauko ba,hankalinsa fa bazai kwanta ba har sai yayi tozali da YA SAYYADI,
Suna cikin magana muryar azmee ta katse su da cewa"Abba an kammala shirya breakfast Ιin,yakamata ku hallara a dining Ιin," tana magana idonta na akan su jahad fuskar nan Ιauke da murmushi,
Batare da 6ata lokaci ba,gaba Ιayansu suka hallara asaman zungureran dining table Ιin wanda ke shake cike tab maΖil da kayan makwalashe naci dana sha,mutun goma shabiyu yake Ιauka,akwai kuma wanda Abban su junaid yasa aka Ζara cikin wanda aka shirya walimar jiya dasu,Ansanya shi a gefen nasu mai mazaunin mutun shida,Aunty azmee ta jera wasu kayan kalacin asaman shi,anan Abusufyan ya zauna tare da su sehrish jahad da hosana,
Tun daga kan yadda kowa ke zuba abinci acikinshi zai tabbatar maka da cewar ba Ζaramar yunwa suke ji ba,ko azmee basu jiya tayi serving Ιinsu ba suka shiga zuba abincin da kansu,Sgr ne kawai tayi serving Ιinsa sae kuma Abbansu,amma sauran ba wanda ya tsaya jira,wurin yayi tsit bakajin hayaniyar komai,sai sautin Cokulla,kwas kwas kwakwasss,
Ιagowa Marshal omar yayi karaf idonshi yaci karo dana hosana,ta zuba mashi ido ko kyaftawa batayi,kasancewar table Ιinsu na kusa dana juna,tazarar kadan ce,
Da cokalin hannunshi yayi mata nuni da plate din gabanta,alamar ta mayar da hankalinta kan abunda take ci,
murmushi tayi tare da kai hannu ta dauki lemu tana korawa,
Junaid kuwa duk ya rasa samun natsuwa sam ya gaza cin abincin dake a gabanshi sae faman juya cokalin yake yi acikin plate,duk in ya tuna abunda yayi ma Jahad acikin mota amatsayin Sehrish sai yaji gabanshi ya faΙi rass,fargabar shi kada jahad tayi tunanin ko Ιan iska ne shi,tunda ba sanin shi tayi ba,kar kuma tace zata sanar ma wani abunda yayi mata,tunawa yayi da lokacin daya tsoma harshenshi acikin bakinta ya ΖanΖameta yana kissing lips Ιinta,ba iya nan ba ya tsaya har hannunshi saida ya zura ackin hijabinta
Hankali tashe junaid ya miΖe yana ΖoΖarin barin dining Ιin,hankalin kowa ya koma kanshi,
Har suna haΙa baki wurin tambayar shi ina zashi,
fuskarshi Ιauke da damuwa yace"Abba,bana jin yunwa,dama munyi breakfast tare da Mommy,zanje wurinta yanzu" Abbansu yake ma magana amma hankalinshi na akan Jahad dake shan farfesun da azmee ta zuba mata a plate,da alama ba Ζaramin daΙi farfesun yayi mata ba,duba da yadda ta mayar da hankali akanshi,
"Okey,zaka iya tafiya," ya bashi amsa,cikin sauri junaid ya kama hanyar zuwa bedroom Ιin Abbansu don acan ta sauka,yana tafiya yana waiwayen su jahad aranshi yana cewa"wayyo Allah na,bansan me zai biyo baya ba,nasan cewa dole ta sanar ma Uncle abunda nayi mata,idan ta faΙa mashi shi kuma zai faΙa ma Abban mu ne,Abban mu kuma zai faΙa ma Babban yayanmu ne,shi kuma zaice wuyana ya isa yanka tunda har na iya Sumbatar mace daga nan zaiyi tunanin turani aikin Soja abunda banso,shikenan tawa ta Ζare'
ranta ne ya bata cewar ana kallonta,hakan yasa ta tsagaita daga shan farfesun da takeyi,ta Ιan Ιago idanunta,kai tsaye suka sauka akan junaid dake can nesa dasu yana kallonsu,
Mamaki ne ya kamata ganin yadda ya Ζura mata ido yana kallonta,aranta tace"bansan meyasa yake kallona ba,tsorana kar ace baisan ganina ne,'
"Allah yasa halinta irin na Sehrish ne,idan takasance mai sauΖin kai irin na rishi Ιina nasan cewa zata rufa mun asiri,amma anya zatayi sauΖin kai?Nasan me zanyi daga yanzu zan dinga Ιaure mata fuska,in nuna kamar na tsane ta,nasan hakan ne kawai zaisa taji tsorona taΖi faΙa masu abunda ya faru atsakaninmu!good idea",
Yana kai Ζarshen zancen zucin nashi ya watsa mata harara tare da murguΙa mata baki,ya juya ya nufi bedroom Ιin abbansu,
Jiki asanyaye jahad ta Ιauke idanunta daga kallon bayanshi da take yi,lokaci guda taji komai ya fita ranta ba don komai ba sai don kallon da taga junaid yayi mata,maganarta ta tabbata,Junaid baison ganinta,tunda gashi ya harare ta kuma hada murguΙa mata baki,
Muryar daddynsu ce ta katse ta da cewa"Jahad,meya faru ne?naga kin daina shan farfesun ina fata lafiya?
firgit ta Ιanyi tare da wurga eye balls Ιinta akanshi tace"Am ok daddy,'
jinjina kansa yayi kafin yace"Ku saki jikinku,kuci abinci sosai,kada kuji komai,nasan baku saba ba,don na lura akwai rashin sabo atattare daku,amma a hankali zaku saba da Ζ΄an uwanku,'
hosana tace"Abba ae ni,nama saba da kowa,baka ga yadda nake ta cika cikina da abinci ba,jahad ce ke jin kunya,ni bana jin kunyar kowa,'
Dariya sukayi gaba Ιayansu,Sehrish na cikin sakin dariyar nan,Karaf idanunta suka haΙu dana Sgr,Ιagowar shi kenan yayi arba da ita,gabanta ne taji ya faΙi rass saboda fuskarshi a murtuke take ba annuri,nan take dariyar da takeyi ta koma ciki,ganin ta zuba mashi ido,yasa shi jefa mata harara,a hanzarce ta kawar da idanunta daga kallon fuskarshi da take yi,jikinta kuma yayi sanyi,ta shiga tambayar kanta dalilin hararar da taga big bro yayi mata,kodai baya farin ciki ne da kasancewarta JININ SA!?tabbas hakan zai iya faruwa,WataΖil kodan ya saba ganinta a matsayin Ζ΄ar aikinsa,baiwarsa,ΖasΖantacciya shiyasa yanzu Yake nuna 6acin ranshi don yana ganinta tamkar a matsayi Ιaya suke dashi,Ζ³a'Ζ΄an Wa da Ζani,da alama hakan baiyi masa ba,
"Idan har dagaske ne abunda nake hasashe,insha Allah zan tattara na bar masu gidan,saboda bana son 6acin ranshi,zan iya yin komai don farin cikin shi," ta Ζarasa zancen zucin nata tare da sake Ιagowa a hankali don ta saci kallonshi,adai dai lokacin shima ya Ζara Ιagowa da kyawawan idanuwanshi kai tsaye suka shiga cikin nata,nan take taji gabanta ya kuma faΙuwa rass,kasa janye idanuwanshi yayi daga kallonta da yake yi,a yayin da yake jujjuya spoon Ιin dake hannunsa acikin plate Ιin abincin gabansa,har Yanzu bai daina mamakin kasantuwarta Ζ΄ar uwarshi ba,ta jininsa,tamkar a mafarki haka yake ganin abun,ganin ta zuba mashi ido batare da ta janyesu ba yasa shi Ιaure fuskarshi yasha murrr,saboda kada ma yarinya taga fuska har tayi tunanin raina sa don tasamu matsayi,
"U will still remain who u are,wadda take aiki a ΖarΖashina,Matsayin dana baki kenan,"ya fada a ransa
Murmushi Abusufyan yayi tare da cewa"bazasu kara wahala ba,bazan ta6a bari hakan ya faru ba,tunda dae har yaran nan suka bayyana a matsayin Ζ΄a'Ζ΄ana,In sha Allah bazan Ζara bari suyi aikin wahala ba,ko cokali bazan Ζara bari Ιaya daga cikinsu ta Ιauko ba acikin gidan nan,rayuwar hutu kawai nake so suyi rayuwar Ζ΄anci," ya Ζarasa zancen zucin nashi a yayin da yake bin kowaccen su da kallo cike da so da Ζaunar Ζ΄a'Ζ΄an nashi,'
Janye idanunshi yayi daga kan nata,kafin ya miΖa hannu tare da Ιaukar Glass cup mai Ιauke da abun sha me sanyi ya kai shi saitin mouth dinsa yana sipping Ιinshi anatse,yayin da sanyin lemun ke ratsa throat Ιinsa,a hankali ya lumshe idanunsa tare da Ιan ware su kaΙan,again suka Ζara sauka akan na sehrish a karo na uku kenan,agaggauce tayi hanzarin janye idanunta daga kan fuskarshi ta mayar dasu akan plate Ιin abincin dake a gabanta,
Hannu Sgr ya sanya tare da yago tissue ya goge bakinsa,kafin ya miΖe tare da juyawa ya nufi upstairs,MiΖewa Marshal yayi da alama shima ya kammala breakfast Ζin nasa,shima upstairs ya nufa,
Fitowar Hajiya azeema keda wuya daga cikin bedroon Ιinta,ta jiyo muryar gwaggon katsina tana ta faman sambatu tana cewa"Tsiyarta kenan mutun yazo gidan Ζ΄an gayu,Ni bazan iya rayuwar turawan nan ba,taya za akai ma mutun salalar biredi tare da tea rabin kofi kamar wata Ζ΄ar iska ace in sha"?
Tafiya take tana sambatu zaninta a hannu sai Ιan undi ajikinta,kanta kuwa ta kifa wannan Ιaurin Ιan kwalin nata mai kama da helmert,
har zata gifta hajiya azeema tayi gyaran murya tare da ambaton sunanta"Goggo," fuska a yamutse ta juyo tana kallonta,dawowa tayi daga gefenta suna fuskantar juna tace"Yawwa azeema,wai nikam inaso in tambayeki,'
Natsuwa hajiya azeema tayi tare da cewa"ina sauraronki gwaggo,"
"Jiya nayi wani mafarki,Ζ΄a'Ζ΄an abusufyan sun bayyana,wasu Ζ΄an uku kyawawan gaske,da nayi tunanin koda gaske ne abun ya faru amma daga baya na gane ba gaskiya bane,in ba haka ba,yaushe abusufyan ya ta6a yin aure"? Tayi tambayar tana kallon hajiya azeema,wadda ta saki baki tana kallon gwaggon,
Ganin azeema tayi sototo tana kallonta yasa tayi tunanin cewa ko abunda ta faΙa ya bata mata rai ne,
"Nasan dole kiyi mamaki kema,Mafarkin fa kamar dagaske,Ιaya daga cikinsu har tana sharara mana labarin Ζarya waisu Ζ΄a'Ζ΄an wata zainabu ne,kuma ma acikin labarin hada wata hajiya Ameena,in banda shaiΙan ina abusufyan ina Ζ΄a'Ζ΄a"?
Ζiris ya rage Azeema ta fashe da dariya agaban gwaggon katsina,ganin yadda ta haΖiΖance tana kora mata bayani,kuma babu alamun wasa a fuskarta,
Ζunshe dariyar bakinta tayi tare da basar da ita tace"Gwaggo Anya kina shan maganinki kuwa?ina Dr harris yake?gaskiya inason ganinshi,'
Tsoki gwaggon katsina taja tare da cewa"Harrisun daya zama Ιan iska,"
Waro ido waje azeema tayi tace"gwaggo harris ne Ιan iska"?
ta6e baki tayi tare da cewa"Zan masa Ζarya ne?ba Ιan cikina bane"?nasha wahalar yima yarona tarbiya amma waccen sauden.....'kasa Ζarasa maganar tayi saboda kukan daya ciyota,zanin hannunta takai saitin idonta tana ΖoΖarin goge hawayenta,
Zuru harris yayi wanda fitowarshi kenan kuma atare da saude suka fito,jin maganar gwaggone ma yasa yayi hanzarin cire hannunshi daga cikin na sauden,
Hajiya azeema tace"gwaggo faΙamun me harris Ιin ya akaita,?
Hankali tashe Saude tace"ya harris pls kada ka bari gwaggo ta faΙa mata abunda muka aikata,kasan gwaggo yadda take Ιaukaka abu,inta tashi faΙi saita Ζara ma miya gishiri,'
Dr harris yace"just don't worry ur self,insha Allah bazata faΙa mata ba,"
FaΙin hakan keda wuya gwaggon Katsina tace"Azeema abun da ciwo,yanzu yunwa nake ji,shiyasa ma kika ga nafito ina sambatu,Wurin waccen matar zani,wlh ba azmee ba Allah yasa ramadan ce ita yau saina zazzaga mata rashin mutunci!Ni zata raina ma hankali tunda safe,takawo mun tea rabin kofi da salalar biredi wai in fara da wannan,don ta raina mun hankali,nayi mata kama da kusu ne?
Rai a6ace tayi maganar,aikuwa atare haris da saude suka fashe da dariya,a hanzarce ta juyo sakamakon jin sautin dariyar tasu,nan take ta tsuke fuska ganin shi tare da saude,
Murmushi Hajiya azeema tayi tare da cewa"haba gwaggo baki fahimce ta bane,cewa fa tayi ki fara da wannan tana nufin kafin ki tashi fitowa zuwa yin breakfast Ιin,yanzu haka yana can an shirya mana mu kawai ake jira muje muci namu kalacin,"
Hajiya azeema ta Ζarasa maganar tare da ruΖo zanin hannun gwaggon tace"Bari na taimaka maki ki Ιaura shi,"
Girgiza kai tayi tare da cewa"Barmin shi a hannuna,nafison inji iska na shiga ta ko'ina,"murmushi hajiya azeema tayi kafin tace"hakan ma yayi gwaggo,ae under skirt din ma bamai sharashara bane,yana da kauri,amma duk da haka dae ki Ιaura zanin yadda zaki fito da kyau tunda ga rigarshi kin sanya ajikinki,Kuma kinga Abusufyan na nan,Ga kuma Ζ΄a'Ζ΄ansa,bazasu so suga gwaggonsu a haka ba,"
wani irin Ζayataccen murmushi gwaggon katsina tasaki tare da cewa"Kenan dagaske ne Mafarkin da nayi jiya"?
