Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

TSINTACCIYA CHAPTER 2 BY NIMCY LUV

TSINTACCIYA CHAPTER 2 BY NIMCY LUV

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tsundum” sautin Amon faΙ—awarsa cikin kogin ya bada, kafin kuma wasu manyan Ζ™wayaye su fara firfitowa alamar wanda ya shiga cikin ruwan yana fidda numfashi.

Malam ne ya sauke Ajjiyar zuciya tsoro duk ya cika masa zuciya, Musamman like Md Adnan did! Yay Wani good jum before he fall in to the river.

Cikin damuwa Malam ya kalli Drive yace “Yadai iya ruwan sosai ko? Nasan Adnanu gwamma shi da Ι—an uwansa, bana son rasa rai biyu a lokaci guda, Akeela nada matuΖ™ar muhimmaci a rayuwata haka Adnanu”

Shiru Driver yay domin like serious bai san komai ba amma dai yasan Adnan na yawan shiga wani ruwa.

Isiya ne yace “Uhm yadai iya ruwan ko?” Kallonsu driver yay kafin yace.

“Not sure! Amma Ƙaramin Mai gida yana shiga swwiming pool sosai yana son wasan ruwa, ta takalmin taya, amma dai ruwa kamar wannan bana da tabbacin yana shigarsa”

Malam ya kalli ruwan yace.

“Allah ka taimaka ni, ka duba lamarin wannan yaran”

Juyawa Driver yay yace “bari na kira taimakon kwanakwana incase”

Wajan motar ya nufa ya Ι—auki Wayarsa tare da fara shiga goggle yana duba yadda zai samu impormation na ma’aikatan mafi kusa da garin.

Md Adnan wani numfashi yaja mai wahala yana jin yadda numfashin nasa ke wata fisga kamar zai bari Ζ™irjinsa.

A hankali kuma ya Ι—aga hannunsa zuwa sama kafin ya ware legs Ι—insa, idanunsa dake a rufe ya buΙ—e yana kumbura bakinsa tare da fidda numfashi.

Girman ruwan da yadda yaga ruwa yay bala’in firgitar sa.

Cikin sauri kuma yay baya da hannunsu yana ware Ζ™afa tare da fara nutsu cikin ruwan yana ninΖ™aya, ya Ι—auki good 10minutes yana duban Akeela amma babu ita, yana Ζ™oΖ™arin juyawa idanunsa ya sauka akan ta tana jin wani reshe na baΖ™in ruwan daya riΖ™e mata riΖ™a.

Hijab Ι—in jikinta tuni ya zame yay gaba, gudun ya Ζ™ara yana cimma ta yana gab da zuwa inda take wata igiyar ruwa ta riΖ™esa cikin kuma rashin Sa’a Wani irin ruwa mai yawan gaske ya tawo cure guda.

Wani kalan ware idanu Md Adnan yay kafin yay wani yunΖ™uri na guduwa ruwan yay gaba dashi ji kake “Shuuuuuu” sautin gudan ruwan ya bayar.

Dawo Driven yay yana faΙ—in “na kira, in sha Allah dukkan su noting will happen to them” Cikin damuwa Malam yace “Amma ko motsi babu, ji yadda ruwa ke gudu tsoro ya kamani sosai” “aifa da tsoro mutane har biyu ga wannan bawan Allan da gani bai saba da wahala ba” cewar Sunusi yana mai Ζ™ara leΖ™awa cikin kogin.

A can cikin motar Md Adnan Wayarsa ce take ta ringing kira na wajan uku kenan amma babu respond! A hankali motar da fara shigewa wani matashi ya fara knocking Ƙofar motar hannunsa riΖ™e da wayarsa yana Ζ™ara danna number Md Adnan yana mamakin abinda ya tsayar da shi har yanzu bai Ζ™arasu ba gashi lokaci na tafiya.

Daga cikin motar wani mutum ne mai kimanin shekaru 32 a duniya, yana zaune a back seat idanunsa maΖ™ale da wani farin glass na haΙ—aΙ—Ι—un goyon nan.

Sanye yake da wata fitinanniyar Double breasted suit dark Maroon. Gashin kan nan nashi yay kwance har wuya daga gaba ya kwanto, sai Ζ™yalli yake yasha Ginger Geminal Oil hair.

