RAWANIN TSIYA CHAPTER 1 BY FADEELAH RAWANIN TSIYA CHAPTER 1 BY FADEELAH Www.bankinhausanovels.com.ng MALLAM AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT-KANO STATE Zaune yake a cikin motar shi qirar BMW M340 baqa wuluk sannan sabuwa gal wadda ya faka a parking lot na airport din. Babu abinda yake tashi a cikin motar sai wani asirtaccen qamshin da humidifier take fesowa wanda ya gauraye da sanyin AC ya bada wani yanayi mai dadin gaske. Maganar gaskiya ita ce mamallakin motar nan ya kwana biyu yana hawan ta don haka ba wani abu ya janyo ake yi mata kallon sabunta ba, bala’in tsabta ne na mai ita. A yanzu haka da nake kallon interior na motar babu datti ko alama.. infact the car is spotlessly clean. Magana yake yi a waya through CarPlay. It’s exactly 10:30am. “…Yes Sir yanzu na karbi saqon” ya fada cikin muryar shi mai dadin ji wadda ga dukkan alamu zata yi tsada domin kuwa yadda yayi maganar zaka tabbatar ba mai yawan yin magana bane. On the other side of the call ne na ji yace “toh ko dai zaka tafi gida ne abinka tunda na ga yau Saturday k…