Jinjina kai Azeema tayi tace"Ae suna nan,duk abunda ya faru jiya dagaske ne,ba mafarki kikayi ba,agabanki akayi komai kin dai shafa'a ne,'
Jin haka yasa tayi saurin mayar da zanin ajikinta tana Ιaure shi tana cewa"Allah sarki Ζ΄a'Ζ΄an abusufyan Ιina,bayin Allah,sunsha wahala a hannun wannan fasiΖin mutumin baΖin shaiΙani,Allah mutumin nan Ζaho ne kawai bai fito masa aka ba,amma ina tantama anya ba Irin shaiΙan bane"?
"gwaggo kidaina maganarsa ma,Ni wlh ko zancen shi ma bana so anayi,Na tsani mutumin nan kamar yadda natsani mutuwa ta,"acewar hajiya azeema,tayi maganar ne a yayin da take kama hanyar Zuwa Dining area Ιin nasu,bin bayanta Gwaggon tayi tana cewa"Ae ko sai dai ki toshe kunnanki,don zancen sayyadi ya zama dole,in har ba'a kawo min kansa ba,bazan daina faΙan sunan shi ba,'
Murmushi kawai hajiya azeema tayi,atare suka Ζarasa dining area din,
Gaggaisawa suka fara yi da junansu,su jahad na ganin saude suka tashi atare suka nufe ta,dama Jiya basu samu damar gaisawa da ita ba,saboda yanayin da suka shiga gaba Ιayansu,haΙasu tayi ta rungume ajikinta,cike da farin ciki tace"Ina tayaku murna sosai,nayi farin ciki sosai,Ya harris ya sanar dani komai agame daku,ashe ku jininsu ne,'ta Ζarasa maganar ayayin da take raba jikinta daga nasu,kowannansu fuskarshi Ιauke da murmushi,Jahad tace"Aunty saude kinga ikon Allah ko?munsha wahala sosai,mu kanmu bamu ta6a tunanin cewa muna da dangi ba,amma sai gashi Ζaddara ta haΙamu da ya Omar,Ita kuma Ζ΄ar uwarmu Sehrish Ζaddarar aikine ya kawota gidan nan,Muna tare da Ζ΄an uwanmu ba tare da mun sani ba,sae gashi rana Ιaya Allah ya bayyana mana komai,'
Saude tace"Congratulations Once again,ina Ζara tayaku murna sosai da kuka fito daga tsatson wannan Family Ιin,abun alfahari ne wannan"kafin ta mayar da idanunta kan Hosana,Cike da zolaya taja kumatunta tare da cewa"Hosana Kinga yadda kika canza?kamar ba wannan Sha takwas sha taran ba,mai Ιan kai,kinyi kumatu kamar Balon balon,Ga haske gaskiya ya Omar ya Iya raino,"
Fashewa da dariya hosana tayi tana faman sunnar dakai,
"Kiyi ma sister Ιinku mana,Ita bazata taso mu gaisa ba"?tayi maganar tana kallon sehrish dake zaune,tana faman kallonsu Ιaya bayan Ιaya,
Murmushi jahad tayi tare da juyawa tayi mata alamar ta taso da hannunta,
MiΖewa sehrish tayi tare da nufar inda suke,koda ta Ζaraso saude ta sanya hannu tare da janyota ta rungumeta,kafin ta raba jikinta dana sehrish tace"Masha Allah,gaskiya ban ta6a ganin triplet,masu kama iri Ιaya sak kamar taku ba,ina taya ki murna sosai da Allah ya haΙaki da Ζ΄an uwanki,da kuma mahaifinku,da kuma danginku,'
Fuskar sehrish Ιauke da murmushi tace"Ngde sosai,"
"Allah ya tsare mana ku,Ya Albarkaci rayuwarku ya kuma kare ku daga sharrin maΖiya,'
Atare suka amsa mata da Ameen,bama su kadae ba,hadasu Abba dake sauraron maganganun nasu,
Kamar yadda Abba yayi alΖawarin shirya gagarumar walima na bayyanar Ζ΄a'Ζ΄an Ζaninsa Abusufyan,Da kanshi ya fidda date Ιin da za'a gabatar da ita,Kuma tun aranar ya fara kiran Ζ³an uwa da abokanan arziΖi yana sanar dasu game da Ζ΄a'Ζ΄an abusufyan da suka bayyana,Babu wanda bai bari ba,kowa kira yake tun daga kan danginsu na Zaria,na damaturu dana sauran states Ιin da kuma waΙanda ke zaune Ζasashen waje,kowa saidaya sanar mawa,Bayan Abbas ya koma gidane da safe Amani ke tambayarshi meya faru ne jiya ya hanasu zuwa gidansu,Anan ya kwashe duka abunda ya faru game da su Sehrish ya sanar mata,wani irin farin ciki ne ya cika ta,Ba don komai ba sai don sanin cewa plan Ιin Aunty babba ya gama Tarwatsewa,ae tunda taji cewar Ζ΄an mata ne kuma sun kai shekara goma sha bakwai zuwa sha takwas kyawawan gaske,Nan fa ta kwashe da dariyar mugunta aranta tana cewa Naga yadda za'ae Aunty laila ta cimma burinta,Gida bai Ζoshi ba taya za'a ba na waje,Ae tuwona maina za'ayi,Haba ae xance ya Ζare,
ita kanta Amani ta Ζosa ranar walimar tazo saboda suje gidan,saboda taji cewar Aranar Aunty babba da hafsat zasu zo Abuja,babban burinta taga tashin hankalin da aunty babba zata fuskanta inta gansu,
Ranar walimar kuma yayi dai dai da ranar da Ammi zata zo,tare da wasu daga cikin danginsu,haka zalika captain Najeeb da kuma Talal suma duk a ranar zasu dawo gida,ba don komai ba sai don su sanya Ζ΄a'Ζ΄an uncle Ιinsu abusufyan acikin idanunsu,Kowa Ιokin ganinsu yake yi kamar kamar me,musamman da sukaji irin rayuwar da yaran sukayi a wulaΖance sai suji wani irin tausayinsu da kuma Ζaunarsu ya shiga cikin ransu,kuma duk aranar MG Osman da kuma Captain Adam suma zasu dawo gida,wanda tun dawowarsu daga U.s suka tafi sada zumunci,Gaskiya wannan Babbar rana ce,Hakan yasa ma Zamuyi shiri na musamman ni da makaranta littafina don mu halarci gidan amatsayin gayyar soΙi tunda ba'a gayyace mu ba,Sa kaine kawai,
Cikin Ζ΄an kwanakin nan wata irin rayuwar farin ciki suke gudanarwa tare da Daddynsu,kullum yana manne dasu,Da kanshi ya zauna yayi masu kitson kalaba guda bibbiyu akansu kamar yadda ya ta6a yi masu suna yara,koda yazo kan Sehrish,Cike da mamaki yace"Ya akai naga gashin kanki guntu?ko kinyi wani ciwo ne dayasa aka datse maki gashin,"girgixa kai tayi tare da cewa"a'a Laifi nayi ma Babba yaya shine ya yanke mun gashin da almakashi,"
da buΙar bakin Abusufyan sai cewa yayi"Yayiwa kanshi ai," murmushi sehrish tayi duk da batasan me daddyn nasu yake nufi da hakan ba,duk a wannan kwanakin basu je school ba,Abusufyan da kanshi yace kada su damu shi da kanshi zai kaisu makarantar don karma a tuhume su,
A 6angaren Sir Commander haroon kuwa,tamkar munafuki haka ya koma acikin gidan,ba kowa ma ke sanin lokacin da yake shigowa gidan ba,da kuma lokacin da yake fita,Da alama dae akwai wani abu da yake shiryawa a 6oye,
*AMRISH*
Zaune take acikin class Ιin gaba daya ta shiga damuwar rashin ganin Sehrish kwana biyu ko layinta ta kira bata samu,hatta wayar junaid ta jaraba kira shima ba'a Ιagawa,hakan ba Ζaramin tayar mata da hankali yayi ba,tagumi tayi idonta cike tab da hawaye saboda damuwar da take ciki,taso ace sehrish na nan atlease zata Ιebe mata kewa,tana cikin wannan tunanin har malam ya shigo cikin class Ιin nasu bata sani ba,bayan ya kammala amsar gaisuwa daga wurin student din,kai tsaye ya Ζarasa seat Ιin da Amrish take,hannun shi yakai wanda ke ruΖe da maker ya Ιan bubbugi desk Ιinta,a firgice takai idanunta akanshi,YunΖurawa tayi tare da miΖewa ganin Ya mu'allim,wanda tun ranar daya ba sehrish Ruwan addu'ar nan bai Ζara zuwa makarantar ba,duk da sun samu labarin cewar Ya tafi Umra ne,shiyasa aka musanya masu shi,
Murmushi ya Ιan saki afuskarshi yana kallonta yace"tunanin me kike yi ne?har na shigo cikin class Ιin baki sani ba?
Muryarta na rawa tace"Ayimun afwa ya mu'allim,Bana jin daΙi ne bansan ka shigo ba,
Jinjina kanshi yayi tare da Ιan kai idanunshi kan Seat Ιin sehrish yace"Ina yarinyar nan take?Ζ΄ar family Ιin Salahuddeeen hussein naga kamar bata a class Ιin"?
fuskarta Ιauke da damuwa tace"Batazo ba,yau kusan kwana huΙu kenan bata zo school ba,kuma nayi trying kiran layinta amma bana samu,har brother Ιinta na kira,shima layinsa ba'a samu,'
Jin hakan yasa shi fargabar to kodai wani abu ya faru da yarinyar?Yaso yaji ya tayi da ruwan addu'ar daya bata,shin tasha ko bata sha ba?
Jinjina kanshi yayi tare da juyawa yace"Allah yasa dae lafiya,in har batazo ba,zuwa sati mai zuwa zan je gidansu don na binciki dalilin rashin zuwan nata,'
Jiki asanyaye Amrish ta koma ta zauna,saman seat Ιin nata,jikinta har ya fara kerma saboda tsoran kar ace wani abune ya faru da Sehrish,
A Ζarshe dae ta yanke shawarar neman gidansu don taje ta ganta da kanta.
*SANARWA SANARWA*ππππ
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
*πBoss Batureπ*
Join this link to follow my tiktok acctπ
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
ΩΨ΅Ψ© ΨΨ¨ Ψ±ΩΩ Ψ§ΩΨ³ΩΨ© Ψ¨ΩΩ Ψ³ΨΨ±ΩΨ΄ ΩΨ§ΩΨ¬Ψ±Ψ§Ψ Ψ§ΩΨΉΨ§Ω Ψ±ΩΨ§ΩΨͺππ❤π€❤ππ*

Hannu yasa tare da tallabo fuskarta yace"Hosana bada sani na nayi maki hakan ba,laifin ki ne,meyasa zaki toshe mun hancina?so kike na mutu'?
Girgiza kai tayi"a'a,banso ka mutu,ae ni wasa nayi maka ko,"tayi maganar tana satar kallon fuskarshi,
"FaΙa mun me ya kawoki bedroom Ιina har saman gadona"?
A Ζule tace"nifa nazo ne na tashe ka don kaje ka ci abinci,naga kowa ya fito banda kai,kuma zasu iya cinye abincin duka,"
fuskarshi Ιauke da murmushi yace"Waya faΙa maki za'a cinye abincin,ae ko ban fita ba Azmee zata kawo mun ne har cikin part Ιina,"
Shiru tayi tana faman sauke ajiyar zuciya,Ιagowa ta Ζara yi zata saci kallonshi suka haΙa ido,ganin yadda yake kallonta ko Ζyaftawa baiyi hakan yasa ta Ιaure fuska cikin shagwa6a tace"Ya omar wannan kallon fa,ka wani tsare ni da ido,"
yadda tayi maganar ba Ζaramin burgeshi tayi ba,ya jima yana kallonta batare da yace wani abu ba,har sai da ta hasala rai a6ace tace"shikenan tunda ba zaka mun magana ba,bari na tashi na tafi,dama ko abincina banci ba,saboda kawai inzo in tashe ka daga bacci,amma ko farin ciki ba kayi ba,'
Ajiyar zuciya ya sauke tare da ruΖo hannunta cikin nashi"Hosana,so nake ki faΙa mun gaskiya,kina sona da gaske?kuma zaki aure ni? Waro ido waje hosana tayi tana kyakkyaftasu kamar na Ζ΄ar tsana jin abunda yace,a ruΙe tace"Ya Omar!aure fa!"_
Jinjina mata kai yayi tare da cewa"eh,aure hosana ko baki shirya ba,"
Turo baki ta Ιanyi tana ΖunΖuni Ζasa Ζasa,hankalinsa kam harya Ιan tashi saboda ganin yadda ta tsorata don yayi mata zancen aure,dama fargabarsa kada sai anje wurin nema mashi auranta tace bata shirya ba,don yasan ba cikakken hankali gare ta ba,
Lalla6ata ya shiga yi"pls hosana,ki faΙamun gaskiya,zaki aure ni"?
daΖyar ta iya buΙe baki tace"Ni yanzu tashi zanyi in tafi,dama zuwa nayi fa don in tambayeka,wani kalar Ζunshi kake so ayimun baΖi ko ja,"
ya lura cewa batason zancen auren shiyasa ta kawo maganar Ζunshin,cikin sanyin murya yace"Nafison jan lalle zai fi yi maki kyau,kuma ba mai yawa ba Ζunshin,Ζ΄ar flower kawai za'a zana maki mai kyau,"
Yana kai Ζarshen maganar,hosana ta miΖe tana faman shan Ζamshi,da sauri ta juya ta bar bedroom Ιin nashi,bin bayanta yayi da kallo har ta fuce,jiki asanyaye ya miΖe tare da nufar toilet ya shige,
Hosana na fita daga cikin bedroom Ιin nashi,a falonsa ta tsaya tana faman zabga murmushi,tsabar farin ciki kamar ta zuba ruwa a Ζasa tasha,Yau ya Omar ya nuna yana sonta harma yanayi mata zancen aure,ta rasa ma wa zata fara faΙamawa,sai faman zagaye zagaye takeyi a cikin falon,
Wuraren Ζarfe biyu da rabi na rana,Abusufyan ya Ιaukesu acikin motarshi kamar yadda yayi masu alΖwarin kaisu wurin saloon da kanshi,hosana da jahad suna a bayan motar duk sun Ιau wankan jallabiya sun laga mayafi,Sehrish na agaban motar kusa da driver seat inda Uncle abusufyan ke zaune yana driving Ιinsu anatse,Su jahad da hosana sae fira sukeyi tare dashi,amma ita ko uffan bata tanka masu ba,dama tunda ta shigo cikin motar Abusufyan ya lura da yanayinta,
gyaran murya yayi mata hakan yasa ta Ιan dago da kanta ta kalle shi,
"Meyake damunki ne Daughter?tunda kika shigo cikin motar nan baki tanka mana ba,ga Ζ΄an uwanki suna ta fira a tsakaninsu amma ban dake".