Kakkauran laΙ“Ι“ansa pink irin yirr Ι—in nan lokacin zuwa lokacin yana taune su like his punishing kansa, fari ne tass irin farin nan da kai tsaye ba zaka iya tantance na wani Ζ™asa ko kuma jinsi ba, yana da kyau sosai looking soo damn sexcy and hot!

Irin manyan mutanan ne masu tashe da zamani irin definition of classic masu fama da mahaukacin kuΙ—i na halak.

Idanunsa ya janye daga kan haΙ—aΙ—Ι—iyar Ζ™aramar Apple system Ι—insa yana maida idanunsa Submariner Rolex ganin lokacin yaja ya Ι—an saki siririn tsaki.

Deep down kuma zuciyarsa na wani irin bugawa da Ζ™arfi, like something bad gonna happen to him.

Irin mutanan ne da wahala ka fahimci sauyin fuskarsa, farin ciki da damuwa baya sanyawa kaga sauyi a saman fuskarsa.

Yana da kamilalliyar fuska mai cike da ilhama da kuma tarin nutsuwa abu guda ke sauya masa tunani yaji ana masa ihu a saman kansa, ko kuma yaga anci zarafin wani Ι—an Adam.

Zame system Ι—in yay tare da ajjiye ta a gefensa, cikin nutsuwa ya fara juyawa laΙ“Ι“ansa yana motsawa a hankali.

A taushashe sautin fitar amon muryarsa ke tashi yana faΙ—in.

_“Asstagafirullah, Walahamdulillah, Wallahu Akbar”_ shine Amon kalaman dake fita a bakinsa.

A karo na wajan huΙ—u P.a dake tsaye daga baΖ™in Ζ™ofar ya Ζ™ara Knocking Ζ™ofar, taΙ“e baki yay kafin ya Ι—aga hannunsa tare da danna glass Ι—in motar yay Ζ™asa.

P.a ne ya kalli mutumin cikin motar yace.

“5times ina kiran number Md amma no answer”

A karo na farko bayan sauke glass motar  Dr. ABDUL-HAKEEM BUKAR BELLO ya Ι—aga idanunsa tare da kallon P.a idanunsa kawai ya juya da sauri P.a yace.

“Ok lemme try it”

Ya faΙ—a yana Ζ™ara danna number Md Adnan, kafin kuma gently ya miΖ™a hannunsa ya buΙ—e murfin motar, kamar bai so haka Dr A.b ya fito da Ζ™afarsa kafin kuma ya fito daga motar baki.

Lumshe idanunsa yay saboda iskar Ζ™asa da Ζ™amshin sabbin shukokin da akai da suke dukan hancinsa.

Yana da tsayi da faΙ—i jikinsa a murΙ—e yake ga wani faΙ—in Ζ™irji da yake dashi _(Physique chest)_ bayyanar Ζ™wayar idanunsa a yanzu ya tabbatar cewa shi Ι—in _(Half-caste)_ ruwa biyu kenan.

Zare jacket Ι—in yay ya saΖ™ala a hannunsa yana mai sassauta necktie Ι—in wuyansa.

“Sir har yanzu ga, gashi mun tara mutane sun taro mu kawai suke jira”

TaΙ“e baki yay walking slowly ya nufi wani ma dai-dai cin waje da aka gyara yay ta tass ga kujerar da aka sanya masa.

Maida wayar P.a yay zuwa aljihunsa yana mai mamakin abinda ya hana Md Adnan Ι—aga wayar da kuma mamakin rashin Ζ™arasuwar sa is anything okay Babu damuwa ai rashin sanin dalilin shine damuwar.

Waje Dr A.b ya samu wanda wasu jama’ar suke kiransa da AKEEM ya zauna yana mai sassauta haΙ—ewar fuskarsa saboda ganin duk manya ne a wajan wanda shekarunsu, suka ja ainun.

Cikin mutunci ya buΙ—e bakinsa a nutsu yace “Assalamu alaikum warahamatullah”

Gaba Ι—aya mutanan suka amsa masa kafin yay Shiru yin shirun nasa ne kuma yasa P.a dake gefensa a tsaye yace.