Muryarta asanyaye tace"Babu komai,"
"ko don saboda na hana ki kai ma Sgr abinci ne"? Yayi maganar batare daya kalleta,
Cikin sauri tace"a'a ba haka bane,kawai bana jin daΙin jikina ne,"
"Ban yarda ba daughter,saboda shi ne yasa kika shiga damuwa,"_
Shiru tayi bata ce komai ba,murmushi abusufyan yayi kafin yace"banyi hakan don na takura maki ba,face don na Ιaukaka darajarki,nasan ba zaki fahimce ni ba a yanzu amma nan gaba da kanki zakiyi mun godiya akan hakan,idan kuma hakan ya 6ata maki rai,kiyi haΖuri,'ya Ζarasa maganar adai dai lokacin da suka Ζaraso wurin Saloon Ιin,parking Ιin motar yayi jahad da hosana suka fita waje,tana ΖoΖarin buΙe motar ta fita ya ambaci sunanta"Sehrish,"juyowa tayi tare da kallon fuskar daddyn nasu tace"Na'am daddy,"
"Murmushi kawai nakeso kiyi mun kafin ki fita,"
fashewa tayi da dariya har fararen hakoranta suka bayyana,duk a tunaninta wani abu mai muhimmanci ne yasa ya kirata,ashe kawai don ya tambayi murmushinta ne,shima dariyar yakeyi,kafin su fita daga cikin motar atare,
**************
Fitowarshi kenan daga wanka,yana cikin shirya kanshi cikin riga da wandon jeans,yaji an kwankwasa Ζopar Ιakinshi,daga muryarshi yayi tare da cewa"Ζopar a buΙe take,"yayi maganar tare da juyawa yana kallon mai shigowar,
Cike da mamaki yace"Ya HAROON!kaine!dama kana nan,"
Shu'umin murmushin nan nashi ya saki tare da Ζarasa shiga cikin bedroom Ιin nashi yana cewa"Ina nan mana junaid,kaine ka manta dani,kowa ma ya manta dani,"
"Ya haroon ba haka bane,wlh ni ban manta dakai ba,kana araina,"
ta6e baki haroon yayi alokacin da yake tsayawa agaban junaid suna fuskantar juna yace"Ka Ζara kyau da haske,hankalinka kwance baka da wata damuwa,ba kamar ni ba,kullum cikin damuwa nake,zuciyata har nauyi takeyi mun saboda halin da nake ciki amma babu wanda ya damu dani,yau ko mutuwa nayi babu wanda zai damu,sae ma farin ciki da za'ayi,"
Jin wannan maganar ta haroon yasa jikin junaid yin sanyi,wani irin tausayin shi ya kamashi,muryarshi tamkar zaiyi kuka yace"pls Ya haroon dan Allah kadaina faΙin wannan maganganun,wlh bana jin daΙi,"
"Junaid Ζarya nayi ne?an damu dani acikin gidan nan ne?kowa yayi watsi dani,babu wanda ke damuwa dani,tamkar bare haka nakeyin rayuwata,hatta azmee da take Ζ΄ar aiki acikin gidan nan ta fi ni muhimmanci tunda ita ana damuwa da ita,ni kuwa fa?
Hawaye ne suka cicciko a idanun junaid,dama shi akwai tausayi,gaba Ιaya tausayin haroon ya kamashi,saboda duk abunda ya faΙi gaskiya ne,ba'a damu dashi ba,ko zancen shi ma babu maiyi acikin gidan,idan zai share wata a waje babu mai tambayar ina yaje,
"Tamkar maraya ni fa haka nake acikin gidan nan,kalli kaga yadda na koma duk na rame saboda damuwa,gaskiya ni bazan iya cigaba da rayuwa ba junaid,zan kashe kaina ne kowa ya huta," yana kai Ζarshen maganarshi ya juya da sauri zai bar Ιakin,
Da gudun gaske junaid ya rungumoshi ta baya tare da fashewa da matsanancin kuka yana cewa"Meyasa ya Haroon!pls stop saying that,banason jin kana zancen mutuwa,ko kowa bai damu dakai ba,Ni nadamu dakai,ko don saboda ni ya haroon kada ka aikata hakan,idan ka kashe kanka,nima bazan rayuwa ba,zan bi ka mu tafi tare,"
Wannan kalaman na junaid ba Ζaramin sanyaya mashi zuciya su kayi ba,cire hannunshi yayi daga ruΖon da yayi ma waist dinshi,sannan ya juya suna fuskantar juna yace"Junaid dagaske ne ka damu dani?kuma bakaso in mutu"?
cikin shessheΖar kuka junaid yace"Eh ya haroon bana so pls,"
Hannu haroon yasa yana share mashi hawayenshi,kafin daga bisani ya janyo shi ajikinshi tare da rungume shi sosai ajikinshi,kamar zai mayar dashi cikin shi,saitin kunnanshi yakai bakinshi tare da cewa"I love u so much junaid,cos you're so special,in dai zan kasance tare dakai bazan ta6a shiga wani Ζunci na rayuwa ba,kallon ka kawai zai iya sanya farin ciki a cikin zuciyata,daga yanzu inason ka zama abokina junaid,saboda ka dinga Ιebe mun kewa,muna fita yawo atare,don bani da aboki,nifa kowa gudu na yake yi,bansan meyasa ba,'ya Ζarasa maganar tare da janye junaid daga jikinshi,
"Junaid!ka amince zaka zama abokina"?
Jinjia kai junaid yayi tare da cewa"Eh,na amince,amma dan Allah ya haroon kadaina zancen zaka kashe kanka,banjin daΙi banso pls,"
"Shikenan na daina,daga yau kome kakeso ma zanyi,am sorry na sanyaka zubar da hawayenka,"
"Ya haroon ni zanje nayi ma Abba magana akanka,nasan abba zai fahimce ni,"
cikin sauri haroon ya ruΖo hannun shi tare da cewa"A'a junaid,just leave it,banason kowa yasan meke tsakanina dakai,kada kayi ma kowa maganata don ba lalle su fahimce ni kaman yadda kai ka fahimce ni ba,"
"Shikenan bazan faΙa ba,"
"Yawwa junaid Ιina,Yanzu zan barka ka Ζarasa shiryawa,"
Yana faΙin hakan ya juya tare da fucewa daga Ιakin junaid,ya koma bedroom Ιinsa,agaban dressing mirror Ιinshi ya tsaya yana Ζarewa fuskarshi kallo,
A hankali wannan mugun murmushin nashi ya soma bayyana akan fuskarshi,fashewa yayi da dariya kafin daga bisani ya Ιaure fuskarshi,kalaman junaid ya shiga tariyowa,tuni jikinshi yayi sanyi,ta wani 6angaren ji yake tamkar bazai iya ba,amma bai da wata mafita daya wuce wannan!
"Junaid kada ka damu zamu mutu atare,"ya faΙi hakan tare da komawa ya zauna daga gefen gadonshi,
Bayan junaid ya kammala shiryawa,saukowa downstairs yayi har lokacin jikinshi ba kwari,haroon ba Ζaramin tausayi ya bashi ba,A main palor ya samu Abbansu tare da Momnynsu dasu Twins suna fira atsakaninsu,tunkararsu yayi fuskarshi Ιauke da murmushi,suna haΙa ido da Abbansu ya watsa mashi harara,sunnar da kai Ζasa junaid yayi da wurin Abban yaso ya fara zuwa amma wannan hararar da yayi mashi ce tasa ya fasa zuwa ya wuce wurin mommynsu,dukawa yayi tare da manna mata kiss kafin ya rungumeta,fuskarta asake tace"My romeo,"Amsa mata yayi da mommy,a lokacin daya koma wurinsu twins suna gaisawa,Jahan yace"Ina zuwa naga key Ιin mota a hannunka,"
"Zanbi su uncle ne," ayaan yace"Kada ka bari Mommy taji to,in ba haka ba bazata bari kabi su ba,"
"Saboda me"?ya tambaya yana kallonshi,Jahan ne ya bashi amsa da cewa"Saboda bazata barka ba,idan ta tambayeka ina zaka je,sae kace mata gidan abokinka zakaje,"duk wannan maganar da sukeyi a kunnan abbansu saboda yana kusa dasu,kallonsu kawai yakeyi,juyawa junaid ya Ιanyi tare da satar kallon mommyn,idonta na akanshi hakan ya tabbatar mashi da cewar so take taji me suke cewa,'
"Ka tafi kawai,"acewar ayaan,
harya juya zai tafi ya tuna da Abbansu,dawowa yayi tare da zuΖunnawa agabanshi yace"Abba,"Ιaure fuska abba yayi batare da ya tanka mashi ba,
"dan Allah kayi haΖuri abba in na 6ata maka rai,bazan Ζara ba,"
Ta6e baki abba yayi tare da cewa"Junaid kenan,ae ni yanzu babu ruwana dakai,kafi Ζarfi na,"_
Ashagwa6e ya kuma cewa"pls abba,kayi hakuri,ka manta da abunda ya faru jiya,bazan Ζara ba,"
"Naji,tashi ka tafi,ka kulamun da kanka,"
Murmushi junaid ya saki tare da mikewa ya manna mashi kiss a fuskarshi,sannan cikin sauri ya kama hanyar fita,
"Junaid ina zuwa"? Jin muryar Momnynsu yasa shi dakatawa da tafiyar da yake yi,
tsayawa yayi tare da juyawo ya kalleta,
"Mommy gidansu abokina zani je,"
"Kai da wa?waye zai kai ka?
Nuna mata key Ιin motarshi yayi kafin yace"Ni zan kai kaina,"
Jinjina kai tayi tare da cewa"Okey,u can go," da sauri ya fuce daga cikin gidan,
Mayar da idanunta tayi akan abbansu tace"Dama inaso inyi magana dakai,wai meyasa kuka bar romeo yana Driving da kanshi?Also babu wani security guard dake tsaronsa,Shi kadae yake yawonshi,"
Abba yace"Allah xai tsare mana shi,"
Alexandra tace"Nasan da wannan,Amma wannan babban ganganci ne,koda ace kowanne daga cikinsu zaiyi yawonshi batare da security guards ba,amma bai kamata ace kamar junaid Ζaramin yaro yana yawo shi kaΙae ba,ba wani tsaro atare dashi,Especially yadda kowa ya sanya mashi ido,gaskiya ni hakan bai kwanta mun araina ba!!"
shiru abbansu yayi yana nazarin maganarta,
Jahan yace"Gaskiya Abba,maganar mommy gaskiya ne,yakamata ace junaid akwai security guards dake tsaronsa duk inda zaije,musamman a wannan yanayin da muke ciki,bibiyar rayuwarmu akeyi don kawai acutar damu,junaid kuma yafi kowa Ζaranta acikinmu,yana buΖatar security,"
"Abunda nake ΖoΖarin fahimtar dashi kenan,"acewar mommnynsu,
jinjina kai Abba yayi tare da cewa"hakane,zanyi wani abu akai',
daga nan suka cigaba da tattauna a tsakaninsu,
*Boss Bature*
Tun bayan da Hayaam ta tura ma Aunty babba hotonsu hosana,bata samu damar duba hoton nasu ba,ko whatsapp Ιinta bata shiga ba,wayarma tana ajiye cikin bedroom Ιinta,Shirye shiryen zuwa walima kawai sukeyi,atare da hafsat suka fita saloon daga nan za'ayi masu Ζunshi,bayan nan kuma zasu biya Shopping mall,saboda siyayyar da tace zatayi ma Ζ³a'Ζ΄an uncle Ιinsu,basu suka dawo gidan ba sai wuraren karfe shida na yamma agajiye suka dawo,kowa ya wuce bedroom Ιinshi,Aunty babba na shiga Ιakinta,kai tsaye ta faΙa saman gadonta ta shiga sharar bacci,Hafsa kuwa saida ta fara yin wanka,ta canza kayan jikinta izuwa riga da skirt marasa nauyi,sannan ta fito falo ta kwashe shopping bags Ιin da suka bari a falo,takaisu Ιakinta,tana cikin dudduba kayan wayarta dake ajiye gaban mirror ta shiga ringing,hannu takai tare da Ιaukar wayar tana kallon screen Ιinta,ganin Sunan Aunty Hayaam ya bayyana akan secreen Ιin wayar,yasa ta Ιaga kiran tare da karawa a kunnanta,
"Assalamu Alaikum aunty hayaam,'
Ko amsa mata sallamar batayi ba tace"Hafsat ina Aunty laila take ne?tun da sassafe na tura mata hoton bata duba ba,har nagaji da jira,"
Hafsat tace"yanzu muka dawo daga kasuwa agajiye,tana a bedroom Ιinta ina jin bacci ne ya dauketa,ko inyi mata magana ne"?
Hayaam tace"A'a,kawai idan ta tashi ki sanar da ita cewa na tura mata hoton Ζ΄a'Ζ΄an abusufyan Ιin,ta duba ta whatsapp Ιinta,"
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e hafsat,muryarta na rawa tace"hoton Ζ΄a'Ζ΄an Abusufyan dinmu!zan sanar mata kuwa,"
Rejecting call Ιin tayi,da gudu ta fito daga bedroom Ιinta,kai tsaye ta haye upstairs Ιakin aunty babba,tura kopar Ιakin tayi tare da shigewa ciki,a kwance ta samu aunty babba saman gadonta sai sharar bacci takeyi,ga wayarta ajiye agefenta,
Cikin sanΙa takai hannu tare da Ιaukar wayar,ta danna power Ιinta ta kawo haske,ganin akwai password yasa ta Ιan bubbuga kafarta tana cewa"Kai mommy,yanzu dole sae kin tashi sannan zan samu damar ganin hoton babies Ιinmu!gaskiya ni a Ζagare nake,"
Tana cikin maganar,ta tuna da finger print Ιin dake akwai ajikin wayar,nan take zuciyarta ta bata shawarar cewar me zai hana,ta lalla6a ta hau saman gadon,ta dangwalo yatsan aunty babba,kota samu wayar ta buΙe,Good idea,ta furta hakan tare da lalla6awa ta hau saman gadon,cikin sanΙa ta Ζarasa inda aunty babbar take,hannunta ta ruΖo tare da sanya yatsan hannunta a wurin,ya rubuta mata wrong,haka ta dinga bin yatsun hannun aunty babba tana jarabawa,har sai da taci nasarar buΙe wayar,saukowa tayi daga saman gadon,ta tsaya atsaye,hannunta har kerma sukeyi wurin daddana wayar,tsoranta kar Aunty babba tafarka saboda tasan halin Mommyn nata,ta tsani wani ya Ιaukar mata wayarta,kamar mara gaskiya,
Tana shiga whatsapp Ιinta,sai ga wani security Ιin,rai a6ace tace"Mommy kamar mara gaskiya,duk tabi waya ta garΖame da security,"
Allah yaso shima finger print ne,komawa tayi tare da dangwalo yatsan aunty babba,whatsapp Ιin ya buΙe,
Kaitsaye ta shiga chat Ιinsu da Hayaam,anan taga hoton da Hayaam ta tura mata,bai buΙe ba hoton saboda data a kashe take,cikin sauri hafsat ta kunna data Ιin,nan take yashiga loading yana ΖoΖarin budewa,a hankali hoton ya soma bayyana,Ζura ido hafsat tayi tana jiran hoton ya kammala buΙewa,
Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu ji kake Daram!!Dararam!!tamkar ana buga ganga,Waro ido waje hafsat tayi agigice a matukar razane,tamkar wadda taga Zombie,hankali a matuΖar tashe tace"Kai!!!"
Hannunta har kerma yakeyi wurin yin zooming Ιin hoton nasu ta matso dashi kusa don tagani dakyau,gaba Ιaya tagama kiΙima,wata irin zufa ce ta soma tsattsafo mata agefen fuskarta,daΖyar take iya haΙiye yawun bakinta saboda maΖoshinta daya bushe Ζamas,juyawa tayi ta kalli Aunty baba dake ta faman mutsu-mutsu alamar zata farka daga baccin da takeyi,aikuwa cikin sauri tayi deleting Ιin hoton gaba daya,sannan ta rufe wayar,tayi wurgi da ita asaman gadon,jikinta na kerma ta fuce daga dakin,gudu gudu sauri sauri haka take tattaka stairs Ιin Ζiris ya rage ma tayi tuntu6e saboda yadda jikinta ke rawa kafkaf kamar wadda sanyi ya kama,
Bedroom Ιinta ta koma,tana shiga ta aza hannu akai tana faΙin"Tashin hankali!In har dagaske ne abunda idanuna suka gane mun acikin hoton nan kenan hakan na nufin cewa HOSANA DA JAHAD Suna araye kuma suna a gidansu daddy!taya hakan ya faru?Kenan Ya Omar shine ya Ιaukesu?Ina wannan tsohon mutumin da mommy tasa ya kwashe su da nufin ya zubar dasu?Taya akai hosana da jahad suka kasance Ζ΄a'Ζ΄an uncle Ιinmu!?wacece ita Ιayar yarinyar mai kama dasu sak!dama su Ζ΄an uku ne?TabΙijancan,akwai matsala,
Komawa tayi gefen gadonta ta zauna tare da kifa hannunta asaman fuskarta,hosana da jahad suna raye,suna gidan abban mu,wayyo Allah na,ina farin ciki sosai,duk da ina tsoran abunda zai biyo baya,Ashe jinina ne su!shiyasa akace rashin sani yafi dare duhu,mun cutar dasu sosai,mun zalunce su bayin Allah,mutuwa ce kawai batazo ta daukesu ba acikin gidan nan amma sunsha wahala,sun Ζuntata,tabbas Mommy mun shiga uku,idan Abba yaji,daga ni harke ba wanda zai tsira,kwara ni hukuncina mai sauΖi ne tunda na nuna masu soyayya daga baya amma ita mommy itace silar fitar dasu daga gidan nan don azubar dasu,Wayyo Allah na!,
Yatsun hannunta sae faman kerma sukeyi,jiki na rawa ta Ιauki wayarta tare da lalubar numbar junaid ta danna mashi kira,
A lokacin junaid yana tare dasu Uncle abusufyan,dama sai daya fara kiranshi a waya ya tambayi address Ιin inda suke ya bashi,har an kammala yi masu saloon tuntuni,anyi masu Ζunshin jan lalle a hannuwansu,daga can suka wuce shoprite siyayya,bayan sun kammala siyayyar,suka biya gidan Uncle Ιin nasu wuraren 6,saboda su kwaso wasu daga cikin kayansu Jahad da hosana wanda zasuyi kwalliyar walima dasu,
A bayan motar junaid aka sanya trolley Ιin kayan nasu,sannan Sehrish da hosana suka shige motar abusufyan,jahad kuma ta shiga motar junaid,atare motocinsu suka fita daga cikin gidan,
Tunda jahad ta shiga motarshi,ya Ιaure fuskarshi,dama tun wurin siyayyar yake ta shan mur yana murtuke mata fuska,amma hakan bai hana tayi masa magana ba,duk in ta Ιauko abu sai ta gwada mashi ta tambayeshi zaiyi mata kyau,daΖyar yake amsa mata da eh,ko a'a,sai dae kawai tayi murmushi ta girgiza kai,
Kiran Hafsat na shigowa a wayarshi,yace"ki Ιauki wayar,ki amsa wayar sai ki sanyata a handsfree,"
hannu jahad tasa tare da ciro wayar daga aljihun gaban rigarshi,picking call Ιin tayi bayan ta sanyata handsfree sannan tayi Mata sallama,
Muryar hafsat ce ta karaΙe kunnansu"Junaid!kana ina ne"? Gaban jahad ne ya faΙi rass saboda jin muryar hafsat,duk da bata tabbatar da cewar ita bace,amma muryar tayi mata kama da ta sister hafsat,
"Ina akan hanyar komawa gida ne yanzu hakan,"
Hafsat tace"junaid dan Allah so nake in tambayeka,waΙannan yaran Ζ΄a'Ζ΄an uncle abusufyan Ζ³an uku ne"?
"Of course they are triplet,"ya bata amsa a yayin da yake ΖoΖarin juya sitiyarin motar,ya karya kwana,
Hafsat tace"Ya sunan su"!
Juyowa yayi ya Ιan kalli jahad da idanunta ke akan shi,kafin ya mayar da idanunshi kan driving din da yakeyi,a jere ya ambaci sunayensu"Hosana Sehrish Jahad"!hafsat na jin haka,a gigice ta kashe wayar,
"kiran ya katse,"Jahad ta faΙi tana Ζare ma wayar kallo,
"May be network ne,idan na koma gidan zan kirata,"
"In mayar maka da wayar"?
"A'a ki ruΖe a wurinki,idan mun isa gida zan kar6a,"
ta amsa mashi da toh,
Gallery Ιinshi ta shiga tana kallon kyawawan hotunanshi da yayi,tare da videos,yawanci duk na ban dariya ne,wasu yana a kwance,wasu ya zullo harshe waje,wasu hotunan ya kashe idanunshi,
Dariya ta dinga yi a yayin da take kallon videos Ιinshi na tiktok,duk yana sauraron sautin dariyarta,wani lokacin har satar kallon fuskarta yakeyi,ba Ζaramin kyau tayi mashi ba,musamman inta tuntsire da dariya,wani sa'in hada kifa kanta saman laps dinta saboda tsabar dariya,murmushi kawai yayi tare da mayar da hankalinshi akan driving Ιin da yake yi,a haka har suka Ζarasa gida,
Bayan hafsat ta katse kiran,ta Kifa kanta asaman pillow Ιinta,tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka,dama ance dana sani Ζeya ce,
Farkawa Aunty babba tayi da wata irin matsiyaciyar yunwa,sae faman hamma takeyi,tashi tayi daga zaune tare da kai hannu ta Ιauki wayarta tana cewa"Ko hayam ta tura mun da hoton?bari na duba na gani,Allah yasa dai bata manta ba,"
shiga cikin whatsapp Ιinta tayi tare da duba chat Ιinsu da hayaam,rai a6ace taja dogon tsoki tare da cewa"Wai dama bata turamun hoton ba!harfa Ζara nanata mata nayi akan ta tura mun hoton amma bata turo ba," ta Ζarasa maganar tare da yin wurgi da wayar saman gadon,
Saukowa tayi daga saman gadon,fita tayi daga cikin bedroom din ta sauko Ζasa,kai tsaye ta nufi kitchen,
Batare da 6ata lokaci ba,ta shiga harhaΙa kayan da zatayi amfani dasu,bayan ta Ιaura girkin,ta Ιebo snacks a plate ta haΙo da coke mai sanyi ta dawo falo,ta zauna,tana ci tana kallo a plasma hankalinta kwance,
jin motsin mutun a gefenta yasa tayi firgit tare da juyawa don taga wanene,ashe hafsat ce atsaye yanayinta kamar na wadda tayi amai da zawo,fuskar nan tayi gwanin ban tausayi,idanunta sun Ζankance saboda kukan da tasha,
"Hafsat!lafiya naga fuskarki tayi jawur?kinyi kuka ne"?
Girgiza kai hafsat tayi tare da cewa"Babu komai mommy,wani film nake kallo acikin wayata,shine ya sanya ni kuka,"
Tsoki Aunty babba taja"shirmen banza,kawai daga kallon film saiki kama kuka kamar wata sakarya,"
murmushin takaici hafsat tayi tare da samun wuri daga gefen aunty babba ta zauna,batare da tace komai ba,
Aunty babba taci gaba da cewa"gaskiya kowane film ne wannan ya ciri tuta tunda har ya iya sanyaki zubar da hawayenki,yadda kike da shegen taurin kai,
"Mommy ba zaki gane bane,"
"Taya za'ae in gane?tunda bakiyi mun bayanin meya faru ,acikin film Ιin ba,ki Ιan bani labari mana,"
Gyara zama hafsat tayi kafin ta soma bata labarin kamar haka"wata matace fa,mijinta ya kawo mata wasu marayun yara donta rainesu a wurinta,tun ranar da mijin ya kawosu gidan shi kuma yayi tafiya,ae kuwa matar nan,ta shiga gana masu azaba,ta hanasu abinci yunwa kamar zata kashesu,har bugunsu takeyi,sannan kuma ta dinga sanyasu aikin wahala,har saida suka kusa rasa rayuwarsu,mommy kinsan meya faru"?
Dakatawa Aunty babba tayi daga shan lemun hannunta da takeyi tace"a'a saikin faΙa,"
"Hmmm,Mommy Ζarshe fa matar nan,tasa aka kwashe yaran nan,aka 6atar dasu saboda kawai kar asirinta ya tonu a wurin mijinta...'
"Hakan da tayi yayi mun dai dai,"Acewar aunty babba,
Murmushi hafsa tayi kamin tace"Ae ban Ζarasa maki labarin film Ιin ba,bayan tasa an zubar da yaran nan,ita duk a tunaninta sun mutu ma,Ashe can wurin gararin rayuwar da sukeyi a daji Allah ya haΙasu da kanin mijinta har ya taimakesu ya kaisu gidansu mijin,da akayi bincike aka gano cewar yaran Ζ΄a'Ζ΄an kawunsu ne wato Ζanin mahaifinsu,"
Aunty babba tace"tashin hankali!ita ko wannan ya zatayi da kanta?