Al’amarin ya girmi tunanin su Malam tashin hankali sosai ya bayyana akan fuskarsa yasan yadda Ζ™aninsa Bukar Bello ke bala’in son yaran nasa fiye da komai na rayuwarsa, yanayin komai saboda dasu ya hakan salwantar da nasa farin cikin just to see them happy, yaya zai kasance idan wani abu ya faru da Md Adnan? Wannan dalilin yasa baya barin su ko’ina sai companies Ι—insu da gida ko kuma Ζ™asar waje, he cares about his children yana mutuwan son su, ko zazzaΙ“in su baya jurewa musamman Mai sunan kawonsu.

Driven Md Adnan ne yace “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un yanzu mene zance da Babban mai gida eh? Dan Allah? Yau warning Ι—ina akan na kula da driving Ι—in Md Adnan ya kula dashi amma gashi shine ma yace ya shiga ruwan Ζ™ilan dai yama kashe sa idan yaji labarin haka, domin yasan baΖ™ar zuciyarsa.

Malam ne yace “Ubangijin sammai da Ζ™assai ya kawo mana Ι—auki, Wannan wanne irin tashin hankali ne eh?”

Ya faΙ—a hawaye na zubu masa.

Kafin kace wani abu tuni mutane sun taro wajan yara da manya, a dai-dai lokacin ne kuma motar kwanakwana ta Ζ™arasu suna zuwa suka fara aikin su nan da nan suka shiga cikin ruwan, sama da mintuna talatin babu Md Adnan babu Akeela.

Tuni Driver ya fara kuka yana faΙ—in “shikenan wallahi na shiga uku wajan Babban mai gida, eh ina laifin Ζ΄ar kazar da nake ci na kwana katifa mai taushi ha banΙ—aki kamar ma kwanci, suttura kala-kala, eh? Duk banga haka ba ga Ι—an ilimi dana samu na kan iya jin turanci ko yaya ne amma yanzu na tura masu Ι—a cikin ruwa i can’t forgive myself if anything happens to Ƙaramin Mai gida”

Wayarsa dake Ζ™ara ya duba ganin sunan Alhaji yasa ya Ι—aga jiki na rawa yace.

“YallaΙ“ai” gyara zama Alhaji Bukar Bello yay saman kujera hannunsa Ι—auke da Mug yana shan coffee, yana sanye cikin Arabian Jallabiya mai taushi da laushi a Ζ™alla zai kai shekaru 63 amma jikinsa sam bai nuna ba, kyawunsa na samartaka na nan.

Cikin Ι—an sakin fuska yace “Bala” da sauri Driven yace “Na’am Yay.. YallaΙ“ai” ya Ζ™are maganar muryarsa na rawa, gaban Abbu ne ya faΙ—i haka kawai yaji zuciyarsa na tsinkewa cikin Ζ™asa da murya yace.

“Bala where is my friends?” Shiru Bala driver yay yana zare idanu jin haka yasa Abbu miΖ™ewa tsaye tare da goya hannunsa a baya a kaushashe Muryar nan babu wasa yace “Bala yarana” jin haka yasa Bala fashewa da kuka yace.

“Tsautsayi da kauΙ—in harshe, Allah na tuba ka yafan…,” Da sauri Abbu ya katse sa da faΙ—in “heeyyy Bala this is the last time da zan tambaye ke where is my friends? Ina cute  two kids Ι—ina? Suna ina Eh Bala?”

HaΙ—iye kukan Bala yay kafin yace.

“YallaΙ“ai Ƙaramin Mai gida ne ya shiga ruwa kuma…” Gaba Ι—aya ya faΙ—a masa abinda ke faruwa. Tun kafin ya gama jikin Abbu ya hau rawa idanunsa suka KaΙ—a ganin yana Ζ™oΖ™arin faΙ—uwa yasa da sauri matarsa mai suna Hajiya Ayusher suna ce mata Ummi tayi saurin miΖ™ewa yana ganin ta ya faΙ—a jikinta ya rungome ta sosai jikinsa na wani irin rawa bakinsa na Ι“ari yace “My Adnan My Friends ya rana Ayushertu” ya faΙ—a yana Ζ™ara matseta a jikinsa.

Jikin Bala Driver na rawa hannunsa wanda yake riΖ™e da wayar ya riΖ™e sosai yana faΙ—in “kai,kai! Ka tsaya mana wallahi yallaΙ“ai bani da laifi idan ka kuran ina zan dinga cin shinkafa? Ina zan dinga cin naman nan naku mai daΙ—i da romo? Innalillahi wayyooo Ni Bala na shige su”

Shiru yaji babu maganar Abbu sai Ummi dake faΙ—in “Subuhanallah, Abbu Meke faruwa da yaran namu? Didi! Didi! Mami” ta shiga kiran sunan mutane.

Da sauri Bala ya koma wajan kogin har yanzu babu wani labari, Ι—aya daga cikin ma’aikatan ne ya fito jikinsa duk ya jiΖ™e da ruwa.

Da sauri Malam yau wajansa yana faΙ—in “Yaya! Wa aka fara cirowa” girgiza ma’aikacin yay yana sharce ruwan fuskarsa yace “till now babu wanda muka gani, ruwa ne yake da ambaliya daga Ζ™asa, Amma we’re still searching in sha Allah za’a same su”

Shiru kawai Malam yay tare da neman waje ya zauna yana ta sauke ajjiyar zuciya.

A hankali p.a Ι—in ya kalli mutanan wajan yace “Kamar yadda kuka sani, kai ya waye lokaci yazo wanda ba sai munce dole sai gwamnati ta taimaka mana Sannan za muyi wani abun ba, ko zamu jira gwamnati at least we have to…” Gyaran Murya Akeem yay da sauri P.a yace “Yes sir” kallonsu yay yace “kuyi hqr bakina yana juye zuwa wani harshe daban, yana da kyau mu fahimci cewa idan muka ce sai mun jira gwamnati Tabbas zamu mutu babu mallaki komai na rayuwa ba, idan nace komai ina nufin, Ilimi both buko da Arabic, Ζ΄an ci, Ζ΄anci na nufin ka samawa kanka abinda babu wanda zai wulaΖ™anta ka, babu wanda zai kanka yace dan Meye ne kai Wannan? Ka zama komai kai updating kanka daga old version zuwa latest version something new haka” shiru yay yana kallon yadda Akeem ya yatsuna fuska kafin ya Ι—ura da faΙ—in “mun samu saΖ™on ku daga office Ι—in mu dake   AKEEM BETTER FARMING INSTITUDE A.B.I na samu sanarwar daga wajan H.o.d Ni kuma na faΙ—awa Md Adnan, Md ya faΙ—awa C.E.O na wannan makaranta zance maku ne ko ma’aikata? Bama duba messages Ι—in da bana e-mail bane, amma muhimmacin garin da kuma albarkatun noma da muke dashi a wannan garin me albarka Sir Akeem kuma Dr Abdul-hakeem Bukar Bello C.e.o of Akeem better farming institute yace a shirya tafiya kafin yace fara gabatar da aikinsa da Za’ai a channel Ι—in M.hausa dake GOtv and DStv yanzu muna son Ι—aya daga cikin ku ya faΙ—a mana matsalar ku”

Wani babban kuma mai Ι—an shekaru ya miΖ™e bayan yay godiya ne ya Ι—ura da faΙ—in.

“A kullum muna fuskantar barazana daga wajan manyan mutane wanda suka tsoratar damu da faΙ—in sunayen su”

Akeem da idanunsa ke Ζ™asa yana zuciyarsa na tsalle kamar zata faso Ζ™irjinsa ta fito saboda faΙ—uwar gaba ya Ι—aga idanunsa ya kalli mutumin kamar bazai magana ba sai kuma yace “Uhm” yana faΙ—in hakan yay shiru da sauri kuma P.a ya miΖ™a masa gorar ganin yana shafa Ζ™irjinsa cikin Ζ™asa da murya cike da tsoro mutumin yace.