Dariya hafsat tayi tare da cewa"Nima abunda nake tunani kenan!amma Mommy idan kece ya zakiyi,"
shiru Aunty babba tayi tana tunani kafin daga bisani tace"Ae kawai tunkan asirina ya tonu zan gudu ne,a neme ni arasa,amma nikam hafsat wai ya sunan Film Ιin nan ne?tayi tambayar tare da kallon hafsat Ιin wadda itama kallonta takeyi,mikewa hafsat tayi tsaye tare da cewa"An fara kiran sallar magriba,bari naje nayi salla,"
"Amma baki faΙamun sunan film Ιin ba!"Aunty babba ce ta sake nanata mata tambayar da tayi mata,
*AN YANKA TA TASHI* shine sunan film Ιin mommy,yanzu na kalleshi a tashar youtube,tana kai Ζarshen maganarta,ta juya da sauri ta wuce bedroom Ιinta,
Zugudum Aunty babba tayi tana maimaita sunan film Ιin da hafsat ta faΙa mata,wato An yanka ta tashi,
Aranta tace"gaskiya ya kamata in kalli film Ιin nan,Inaso inga yadda matar nan zata Ζare,ko ya mijinta zaiyi da ita?tabΙijancan,akwai badaΖala,"tayi maganar tare da mikewa ta wuce kitchen domin ta duba girkin da ta Ιaura,
Bayan ta kuma fitowa daga kitchen Ιin,upstairs ta wuce bedroom Ιinta,gefen gadon ta zauna tare da miΖa hannunta ajikin drawer chest ta janyo gidan farko,sabon sim ne ta Ιauko tare da daukar wayarta dake ajiye saman gadon,zura sim card Ιin tayi aciki,sannan ta lalubo lambar wayar Ammi wadda tayi copying kan phone,danna mata kira tayi,nan take kiran ya shiga,kusan sau uku kiran na katsewa batare da anyi picking Ιinsa ba,tana kira a karo na hutu Ammi ta Ιaga kiran π³
Ιan zaro ido Aunty babba tayi kafin ta gyara natsuwarta tare da zabga sallama"Assalamu Alaikum Ammi barka da warhaka,"ta maΖe muryarta yadda ammi bazata iya gane muryar wacece ba,
on the other hand Ammi ta amsa mata da cewa"Wa'alaikumus salam,barkanki dai,zan iya sanin dawa nake magana"a dake take magana,
Aunty babba tace"Nasan bakisan dawa kike magana ba,saboda baki sanni ba,Ni matar abokin Abusufyan ce,wadda ke zaune a Ζasar turkey,"
Shiru ammi tayi tana sauraran me magana,
Aunty babba taci gaba da cewa"akwai wani mummunan abu da abusufyan ya aikata a 6oye baison kowa ya sani,shiyasa na kira don in sanar dake,don banason abunda zai ta6a mutuncin family Ιinku,wannan abun kunya ne,muddin ya fita waje mutane sukaji to fa,zaku rasa duk wata Ζima da martaba da kuke da ita....'
tana cikin magana Ammi ta dakatar da ita"Ya isa haka!banason wata kwanana,ki faΙamun abunda kikeson sanar dani!me Abusufyan ya aikata?wani laifi ne wannan da har kike ikirarin zai ta6a Ζimar family Ιinmu a idon jama'a,"?
Wani irin wahalallen yawu aunty babba ta haΙiye kafin daΖyar ta soma kora mata jawabi kamar haka
"Shekarun baya da dadewa,Abusufyan yayi ma wata fyaΙe,harta samu ciki....."
Wata irin tsawa da Ammi ta daka mata har sae da takusa sakin fitsari a wando,a tsiwace tace"Dakata!ki iya bakinki!kinaso ki shiga tsakanina da Ιana ne!wacece ke,kada kiyi tunanin kin kirani da 6oyayyiyar number,zan iya sa agano munke duk inda kike,"
Muryar Aunty babba na kerma tashiga faΙin"wlh dagaske nake ammi ba Ζarya nake ba,gobe idan kinzo abuja wurin walima,zaki ga yaran,ae suna nan gidan Abba,Sun jima suna 6oye maki gaskiya,saboda tsoron hukuncin da zaki yanke ma Abusufyan,yanzu haka maganar da nake maki,sun gama shirya yi maki Ζaryar cewar yaran ba shaggu bane ta hanyar aure aka haife su bayan ba haka bane,suna nan yaran Ζ΄an uku ne mata,sun girma sosai,' tana kai Ζarshen maganar Ammi tace"Kin gama"?
Shiru Aunty babba tayi tana faman mazurai aranta tace"Wannan tsohuwa badae taurin kai ba,bansan ya zanyi na fahimtar da ita ba,ta cika jaraba,"
tana cikin wannan zancen zucin Ammi ta katse kiran,
Wurgi Aunty babba tayi da wayarta,tare da mikewa tana cewa"Ae shikenan,nasan cewa gobe tana ganin yaran zata tuna da kalamai na,daga nan saita Ιauki hukuncin daya dace,"
❤π€❤
*Boss Bature*
Zaune yake asaman Sofa mai mazaunin mutun uku,gaba Ιaya ya tattara hankalinshi akan Laptop Ιinshi da yake daddawana anatse,jikin shi na sanye da linen tank top,blue colour tabi shape din jikinsa,sick pack din nan nasa ya bayyana ajikin rigar,trouser Ιin jikinsa kuma white colour ne,wani irin daddaΙan Ζamshi ne ke fitowa daga kowani sashe na jikinsa,
Shigowa Azmee tayi part Ιin nasa da sallama a bakinta,yayin da hannunta ke ruke da tray,amsa mata sallamar yayi batare daya Ιago ya kalleta ba,Ζarasawa azmee tayi tare da ajiye mashi tray Ιin asaman empty table din dake a gefenshi,hannu takai tare da ciro plate ta daukko serving spoon tana Ζokarin buΙe warmer,muryarshi ta katse mata hanzarinta da cewa"Ιazu da safe meyasa kika kawomin breakfast?kuma kika gyaramun bedroom Ιina,dama kece ke gyara mun part Ιina ne"?
gabanta ne taji ya faΙi rass,muryarta na kerma tace"A'a bani bace,Sehrish ce,"
"Meya hanata yi mun aiki,"?yana magana yana danna laptop dinsa har time Ιin bai Ιago da idonshi ba ya kalle ta,
Azmee tace"Am...um...dama..."bata Ζarasa maganar ba,ya dakatar da ita ta hanyar Ιaga mata hannunshi,cikin sauri ta shiga taitayinta,
Cike da bada Umarni yace"Call her right now,"
Jiki na rawa azmee ta juya tare da fucewa daga part dinsa,downstairs ta saukko,babu kowa a falon duk suna a bedroom Ιinsu,wasu ma sunyi bacci,
Kai tsaye Ιakinsu Sehrish taje,tsayawa tayi abakin Ζopar Ιakin tana kwankwasawa,sai faman knocking takeyi amma ba'a buΙe mata kopar ba,da alama sun jima da yin bacci,
Har sae da ta fidda rai da za'a buΙe mata kopar,tana kokarin juyawa tabar wurin,taji alamun za'a buΙe kopar,Jahad ce ta buΙe Ιakin tana tambayar wanene,
Ganin azmee yasa tayi saurin gaishe da ita cikin girmamawa,
Azmee da nan take ta gane ba sehrish bace tace"kiyi hakuri na tashe ki kina bacci,Sehrish nake nema,dan Allah ki sanar da ita cewa SGR yana nemanta a part Ιinsa,"
Jahad tace"tayi bacci,bari na tashe ta,"tayi maganar tare da juyawa cikin sauri ta shiga cikin Ιakin,
Wucewa azmee tayi ta koma kitchen,cike da zullumin mai zai biyo ba idan Sehrish ta sanar ma Sgr cewa Uncle abusufyan ne ya hanata yin aiki a part Ιinsa,tabbas za'a kwashi Ζ΄an kwallo,
"Sehrish!ki tashi babban yaya yana son ganinki a part Ιinsa,dan Allah ki tashi kije,"jahad ce keta kokarin tashinta daga bacci,sehrish kuwa sai faman mutsu mutsu takeyi,daΖyar ta iya cewa"Wanene ke nema ne'?
Jahad tace"babban yaya,"
Jin sunanshi yasa Sehrish buΙe idanunta ta wurgasu kan jahad dake tsaye,yatsina fuska tayi tare da maimaita sunan nashi"babban yaya?shike nema na,waya faΙa maki"?
"Aunty azmee,yanzun nan bata jima da tafiya ba,naga kamar ma bata acikin natsuwarta,"
Jin hakan yasa gaban sehrish faΙuwa rass,yunkurawa tayi tare da mikewa zaune,ta saukko da Ζafafunta Ζasa,kafin ta miΖe tsaye,saboda tsabar saurin ta fita ko Mayafi bata Ιauka ba,gashi kanta ko kallabi babu,sumar kanta ce da tasha gyara,an mayar mata da gashin mai gazar gazar ya sauko har kafaΙarta,a hankali gashin kan nata ke toho yana fitowa,har ta launin gashin anyi mata dying dinsa ya koma 2 colour,Kayan bacci ne ajikinta riga da wando sharara suke,farare masu laushin gaske,irin waΙanda kana sanyasu ajikinka,Ko baka jin bacci nan take zai zo maka,
Tunkan ta Ζarasa shiga falon nashi take jin Ιar Ιar acikin zuciyarta,tun jiya rabon da ta sanyashi acikin idanunta,daΖyar ta iya yi mashi sallama tare da kutsa kai cikin falon nashi,bai amsa sallamarta ba,har ta Ζarasa inda yake,atsaye muryarta na rawa tace"Gani,"bai dago ba kuma bai tanka mata ba,sae ma cigaba da danna system Ιinshi da yake yi,lokaci bayan lokaci yakan kai hannunshi ya dauki Coffee ya kur6a,zuba mashi ido tayi tana kallon kyakkyawar fuskarshi,ba Ζaramin kewarshi tayi ba,sam batayi tunanin ma zai nemeta ba,
sai da ta Ζara cewa"babban yaya gani,Aunty azmee tace kana kira na,"sannan ya soma magana anatse"yau da safe,meya hanaki zuwa part Ιina"?
Shiru tayi gabanta na faΙuwa,batasan amsar da zata bashi ba,saboda tsoran abunda zai biyo baya,
"Kinsan bana maimaita magana,amsarki nake jira,"
Runtse idanunta tayi aranta tana fadin"nashiga uku,!Allah ka kawomin Ιauki,bansan me zan faΙa masa ba,"shirun da tayi mashi ne ya fusata shi,aikuwa a zafafe ya daka mata tsawa,har sai da ta zura da gudu saboda yarda ta tsorata,kama hanyar fita tayi saboda ruΙewar da tayi,hakan yasa ya miΖe tsaye tare da bin bayanta,ruΖo hannunta yayi tare da fusgota ta dawo saitin shi,Waro ido waje tayi tare da ja da baya da baya,har suka Ζure ma bangon,runtse idonta tayi muryarta na kerma tashiga faΙin"Am so sorry babban yaya,I can explain,zan faΙa maka,"
A hankali ya ware blue eyes Ιinshi akan fuskarta,sumar kanta yabi da kallo,yayi mamakin ganin yadda gashin yayi tsayi cikin Ζankanin lokaci har ya kamo kafaΙarta,gyaran gashin da akayi mata ya Ζara fiddo da kyawun fuskarta,mayar da idanunshi yayi akan La66anta dake ta faman kerma duk tabi ta gigice,lokaci guda ya tsinci kanshi cikin wani irin yanayi mara misaltuwa,moving ya Ζarayi gaba Ιaya yayi mata rumfa da faffaΙan Ζirjinshi,lokacin da taji tsinin hancinshi na gogar nata,nan take gabanta ya kuma bugawa daramm,jikinta ya shiga yin kerma ta ko'ina,gaba Ιaya duk tabi ta susuce har lokacin ta gaza buΙe idanunta saboda tsabar tsoro,jin saukar hannunshi asaman Ζirjinta yasa ta yin saurin ware idanunta arazane,kai tsaye suka sauka cikin nashi,face to face,Eyes to eyes,nose to nose,mouth to mouth!!,
A firgice ta janye idanunta daga kan fuskarshi ta mayar dasu akan Ζirjinta,Ashe gaban rigarta ne ta bari a buΙe ta manta bata sanya links Ιin rigar ba,Shine ya sanya hannunshi a wurin yana manne mata su,jurewa kawai takeyi amma ba Ζaramin yanayi Sgr ya jefa mata ba,musamman yadda hannunshi ke nutsewa a cikin boobs Ιinta,ba ita kaΙae ba,hatta shi kanshi daya kai hannunshi wurin saida yayi regretting,saboda wani abu daya dinga jin yana fisgarshi yadda kasan magnet,mayen karfe ba,
daΖyar ya iya zame hannunshi daga saman Ζirjin nata,bayan ya kammala sanya mata links Ιin,Sannan cikin sanyin murya yace"tell me the reason why baki zo yi mun aiki da safe ba!bakisan bana son sharing a aiki na ba!?
Magana yakeyi amma idanunshi sae Ζokarin lumshewa sukeyi tamkar mai jin bacci,wanda kuma ba kowa ne yajawo hakan ba face Sehrish,
Cikin en ena tace"Kayi haΖuri ba laifina bane,Daddy ne ya hanani zuwa"
Cike da mamaki yace"Kina nufin Uncle ne ya hanaki zuwa,"
Jinjina mashi kai tayi alamar eh,yayin da take ta faman haΙiyar yawu,
. "just without any reason ya hanaki aiki a ΖarΖashi na"?
daga mashi kai tayi alamar eh,
Cije pink lips Ιinsa yayi tare da tsoma hannunshi acikin sumar kanshi yana cakuΙata,ranshi a matuΖar 6ace yace"hakan bazai ta6a yiyuwa ba,dole kiyi aiki a ΖarΖashina!ban damu da matsayinshi a wurinki ba,dole ne ayimun biyayya!!!!!!!!*
*Tashin hankalin da ba'a sama shi date!*
Gobe walima,suwa suka shirya zuwaππππ
*SANARWA SANARWA*ππππ
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
*πBoss Batureπ*
Join this link to follow my tiktok acctπ
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
ΩΨ΅Ψ© ΨΨ¨ Ψ±ΩΩ Ψ§ΩΨ³ΩΨ© Ψ¨ΩΩ Ψ³ΨΨ±ΩΨ΄ ΩΨ§ΩΨ¬Ψ±Ψ§Ψ Ψ§ΩΨΉΨ§Ω Ψ±ΩΨ§ΩΨͺππ❤π€❤ππ*
*Father of soldiers*
*π₯TAKUN ΖARSHEπ₯*
Ranshi a matuΖar 6ace yace"hakan bazai ta6a yiyuwa ba,dole kiyi aiki a ΖarΖashina!ban damu da matsayinshi a wurinki ba,dole ne ayimun biyayya!!!!!!!
Waro ido waje Sehrish tayi tana kallonshi,hankali atashe jikinta sai faman kerma yakeyi,ji take tamkar ta zura da gudu,saboda yadda taga Sgr ya fusata tsoranta kar ya ciro belt Ιin wandonsa ya rufe ta da bugu,tana cikin wannan zancen zucin muryar shi ta katseta da cewa"listen to me!"
Natsuwa tayi tana sauraronshi kamar yadda ya Umarta,
"Banaso na Ζara ganin Azmee tazo part Ιina da sunan za tayi mun aiki,ke nakeso ki kawo mun breakfast sannan ki gyaramun part Ιina,hope u understand?"
Muryarta har kerma takeyi wurin cewa"E zan..na..fahimta,'
Jinjina kanshi yayi tare da cewa"Okey,yanzu kizo kiyi serving Ιina,then idan kin kammala ki gyara mun bedroom,"babu wasa a fuskarshi yake yin maganar,wato yadda ya tsare Sehrish yadda kasan Ζ΄ar cikinshi,ta yi tsuru tsuru,Ni dai bansan ya Sehrish zata Ζare ba,ga umarnin mahaifinta gana kuma yayanta mai matukar tsauri,shin wa zatayi ma biyayya?a sanin mu dai Umarnin Mahaifi shine sama da komai,bayan na mahaifiya,bari mu gyara zama muga yadda wannan Al'amarin zai kaya,
Ja da baya yayi tare da juyawa ya koma saman sofa ya zauna sannan yace"Am waiting for u,"
Jiki asanyaye Sehrish ta Ζaraso inda yake,yatsun hannunta sae kerma sukeyi,a haka ta shiga serving Ιinshi,a plate ta zuba mashi chicken pepper soup ta tura mashi agabanshi,yana ci tana satar kallon fuskarshi,ba Ζaramin mamaki Sgr yake bata ba,ta jinjina ma Ζarfin halinsa na yau,batasan me zai faru gobe ba amma tabbas akwai badaΖala,
Bayan ya kammala cin dinner Ιin nashi,sai da ta gyara mashi bedroom Ιinshi,sannan ta samu ta fito daga part Ιinsa da kayan abincin,a hankali take taka stairs Ιin,ranta a jagule ba don komai ba sai don karya umarnin mahaifinta da tayi,wanda kuma ba komai ne yaja hakan ba face shegen tsoron Sgr da takeyi,da ba don haka ba,da ba abunda zai hana tayi mashi gardama,don a yadda yake da bad temper Ιin nan ta kuskura tace zatayi mashi jayayya,bugu zai kai mata,zuΖunnawa tayi asaman steps Ιin benen tana faman cizon la66anta,a hankali ta furta"sae yaushe ne zan fita daga wannan KURKUKUN ΖADDARAR da nake ciki?yaushe ne abubuwa zasu fara tafiya dai dai arayuwata?daga wannan sai wannan"? Idonta cike tab da hawaye tayi maganar,kafin ta yunΖura tare da miΖewa ta nufi bedroom Ιinsu bayan ta kai kayan kitchen,a hankali ta tura Ζopar tare da shigewa ciki,bayan ta datse Ζopar ta juya,mamaki tayi ganin jahad ruΖe da wayarta a hannunta ta Ζura ma screen Ιin wayar ido,duk a tunaninta zata zo ta same ta tayi bacci,ashe bata koma bacci ba tun bayan da Azmee ta tashe ta,
Ζarasawa tayi tare da hayewa saman gadon a gefenta ta zauna,cike da mamaki take kallon jahad,ganin ko motsi ba tayi,bama tasan ta shigo Ιakin ba,ko menene yaja hankalinta haka?
"Jahad!"Sehrish ce ta ambaci sunanta,a firgice ta juyo tana kallonta,ganin sehrish yasa ta sakin murmushi tare da cewa"Har kin dawo,ae nayi tunanin acan zaki kwana,"
dariya sehrish tayi tare da dungurin goshinta tace"Abun hada tsokana,Nima nayi tunanin zanzo na same ki,kina bacci ashe idonki biyu,me kike yi da wayar ne"?don naga gaba Ιaya yaja hankalinki,"
Ζayataccen murmushi jahad ta saki tare da cewa"Hmmmm ba zaki gane bane,wani zazzafan hausa novel ne nake karantawa acikin wayarki,dama jira nakeyi kizo in tambayeki a ina zan samu cigaban littafin"?
Cike da mamaki Sehrish tace"Novel kuma?ae ni bana karatun littafin hausa,banma san ya akai kika samu littafin a wayata ba,don gaskiya bana ajiye su,"
Wani kallon rainin wayau jahad tayi mata tare da cewa"Kina nufin duk haΙuwar littafin nan baki ta6a karanta shi ba!hakanan kike ajiyar shi acikin wayarki?
Yatsina fuska Sehrish tayi tare da cewa"nifa bansan dashi ba,may be cikin friends Ιina na makaranta ne wata wurin tura ma wasu ta turamun shi batare da sani na ba,"
jinjina kai jahad tayi tace"gaskiya an barki a baya,tunda uwata ta haife ni ban ta6a karanta littafin me shegen daΙi irin wannan ba,tunda na fara karantashi bakina ke awashe,kamar anyi mun albishir da gidan aljanna,"ta karasa tana daria,
Ta6e baki sehrish tayi tare da cewa"Wai ya sunan Littafin ne?naji sai faman zuzuta shi kike yi,inaso inji sunanshi ne saboda tun daga kan sunan littafi ake tantance in mai daΙi ne ko mara daΙi,"
Ζayataccen Murmushi jahad ta saki tare da Furta sunan Littafin*A SANADIN MAKWABTAKA*!
Maimaita sunan Sehrish tayi"A sanadin makwabtaka"
Jahad tace"kwarai kuwa,sunanshi kenan,"
Gyara zama sehrish tayi tare da cewa"kawo wayar mu gani,zan jaraba karanta one page naji ya daΙinsa shin yakai Abban sojoji da nake jin friends dina nata faman cewa ya hadu"?
Jahad tace"Ae ya zarce nan,"tayi maganar tare da miΖa mata wayar tace"one page kika ce zaki karanta,zan jira ki kammala don inci gaba daga inda na tsaya,"
Hannu sehrish tasa tare da kar6ar wayar,ta buΙe page Ιin littafin asanadin makwabtaka,a natse ta fara karantashi,"
Zuba mata ido jahad tayi tana jira taga reaction Ιinta,
a hankali murmushi ya fara bayyana akan fuskar Sehrish,daga Ζarshe ma ta fashe da dariya,tunda tafara karanta littafin sae faman zabga murmushi takeyi,ita da tace zata karanta one page sai gashi ta zarce page biyar,ganin abun ya wuce gona da iri yasa jahad sanya hannu ta kar6e wayar tana cewa"Ya isa haka,je ki kwanta,gobe akwai shirye shiryen waleema,"
Ιaure fuska sehrish tayi tare da cewa"wlh baki isa ba,sai da kika fara ΙanΙana mun zuma abakina na lasa daga baya kuma kizo kice zaki hana ni"?
itama jahad Ιin ta tamke fuskarta tace"ae ni na fara karantawa tun farko,ke da bakisan ma da zaman littafin acikin wayarki ba sai da na faΙa maki"
wurga mata harara sehrish tayi tare da miΖa mata hannu tace"Bani wayata,"
Jahad tace"wlh bazan bada ba,sai na kammala karanta littafin nan,"
Abu kamar wasa suka shiga cece kuce,ran sehrish yayi mugun 6aci,aikuwa ta cakumi wuyan rigar jahad,nan fa suka shiga kokowa asaman gadon kamar Ζ΄an wrestling,wani bugu da Sehrish takai ma jahad a kumatunta ne yasa ran jahad ya 6aci,a fusace tayi wurgi da wayar Sehrish,kai tsaye ta faΙi saman tiles,ta daku sosai ji kake taratssss!screen Ιin wayar ya tarwatse,
Tashin hankali,
la66an sehrish har kerma sukeyi wurin cewa"kika fasa mun wayata"?
Girgiza kai jahad tayi hankalinta a matuΖar tashe tace"dan Allah sehrish kiyi haΖuri,wlh bada sanina nayi hakan ba,raina ne ya 6aci saboda naji zafin bugun da kikai man"
Hawaye ne suka cika idon Sehrish cikin murya kamar ta mai son yin kuka tace"Ni babban baΖin ciki na,ba wayar data fashe bane,nasan daddy zai iya canzamin wata,Amma littafin fa?a ina zan same shi,daga ji zai dauke ma mutum damuwa yasa shi nishadi"?
Jahad tace"Am so sorry sehrish,na maki alΖawarin cewa,zan nemo maki shi,nasan baza a rasa me shi ba,akwai wata class mate Ιina sunanta hafsat bature,ta kware wurin karanta littattafan hausa,insha Allah idan muka koma school zan tambayar maki ita,nasan bazata rasa littafin a wayarta ba,idan ma babu littafin to ina da tabbacin cewar tasan marubuciyar shi,sae ta bamu numbar wayarta,"
Jin haka yasa sehrish sakin murmushin jin daΙi,matsawa tayi tare da rungume jahad tace"yawwa jahad,kinyi tunani mai kyau,nagode sosai,yakamata mu kwanta yanzu,dare yayi fa sosai,"
tayi maganar ayayin da ta gyara kwanciyarta,itama jahad ta kwanta,atare su kayi addu'ar bacci cikin ΖanΖanin lokaci baccin ya Ιaukesu,
"Nagode sosai da shawarwarin daka bani,kuma insha Allah ina da tabbacin cewar in muka biyo mashi ta wannan hanyar zamuci nasara akanshi,abun zai zama tamkar wasan kwaiwayo," Acewar Abbansu junaid dake tsaye a bakin Ζopar fita daga Ιakin Uncle abusufyan,Uncle Ιin na a bayanshi fuskar kowannansu Ιauke da murmushi,da alama sun kammala tattaunawar da sukeyi,
"Nike da godiya yaya Hossain,idan har wannan abun ya tabbata,zanfi kowa farin ciki,"
Juyowa Abba yayi cike da zolaya yace"kada ka manta,gobe ne fa sunan Ζ΄an ukun da aka haifa maka,me zaka yanka masu"?