“Sunce mu bar masu gonakin mu akan kuΙ—i dubu Ι—ari biyar biyar ga dukkan mutumin daya sanya hannunsa a kan takardar, za suyi ma’aikata, da farko Bamu san wacce kalar ma’aikata bace, yaran mu masu tashi sune abin tsoro, mun yarda da noma, kuma itace arziΖ™in mu da dukkan wanda yake Ζ™asar Nigeria, Noma toshan arziΖ™in mu kuma kwanciyar hankalinmu mu manoma, wasu nayiwa noma kallon wani abu nada ban amma da ace mutum zai san amfanin noma da kuma ribarta to hatta samarin da suke da kwalin jami’a tabbas zasu ajjiye dugun buri su tawo gona domin yin Noma, babu buΖ™atar kuΙ—i gonakin mu muke buΖ™ata, Ζ™auyen dake gaban namu sun amince bisa shawara dana masu har Abin yake neman juyewa zuwa tashin hankali, shine yasa muke neman taimako daga gareka ka shiga wannan lamarin muna buΖ™atar gonakin mu” ya faΙ—a yana haΙ—e hannayensa waje guda, ganin hakan yasa gaba Ι—aya mutanan wajan suka miΖ™e suna haΙ—a hannayensu waje guda.

Da sauri Akeem ya miΖ™e yana fidda numfashi domin baya Ζ™aunar wani babba ya duΖ™a masa.

Wata haΙ—aΙ—Ι—an jotter da pen P.a ya bawa Akeem cikin sauri ya fara rubutu mai cike da tsari daga Ζ™arshe ya rubuta.

           _From Akeem better farming institute_

              To

    _marasa tsoran Allah masu son ci da gumin wasu_

      Sign ~Abb hero~

Yana gama rubutawa ya miΖ™awa P.a idanunsa Ζ™asa dan bai so ake ganinsa kafin a hankali cikin fitar wata Amon murya irin golden voice Ι—in nan yace.

“Ku Ι—auka ku Alhalin Abdul-hakeem Bukar Bello ne, babu abinda zai samu lafiyar ku, Alhalin ku, duniyoyin ku” yana faΙ—in hakan ya juya walking slowly irin tafiyar nan mai Ι—aukan hankali.

Cikin sauri kuma a ransa ya furta “Adnan” da sauri ya nufi mota ganin hakan yasa P.a yabi bayansa motar ya shiga kana yana da gudu hankalinsa gaba Ι—aya yay kan Ι—an uwansa yana mutuwar son ganin nasa, he Loves him yafi son komai zai faru ya same su tare.

Wayar Md Adnan ya kira amma babu answer hakan yasa Murya can Ζ™asa yace.

“Uhm p.a drive faster”

Gudu ya Ζ™ara suna zuwa dai-dai wajan taron jama’a Bala driver na Ι—aga kiran Akeem ganin sunan Blood yasa Bala ya shiga uku.

Bai tsaya jiran jin abinda Bala zai faΙ—a ba, da sauri p.a ya fito daga motar yana buΙ—ewa Akeem murfin motar, kai tsaye idanun Akeem ya sauka akan Baffansu.

Da sauri Malam ya miΖ™e ganin Mai sunan kawonsu yace.

“Kaga abinda ya faru ko? Daga zuwan Adnanu ya haΙ—u da aljalinsa” da wani irin kallo Akeem yabi Malam yama kasa gane mene sauke faΙ—a.

Ka kaff Malam ya bawa Akeem labarin abinda ya faru, nan da nan fuskarsa tai jajirrr saboda tashin hankali amma ko kaΙ—an babu wani alamar tashin hankalin cikin Ζ™wayar idanunsa saboda shegen shanye abune dashi a rai.

Zame jikinsa yay daga wajan Malam kai tsaye wajan ruwan ya nufa Malam na faΙ—in “A’a Mai sunan kawo kada mu rasaka dan Allah ka tsaya..” kafin ya gama magana tuni Akeem ya faΙ—a cikin kogin nutsu ya fara cikin ruwan cike da Ζ™warewa yake sarrafa ruwan tamkar dai wanda ya san kanshi babu jimawa idanunsa ya sauka akan wani Abu mai duhu, cikin sauri yay wajan yana zuwa yaga mace saΖ™ale jikin reshe Ζ™arasawa yay wajanta yana mai Ι—an Ζ™ara ware idanunsa ganin babu Md Adnan babu Labarinsa wani iri tsoro ya kamasa cikin damuwar ya nufi wajan Yarinyar yana zuwa yay wani irin…..