..sunnar dakai Ζasa Abusufyan yayi yana dariya,yace"Sa za'a yanka masu guda uku,raguna uku,Ιawisu guda uku,Ζ΄an shila guda Ιari uku,kaji guda Ιari uku suma,"
Dariya Abba yayi yana bubbuga kafadarshi yace"Abun ya Ζayatar dani wato komai guda uku kenan za'a yanka masu,idan ma ba uku ba to Ιari uku,dole dae ukun ta fito kamar yadda suke Ζ΄an uku,a Ζagare nake da goben nan tayi,bari na hanzarta zuwa na kwanta,"
"Allah ya nuna mana ita lafiya,"acewar abusufyan daga haka Abba ya bude kopar tare da fucewa yana faΙin"mu kwana lfy,"
Bayan fitarshi,Abusufyan ya koma tare da hayewa saman katafaren gadonshi,yayin da idanunshi ke fuskantar ceiling,bakomai ne ya faΙo mashi aranshi ba face ABU,a kullum cikin tunanin wani hali take ciki yake,haΖiΖa ya damu da ita sosai,kusan kullum ne sai yayi mafarkinta,dama da yawa idan ka sanya abu aranka,zaiyi wuya bakayi mafarki akansa ba,babban abunda yafi damunshi duk in zai ganta a mafarkin cikin wani irin mawuyacin hali,
"Bakomai ne yasa na damu sosai akanta ba,face sanin cewa ita marainiya ce,bata da kowa a duniyar nan wanda zai damu da ita idan bani ba,da kuma Ζ΄a'Ζ΄an data haifa ba,Abu bata da kowa bata da wanda zai neme ta idan wani mummunan abu ya faru da ita,da ace Ζaddara bata haΙani da Abu ba harna aureta ba,a yau akace ta 6ace,nayi imanin cewa babu wanda zai damu akan hakan,mahaifinta ne kawai shi kuma Allah yayi mashi rasuwa,Allah yajiΖanka baba buzu,haka ya damΖa mun amanarta,duk da yasan halina bana jin magana ga Ζuruciya dake fusgata,yayi mun halaccin da bazan ta6a mantawa ba,kuma Insha Allah zan ruΖe mashi amanar daya bani,bazan ta6a mantawa dashi ba,saboda shine silar komai,gashi har nasamu Ζaruwar Ζ΄an uku tare da Ζ΄arsa,naso ace yana raye nasan zaifi kowa farin cikin ganin jikokinsa,'
Hawaye ne suka soma gangarowa daga cikin idanuwansa masu Ιumin gaske,murmushin takaici ya saki tare da gyara kwanciyarshi,ya runtse idanunshi daΖyar bacci ya Ιauke shi,
A 6angaren Abba kuwa,bayan sun rabu da Uncle abusufyan,yana shiga bedroom Ιinshi,ya tsaya turus ganin junaid kwance yana sharar bacci,ga mommynshi agefe tana bacci itama,girgiza kai yayi tare da cewa"bansan meyasa junaid keyi mun haka ba,ya raina ni wlh,"juyawa kawai yayi tare da fucewa daga bedroom Ιin ya koma upstairs bedroom Ιin junaid ya nufa ya kwanta,ya Ζyale shi ne saboda yana cikin farin cikin gobe walima,baison abunda zai 6ata ranshi,
Wuraren Ζarfe 2 na dare junaid ya farka sakamakon zungurar shi dayaji anyi da sanda,a firgice ya tashi zaune yana faman zazzare manyan idanunshi masu Ιauke da bacci,Ζasa Ζasa yaji ana ambatar sunanshi Junaid!junaid!aikuwa a tsorace ya sanya hannunshi tare da toshe kunnanshi ya fasa uwar Ζara,kai tsaye sautin Ζarar daya saki ta daki dodon kunnan Alexandra,a firgice ta farka,ganin junaid da tayi a zaune jikinsa sai kerma yake yi hakan yasa ta miΖe tare da janyoshi jikinta tana faΙin"junaid!romeo Ιina what's wrong with u?baka lafiya ne,"duk tabi ta tsorata da halin da yake ciki,
..Muryarshi na kerma yace"Mommy,wani abu zai faru dani,dan Allah ki taimaka mun,banso in mutu yanzu,"
Jin wannan maganar ta junaid ba Ζaramin tayar mata da hankali tayi ba,kankame shi ta Ζarayi muryarta na rawa tace"Junaid,kadaina faΙin haka banason ji,babu abunda zai faru dakai indai kana tare dani,nasan cewa mafarki kayi,pls calm down ur mind,mu koma mu kwanta,
Ιagowa yayi daga jikinta,cikin shessheΖar kuka yace"Mommy dan Allah,ki tashi muyi sallah,sai kiyimun addu'a,"
a ruΙe tace"Salla kuma junaid,am not a muslim bana sallah,zan daiyi maka addu'a,"
"A'a mommy nidai ki tashi muyi sallah,kiyimun addu'a,"Ashagwa6e yayi maganar,
"Junaid ka fahimce ni,bakasan cewa niba musulma bace!ko daddynku bai ta6a faΙa maka bane,Ni bana sallah,I don't even know how to do it,"
Jin haka yasa junaid sake fashewa da wani sabon kukan mai sautin gaske yana cewa"Mommy ki tashi muyi sallah,ki tashi mommy!wlh idan baki tashi munyi sallah kinmun addu'a ba mutuwa zanyi,"
Tashin hankali,gaba daya junaid yabi ya rikice mata ya hanata sakat,duk yadda taso ta fahimtar dashi akan cewa ita ba musulma bace,bata sallah amma abun ya faskara,junaid ya kurmance mata,
Babu arziΖi ta amince zatayi sallar,tasata gaba yayi ta shiga toilet ta dauro alwala,ko alwalar bata wani iyaba,ruwa kawai ta watsa a fuskarta,ta wanko hannayenta da kafafuwanta tafito,shi ma ya shiga cikin toilet Ιin,wucewa tayi wurin wurin closet Ιinsu,ta buΙe kayan Abbansu ne a jere sai kayan sawar ta,wanda tazo dasu,gaba daya babu hijabin da zata sanya,dakyar ta samu wani mayafin doguwar rigarta mai Ιan tsayi,ta Ιauko shi tare da sanyashi ajikinta,sae yayi mata tamkar hijabi,
tsayawa tayi tana jiran junaid ya fito suyi sallar,lamarin nashi ba Ζaramin Ιaure mata kai yayi ba,Ζiri Ζiri junaid yasata za tayi sallah,ya rufe idonshi ya nuna tamkar baisan cewa ita ba musulma bace,aranta tace"Anya junaid bai samu ta6in hankali ba?in ba haka ma meyasa zai yi forcing Ιina akan inyi salla bayan yasan cewa ni ba musulma bace,Omg!ni bansan ma ya akeyin sallar ba,ko time Ιin baya dana ta6a musulunta ba don Allah nayi ba,ko sallah banyi a lokacin,"
tana cikin zancen zucin nata sai ga junaid ya fito daga cikin toilet yana faman yarfa hannunshi,ruwan alwalar da yayi yana ΙiΙΙigowa Ζasa,
Carpet Ιin salla ya dauko masu na abbansu sannan ya dawo ya shimfiΙa masu shi,
Juyawa yayi tare da kallon Mommyn tasu wanda tayi sototo tana binshi da kallo,
"Ni zan shiga gaba saiki tsaya abaya,"
Dawowa bayanshi tayi ta tsaya,shi kuma ya tsaya agaba,tare da daidaita natsuwarshi,ya kabbara sallar,anatse suka shiga yin sallar atare,tunda suka kai raka'a dayan farko,bacci ya kwashe Alexandra,junaid bai sani ba yaci gaba da yin sallarshi,sai da yayi kusan raka'a takwas sannan ya sallame,
cikin bacci taji an ambaci sunanta da Ζarfi"Mommy"!!a firgice ta farka tare da buΙe idanunta tana kallonshi,muryarta adisashe irin ta mai bacci tace"junaid har mun kammala sallar,"zum6ura mata baki yayi rai a6ace yace"nadai kammala sallar mommy,kin barni ni kaΙae,kina ta bacci,"
cikin lallashi tace"kayi haΖuri romeo Ιina,saida na faΙa maka cewa banyin sallah,nifa ban iya ba,nadai samu nayi Ιaya,dakyar itama na samu nayi ta,don bacci nake ji,"
"Shikenan kiyimun addu'a yanxu,sai muje mu kwanta"
Yadda yayi maganar ba Ζaramin tausayi ya bata ba,nan take taji kamar bata kyauta mashi ba,jiki asanyaye ta sanya hannunta tare da ruΖo hannunshi,ta shiga karanta mashi addu'oin,cikin harshen Faransanci,bai damu da yaren da takeyi mashi addu'ar ba,saboda yasan cewa Allah yana ji da kowani irin yare aka roΖesa,"
Ta jima tanayi mashi addu'a tana tottofa masa asaman sumar kanshi,kafin daga bisani suka koma saman gadon suka kwanta,ba Ζaramin kwanciyar hankali junaid ya samu ba,tunda ta tofa mashi addu'ar nan take yaji wani sanyi aranshi,tamkar an bashi Ζwarin guiwa,kuma tunda ya kwanta bacci ya Ιaukeshi bai Ζara jin an zungure shi ba,
DARE YAYI GARI YA WAYE,
Tun bayan Kammala Sallar asuba,Azmee da Saude,Suka fara Ιaura girke girken da zasuyi anan cikin gida,Uban aiki ne a gabansu,saboda Abinci ne kala kala zasuyi,na kasashe daban daban,saukin su ma Naman da za'a yanka basu zasuyi aikinshi ba,An riga da an bada aikin naman already,sai dai kawai in an kammala akawo masu shi Hada snacks sukayi order wanda za'a ci,akwai kuma Naman da Azmee zatayi masu farfesu dashi,da kuma tsiren nama,don ta kware a wannan 6angaren,Sunyi nisa acikin aikin sai ga Hajiya azeema ta shigo,bayan sun gaisa da junansu,itama tace tazo ayi aikin da ita,hakan ba Ζaramin daΙi yayi masu ba,nan suka haΙu su uku,suka tasar ma girkin nan,Cikin ΖanΖanin Lokaci,Wani irin daddaΙan Ζamshi ya gauraye ko'ina na kitchen Ιin,
Hatta main palour Ιin kamshi ya karaΙe cikinsa,gwaggon katsina dake kwance,saman gado,tun bayan sallar asuba ya Ιauketa,tana cikin bacci ta dinga jin Ζamshin abinci nashiga Hancinta,ba arziΖi ta farka tana faΙin"wannan wani irin Ζamshi ne mai tashin mutun daga bacci"?tana maganar tana shinshinar kamshin,saukowa tayi daga saman gadon,jikinta sanye da kayan baccin nan nata na gado,fitowa tayi daga cikin bedroom Ιin nata tana tunkarar inda kamshin ke fitowa,
Kamar daga sama suka ji muryar gwaggo tana cewa"Ikon Allah,Ζamshi ya tashe ni daga bacci,ya kawo ni cikin kitchen,don inci daΙi,"
Murmushi suka saki gaba Ιayansu,kafin suka shiga gaishe da ita,
Ζarasawa tayi cikin kitchen Ιin suna haΙa ido da saude ta watsa mata harara tare da cewa"ya akai kuka bar wannan tana girki?bafa ta iya girki ba,Rannan ta zuba mana Gishirin lalle amatsayin gishiri cikin farfesun nama,gaba Ιaya girkin nan bai ciyu ba,Ζarshe saboda tsoran kar asirinta ya tonu inyi mata faΙa,ta dauki farfesun ba tare da sanin kowa ba taje ta zuba ma karnukan layinmu,kunsan kare da nama nan fa suka lashe farfesun nan tasss suka cinyi shi,aikuwa cikinsu ya kumbura sumtum,sukayi mussai,gaba Ιaya suka mace aka zubdo su,mai karnukan nan yace bazai yarda ba,sai yayi shari'a da Saude,ranar saude har gudawa saida tayi don jin za'a kaita Ζara kotu,yarinya tabi ta burkice mana,daΖyar Harrisu ya biya diyarsu,daba don haka ba,da tuni saude an jima da yanke mata hukuncin kisa....'
Tunkan gwaggo takai karshen Labarin da take basu gaba Ιaya suka fashe da dariya,banda saude wadda ta tur6une fuska,rai a6ace tace"Kai gwaggo,"
gwaggo tace"Ζarya nayi?ko ba haka akayi ba,ki faΙi tsakaninki da Allah in ba ayi hakan ba,ranar fa har gudawa kikayi,kika dinga kuka kina cewa gwaggo ki maishe ni rugarmu,saboda kawai na kashe karnuka shine za'a kai Ζarata kotu,wlh ko shanun baffa na kashe ba za'ayi mani wannan hukuncin ba,sai ku Ζ΄an gayu da kuka Ιauki ran kare da mahimmanci karen da ko hisabi baza'ayi dashi ba,"
Sake fashewa da dariya sukayi,yadda gwaggo take kwaikwayon muryar Saude,ba Ζaramin dariya ta basu ba,saboda hausar irin ta fulanin da basu kware bace,"
fuskar saude tamkar zatayi kuka,batasan meyasa gwaggo keyi mata haka ba,duk in suka shiga cikin mutane saita kunyata ta,wannan labarin da take bayarwa ya jima da faruwa,tun lokacin da Dr harris ya Ιaukota daga rugarsu ya kawota gidansu,lokacin batasan komai ba,ita arayuwarta ba abunda ta bama mahimmanci inba Kiwon shanu ba shi kadae tafi sani,gwaggo kuma bata koyar da ita komai ba,kwana uku da zuwanta gidan ne,ta shiga kitchen ta Ιaura masu girki,tana cikin girkin ta fara neman gishiri zata zuba acikin,gafa gishirin acikin farar roba an zubashi,amma saboda ta saba ganin gishiri kulle acikin leda yasa tayi zaton koba gishiri bane,hakan yasa ta fito ta wuce Ιakin gwaggo don ta sanar da ita cewa babu gishiri a gidan,tana shiga Ιakin gwaggon katsina,ta same ta tana bacci,harta juya zata fita shine taga wasu kullun kaya da aka kawoma gwaggo acikin leda,nan fa ta shiga laluban kayan,ta zaΖulo ledar gishirin lalle ta fuce dashi,duk a tunaninta gishiri ne,dayake kanta a toshe yake,kwata kwata bata lura da lallen dake acikin ledar ba,ita dae kawai gishirin lallan ta Ιauko,taje ta zuba masu acikin girkin,ba don Allah yasa gwaggo ta tashi tana neman gishirin lallanta ba,har saude taji,daba Ζaramin illa zata yi masu ba,karshe dai abun kan karnukan layinsu ya Ζare,tun daga wannan lokacin ne harris ya sanyata a makaranta,da kuma makarantar koyon girki,har ta samu ta kammala secondary,daga nan ne akasamu kanta ya waye,
"Gwaggo me kikeso a zuba maki ne?nasan yunwa ce ta koro ku,"azmee ce tayi maganar,
Gwaggo tace"komi ma da kuka girka,a zuba mun in ΙanΙana inji yaya ΙanΙanon girkin naku yake,don tunda kuka sanya saude acikin girkin nan naku nasan cewa dole a samu matsalar rashin gishiri kodae ta zuqa shi,ko kuma yayi kaΙan,"
murguΙa mata baki saude tayi tare da juyawa ta shige cikin store,tana faΙin"nashiga uku da wannan matar,a haka Haris yakeso in zama surukarta,bansan ya zan Ζare da ita ba,lafiya lou nake yin girkina acan gida,har santi takeyi amma yanzu tazo sai sharri takeyi mun agaban mutane,Zamu koma gida ne,nasan me zanyi mata,ae mun saba dama,"
Saude bata fito daga cikin store Ιin ba,sai da taji fitar gwaggo daga kitchen din,bayan sun zuzzuba mata abincin da suka girka,komai sai da tasa suka zuba mata,a Ζaton tray ta fuce dashi tana cewa"idan na cinye wannan zan dawo a Ζara mun,"
dawowa tayi cikinsu suka cigaba da aiki,azeema tace"sai kin dinga haΖuri da ita,bayin kanta bane,ku tayata da addu'a,Allah ya yaye mata wannan haukan da aka Ιaura mata,"
Saude tace"insha Allah,zamu cigaba da tayata da addu'a,ae yaya harris ya sanar dani komai,na tausaya mata sosai,Allah dai ya tonu asirin waΙanda ke shirya masu wannan maΖarΖashiyar,Allah ya kawo Ζarshensu,"
Azmee tace"ae bazasu kai labari ba,a sannu asannu zasu gane kurensu,"
Suna aiki suna tattaunawa game da irin rayuwar da su sehrish sukayi a baya,
Wuraren Ζarfe 10 sun kammala Komai,an gyara kitchen Ιin tamkar ba'a ta6a girki acikinsa ba,tun da wuri Abokanan Abba suka fara zuwa,Hada wasu daga cikin abokan Abusufyan wanda ke zaune a Nigeria,tuni gida ya fara ciki,tun da su sehrish suka tashi daga bacci ko arziΖin yin wanka basu samu damar yi ba,saboda kiransu da ake tayi,duk wanda yazo saiya buΖaci a kira mashi su ya gansu,daga sunje haka za'a dinga yabon kyawunsu ana sanya masu albarka,gashi duk wanda sukaje gaidawa cikin abokanan Abba,sai Yayi masu kyautar makudan kudi,babu wanda yayi masu kyautar Ζasa da naira dubu Ιari biyar,hosana duk tabi ta susuce,sae faman lissafin kuΙaΙen da suka samu takeyi,daga sun dawo cikin Ιaki zata fara fadin Abokin abba mai farin gemu ya bamu kyautar Dubu Ιari takwas,sae wannan abokin nasa mai sanye da kaki da yazo ya bamu kyautar gonaki guda uku,kuma ya haΙa mana da dawakai,Sai kuma wannan mai Ζaton tumbin shine ya bamu kyautar miliyan Uku,Ni miliyan Ιaya,Jahad miliyan Ιaya,sae sehrish itama miliyan daya,bayan shi kuma sae wannan abokin daddyn namu Ιan fari mai kumatu,wanda ya biya mana Umrah,Ashe da rabon zanje in ta6a ka'aba Ιakin Allah,harma in roΖe shi akan ya yaye mun haukan dake damuna,don banson jin anace mun Zararriya,haka ta dinga sambatu har sai da suka fara gajiya da surutun hosana,
Sehrish na cikin toilet tana wanka,amma hankalinta gaba Ιaya ya tafi akan Sgr,kalamanshi na jiya ne suka shiga dawo mata acikin kanta,dole tayi aiki a Ζarkashin shi batasan meyasa yake son ganinta a matsayin Ζ΄ar aikinsa ba,
Tana cikin wannan zancen zucin tajiyo muryar jahad,daga waje tana cewa"Sehrish dan Allah kiyi sauri ki fito,inaso nima nayi wankan,kafin asake kiran mu,"
jin haka yasa tayi saurin kammala wankan ta fito,Ιaure da towel a waist Ιinta,shiga ciki jahad tayi,don tayi wankan itama,duk hosana na zaune gefen gadonsu hannunta ruΖe da biro da memo din Sehrish sae faman lissafin kyaututtukan da suka samu takeyi,"
Girgiza kai sehrish tayi tare da cewa"Aiki ya same ki hosana,kowa na Ιokin zuwa yayi wanka amma ke hankalinki na akan kuΙin da muka samu,abunda baki sani ba,idan mukayi wanka mu kayi kwalliya,sae mun samu ninkin abunda muka samu a yanzu,"
Juyowa hosana tayi tare da waro ido jin an ambaci kuΙi tace"dagaske kike sehrish idan mukayi wanka mukayi kwalliya zamu samu fiye da wannan kuΙin da muka samu"?