Tura kansa dake cikin ruwan zuwa waje yay yana haΙ—a numfashi, cikin wata kasalalliyyar murya mai cike da alhini yace “I got her” yana faΙ—in hakan kwanakwanan suka cilla masa duguwar igiya ya kama tare da Ι—aura igiyar a ququnsa.
Cikin saurin ya nusa cikin ruwan kafin a hankali ya kama igiyar data riΖ™e Ζ™afar Akeela.
A hankali ya kunce igiyar gaba Ι—aya Akeela tayi baya tare da fara yawo a ruwan zata matsa can gefe saboda ruwan da yake gudu sosai,
Fararan tafin Ζ™afafuwanta yabi da kallo, sunyi wani mugun haske kamar jini zai zuba a jikinta saboda farin da take dashi.
Tattausan hannunsa ya miΖ™a tare da jawo tafin Ζ™afarta “kittt” ya jata da zuwa inda take Ζ™arar tawowar wani ruwa ne ya daki kunnansa da sauri ya fisgota yana runtse idanunsa tare da sanya dukkan hannayensa ya wist Ι—inta ya wani Ζ™anΖ™ame idanuna da hannunsa dake bisa jikinta ko motsi ya Ζ™iyi.
Ya Ι—auke dukkan Numfashinsa yana jin sanda ruwan ya shige ta gefensu kamar zai tafi dasu.
Zaro kanta dake jikinsu yay sai a lokacin idanunsa ya sauka akan fuskarta _Tsarki  tabbata ga Ubangijin daya halicci sammai bakwai da Ζ™assai bakwai, Ubangijin daya halicci wannan duniya ya kuma halicci wannan surar dake hannun Akeem_ faΙ—in asalin kyan fuskar Akeela bata baki ne, tana da wani irin sahihin kyau, wanda ya wuce tunanin mai tunani, idanunta a rufe suke ruff amma eye lashes Ι—in nan da suke dugwaye  slick dark blck sunyi kwance saman kumburarrun idanunta, ga dugun hancin nan mai kyau sosai, wanda ya tsaya dai-dai tsagen laΙ“Ι“anta wanda suke da kauri sunyi jajir dasu.
Gashin kanta data Ι—aure da ribbon tuni ya wargatse ya baje yana yawo cikin ruwa sai ta zama kamar wata aljanar cikin ruwan da mutanan suke faΙ—a.
TaΙ“e baki Akeem yay kafin cikin zafin nama yay wani cillata bayansa ya goyata sosai kafin ya gyara zaman igiyar jikinsa.
A hankali ya fara ta suwa sama cikin Ζ™warewa kwanakwanan na ganinsa suka fara jawo igiyar ruwan.
P.a ne yabi Ubangidan nasa da kallo yana tuna wani abu daya wuce amma ya rasa ko menene, amma Tabbas ganin Akeem goyo da Akeela ya tuna basa wani abu mai mata tuΖ™ar muhimmacin a rayuwarsa.
A fili Malam ya furta “Allahamdulillah biii rahmatiikaa”
Suna zuwa bakin ruwan yay wani irin baya yana daga tsaye yay wurgi da Akeela ta faΙ—i Ζ™asa ji kake “timmm” kanta ya bugu Ζ™asa amma ko motsi ba tayi ba saboda bata hayyacinta ta jima da sumewa.
Jikin Akeem na wani irin kyarma da rawa idanunsa sunyi jajir jijiyoyin kansa sun yi bala’in tashi sai wuci yake na zafin zuciya da kuma sayin ruwan daya gama ratsa dukkan kofofin jikinsa.
Kai tsaye wajan Bala driver ya nufa, ganin haka yasa P.a ya mara masa y domin yasan anything can happen idan Akeem ya Ζ™arasa domin a wannan karan Ι“arin da jikinsa yake ya bayyana asalin zafi da kuma Ζ™uncin da zuciyarsa keyi, ya bayyana how sad he’s.
Yana zuwa ya kalli Bala driver murya can Ζ™asa yace.
“Car keys?” Zare idanu Bala driver yay kafin ya fashe da kuka yace “Dan Allah dan Annabi kayi min suttura Babban mai gida, ka tausaya min kada ka kuran i don wanna lose my job dan Allah, dashi kawai nake kula da iyali na, na sani a made a mistake amma bani na tursasa Ƙaramin Mai gida shiga ru…”