Jinjina kai sehrish tayi tace"kwarai kuwa,ke dai kawai ki tashi ki fara yin wanka,jahad na fitowa,ki shige ciki,"
Cike da zumuΙi ta miΖe ta koma ta tsaya a kopar shiga toilet Ιin tana kwankwasa ma jahad,
"Ki fito nima in shiga,"
Murmushi sehrish ta saki,dama wayau tayi mata,don taji Ιazu suna magana da jahad tana cewa ita ba yanzu zatayi wanka ba,sae da marece,bayan tun yanzu akeso su shirya,don agansu da kyau,
Gaban dressing mirror ta zauna,tana shafa mai ajikinta,sae faman sauri takeyi saboda taje part Ιin Sgr,kamar yadda ya umarce ta akan taje da safe ta kai mashi breakfast Ιinshi,kuma ta gyara mashi bedroom Ιinsa,light makeup tayi a fuskarta,saboda wannan wankan safe ne zata Ιauka,da anjima Azmee tace za'ayi masu makeover,tamkar brides haka zasu fito,
Bayan ta kammala yin kwalliyar,komawa tayi wurin wardrobe din kayansu ta buΙe tana Ζare masu kallo,dama kullum zata zura kaya ajikinta sai ta tsaya yin ruwan ido wurin za6en kayan da zata sanya,
"Da rana zan sanya shadda lace Ιita,da marece kuma zan Ιauki wankan Swiss lace,yanzu dae bari na sanya wannan Arab gown Ιin,naga sai faman Ζyalli takeyi,in na sanyata ajikina,ba Ζaramin kyau zanyi ba,"ta Ζarasa maganar tare da janyo rigar,golden colour ce,gaba Ιaya jikinta adon stones ne masu Ζyalli da Ιaukar ido,batare da 6ata lokaci ba ta shiga kiciniyar zura rigar ajikinta,daΖyar ta shigeta saboda ta matse ta,gaba Ιaya tabi shape Ιin jikinta,kirjinta ya fito sosai,ga wani uban hips daya bayyana ajikin kayan,dama akwaita da diri sosai,don dai bata cika sanya kayan da zasu bayyana surar jikinta bane,hannun rigar na net ne,dogo ne ya kawo har wrist Ιinta,kana hangen fatar hannunta ta ciki,
siririn mayafin ta Ιauko,ta sanyashi asaman kafaΙarta,wa'iyazubillah,ba Ζaramin wankuwa sehrish tayi ba,juyowa tayi tare da kallon Hosana wadda ta saki baki tana kallonta,tace"Nayi kyau,"
Yadda hosana ta saki baki,tana kallonta ko kyaftawa batayi ba Ζaramin dariya ya bata ba,har saida ta ambaci sunanta,sannan hosana ta iya buΙe baki tace"Wlh kinyi kyau Sehrish sosai,kamar Ζ΄ar matan aljanna,"
Dariya Sehrish tayi yayin da ta koma gaban mirror tana kallon kanta,hannu tasa tare da daukar kwalbar turarenta,tabi jikinta ta feshe,sannan ta fuce daga Ιakin,tun da tafito idon kowa ya dawo kanta,abokanan matasan gidan da suka hallara a babban falon,duk saita tsargu,kitchen ta wuce anan ta samu Azmee tana zuzzuba ma saude abinci acikin warmers tana fitarwa waje,wurin baΖi tana kai masu,
Ae tunda azmee tayi arba da ita tashiga zuzuta kyanta,
"Aunty Azmee ni nasan ban kai haka ba,kawai kina hura mun kaine,".
Azmee tace"ae kin zarce duk yadda nake faΙi maki,dama shi mai kyau bai gane yana da kyau,sai in ana faΙi,"
murmushi kawai ta saki tare da cewa"Aunty azmee ina kayan breakfast Ιin babban yaya inaso nakai mashi,"
"Oh kin manta cewa abusufyan ya hanaki"?
"Nasani Aunty azmee,bansan ya zanyi bane,babban yaya jiya yace,baison ki Ζara aiki part Ιinsa,ni kawai yakeso in dinga zuwa inayi mashi aiki,kuma har faΙa mashi nayi akan cewa daddy ya hanani amma yace shi babu ruwanshi,kawai nayi mashi aiki,
Jinjina Kai azmee tayi tare da cewa"TabΙijancan,aikuwa akwai matsala!don wlh Abusufyan yaji wannan maganar bazai yadda ba,kuma ke in banda abunki kin manta wanene abusufyan a wurinki,mahaifinki fa ne,taya zaki tsallake umarninsa kibi na babban yayanku?hakan na nufin cewa yafi iko dake akan mahaifinki?kina ganin cewa abusufyan zaiji daΙi idan yaji cewa kin cigaba da yi mashi aiki"?
Jin wannan maganar ta azmee yasa jikinta yin sanyi,sunnar da kanta Ζasa tayi,tuni idonta sun ciko da kwalla,
GyaΙa kai azmee tayi tare da cewa"Nasan don baki da yadda zakiyi ne sehrish,zan shirya maki breakfast Ιin ki kai mashi,amma karki kuskura ki bari Uncle abusufyan ya gani,kuma koda ya kamaki,kada ki sanya sunana aciki,"
Amsa mata tayi da toh,
Batare da 6ata lokaci ba,Azmee ta shirya mata warmers da sauran tarkacen abincin acikin kayataccen tray ta bata takai mashi,'
Tunda sehrish ta fito daga kitchen Ιin gabanta ke faduwa sai faman waige waige takeyi,tsoranta kar daddynsu ya ganta,cikin sa'a ta haye upstairs batare da taci karo dashi ba,
Ajiyar zuciya ta sauke lokacin data Ζarasa cikin falonshi,babu kowa aciki,hakan yasa ta tunanin ko bai tashi daga bacci bane,tana ΖoΖarin shiga bedroom Ιinshi,taji muryar namiji a bayanta,
"Ji mana,"a firgice ta juyo don taga wanene,Ιan zaro ido tayi tana kallon matashin daya biyota,acan falo ta ganshi tare dasu kanal yousouf da alama abokinsu ne,
Murmushi ya sakar mata tare da cewa"Am sorry na biyo bayanki batare da saninki ba,nagaza jurewa ne shiyasa na yanke shawarar yin hakan,'
muryar sehrish na kerma tace"Am...um..dan Allah ka jira ni awaje,yanzu zan fito,
"Okey,zan tsaya awaje,but pls don't stay long,"
Ya faΙi hakan tare da juyawa zai fita,har ya sakai zai fita daga falon,ya kuma juyowa tare da kallonta har lokacin tana a tsaye yace"Kin tafi da imanina sosai,zan iyayin komai don na mallake ki,"ya Ζarasa maganar tare da fucewa,
Ajiyar zuciya Sehrish ta sauke aranta tace"Kowanene wannan jarababben,baisan nan part Ιin wanene ba,so yake yaja mun masifa,ya wani kwaso kafafunshi ya biyo ni,'
kamar ance ta juya,idanunta suka sauka kan Sgr dake tsaye ya goya hannayenshi asaman faffaΙan Ζirjinshi,fuskar nan kwata kwata babu annuri,daga shi sai short fari ajikinsa,
Gabanta ba Ζaramin faΙuwa yayi ba,Ζiris ya rage ta saki tray Ιin hannunta,tuni jikinta ya soma rawa,
"Zoki wuce ciki,"yayi maganar babu alamun wasa a fuskarshi,jiki na rawa ta nufi bedroom Ιin nasa,matsa mata hanya yayi ta wuce,sannan ya kama hanya azafafe ya fito daga falonsa,anan waje ya samu saurayin nan,tsaye yana jiran fitowar sehrish bawan Allah,ya Ιauki wankan suits,sae faman zabga murmushi yake yi,
..jin an ta6a kafadarshi yasa shi juyowa don yaga wanene,gabansa ne ya faΙi Rasss lokacin da yayi arba da sgr tsaye agabanshi ya ruΖe qugu,tamkar zaki haka ya koma mashi,mugun tsoranshi suke ji,saboda ko magana bata ta6a haΙashi da abokanan Ζannenshi ba,labarinshi kawai suke ji a wurin su Irfan,babu wanda baisan Sgr ba,wato babban yaya,
Fuskarshi a tamke yace"Wani ganganci ne yasa ka biyota har cikin part Ιina!"?
Muryarshi na kerma yace"wlh ni ba ita na biyo ba,zuwa nayi kawai don in gaishe ka,dama Jabeer ne yace yakamata muzo mu miΖo gaisuwa wurin babban yayansu,kaji dalilin dayasa na kwaso Ζafata nazo,"
Wani irin kallo sgr ya wurga mashi,jin ya sharara mashi Ζarya bayan yaji duk abunda yake faΙa ma sehrish,
Sunnar dakai saurayin yayi yana faman mazurai,tsoranshi karya kai mashi naushi,
Hannu Sgr yasa tare da ruΖo neck tie Ιinsa yace"menene sunanka"
Cikin sauri yace"Jazz,"
Sgr yace"Jazz ko?let me warn u,ka tsaya a iya matsayinka,in ba so kake ka kwana a gadon asibiti ba,ka rufe idanunka daga kallon matan mutane,hakan zaisa ka zauna lafiya,'yana kai Ζarshen maganarshi yace"just u can leave....."ae tunkan sgr ya Ζarasa maganar,Sir Jazz ya watsa da gudu jiki na rawa ya sauka downstairs,
Ajiyar zuciya sgr ya sauke tare da juyawa ya koma ciki,
a Ζopar shiga bedroom Ιin ya tsaya,yana kallon sehrish dake ΖoΖarin gyara mashi gadonshi,har ta ajiye mashi kayan breakfast dinsa,yadda ta rankwafa shape Ιin hips Ιinta ya fito sosai,ba Ζaramin kyau tayi masa ba,sai yanzu ya gane dalilin dayasa wannan saurayin ya biyota,tunda yaga babban kaya dole ya zauce,baisan cewa babban goro sai magogin Ζarfe,
gyaran muryar da yayi ne yasata yin saurin Ιagowa,tana ganinshi tasha jinin jikinta,Ζ΄an kame kame tashiga yi kamar wata mara gaskiya,Ζarasa shiga ciki yayi tare da samu wuri daga gefen gadon ya zauna,sannan anatse yace"Am hungry,"
cikin sauri ta dawo gaban table Ιin tashiga ΖoΖarin yin saving Ιinshi,coffee mai zafi ta fara miΖa mashi acikin cup,hannu yasa tare da kar6a,yana cikin kur6ar coffeen kamar ance mashi ya Ιago,idanunshi suka sauka akan Boobs Ιinta da suka fito sosai,tamkar zasu fasa gaban rigar,zukunnawar da tayi ne yasa suka yi hakan,
Nan take ya shaΖe,ba arziΖi ya ajiye cup Ιin dake hannunshi,gaba Ιaya duk yabi ya susuce ya shiga yin tari,tamkar maΖoshin shi zai 6allo,ganin haka yasa sehrish dakatawa daga yin saving Ιinshi da takeyi,tashiga yi mashi sannu,
daΖyar ya samu ya daidaita natsuwarshi,muryarshi ashake yace"Ke!ina scarf Ιinki yake"?
Muryarta na kerma tace"gashi nan agefenka,da zanyi gyara ne,na ajiye shi anan don karya takuramin,
H