Gigitacciyyar tsawar da Akeem ya daka masa yana faΙ—in “Heyyy, car keys nace kaban, kada ka tunzura ni ka bari zanyi Shari’a dakai da ita kanta tsinanniyar datai Coursing wannan abun i hate her, idan ina da rai da lafiya billahi I’ll take a revenge, you’ll see mene zan, common my friend bani” da sauri Bala  driver ya miΖ™a masa tarin kyes Ι—in, huci kawai Akeem yake idanunsa a Ζ™asa domin duk abinda zai bai fiya kallon mutum ba, gyaran murya yay jin haka yasa p.a faΙ—in Md Adnan’s phone’s, his I.d card” wayar ya miΖ™a masu kafin ya Ι—auki walet Ι—in dukkan wani card da ake amfani da shi ya bawa P.a.
Kai tsaye mota Akeem ya nufa zai shiga ko takan Yarinyar baibi ba, kafin ya shiga motar P.a yace “Sir” da sauri ya juya yana dafe kansa  cikin haΙ—ewar fuskarsa nan nashi yace “what again P.a Al’kaseem Yahya gama?” Yadda ya kira full name Ι—in P.a yasa kowa na wajan kallonsa a sanyaye p.a yace “Abbu” ke kira.
Kamar bazai amshi wayar ba sai kuma ya amsa walking slowly yake tafiya yana baje gashin kansa wanda ruwa ya jiΖ™a daga can Ι“angaren Abbu yace.
“Son” marai-raice  fuska yay ba tare da yace komai ba, jin haka yasa Abbu faΙ—in “Are You okey?” Nan ma shiru yay bai ce komai ba hakan yasa Ummi dake gefensa faΙ—in “Is everything okay?” Didi dake tsaye riΖ™e da bakin zani tsohuwa ce sosai shekaru sun ja tace.
“Ihuu jama’a, bana faΙ—a ba? To kai dai Bukari ka haifi Ι—a baka haifi halinsa ba, yaro baΖ™in hali yay masa yawa a to ai duk duniya ba sun shaida, jiya kana gani ilahirin tsiran daka kawo min ta tasss yabi dare ya sace, to Ι“arawo ne fa? Banda maye waye ne zaice wani tsire ehe? Ai saini da cinsa ya zame min dole amma ina dai ba faΙ—in wasa wallahi Bukari ka nemawa Ι—an ka magani bana son na fita ana min cune da baki ana gata can, jikanta maye ne, mece cin nama da zaro harshe waje…..”
Shiru tayi Saboda saukar Muryar Akeem da taji ta wayar tana faΙ—in “Keeee!” Zare ido Didi tayi sai kuma ta fashe da kuka tana zare bakin zabi tana faΙ—in “to! A nan gidan duniya idan ban sawa Audil albarka ba wa zan sawa? Eh? Ta ka samu Iyaye da basu san komai ba ina nan ina jan casbie sai da nayi salati miliyan tamanin da shida to astagafirullah kamar dai bakai haka ba”
Girgiza kai kawai Abbu yay kafin yace.
“Friend ina son?” Ajjiyar zuciya Akeem ya sauke kafin yace “Abbu she killed my brother ta kashe mana Adnan” MiΖ™ewa Abbu yay kafin yace “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un Adnan ya mutu?” Wane kalar zabura Didi tayi sai ga zani a Ζ™asa tama Ζ™asa magana.
Ummi bakinta ta rufe saboda kukan da yazo mata da sauri tayi bedroom Ι—inta, Mami kuwa idanunta kawai ta Ζ™urawa Abbu Allah yasa raguwar yaran duk suna makaranta Amani kuma tana bacci.
Cikin dauriya Abbu yace “Stay there Abdul-hakeem, in sha Allah on my way yanzu nan kuje gidan Baffa” yana faΙ—in hakan ya kashe wayar tare da nufar part Ι—insa..
Ƙasa Mami tayi da kanta sai sauke Ajjiyar zuciya take, Didi kuka kuka ta fasa tana faΙ—in “Wanne gantalallan ne Adunan? Laa Muhammadur Rasulullah S.a.w ku tare ni kada naje Ζ™asa”
Kwantar da Akeela akai a Ζ™asa TaΙ“a jikinta Malam yay yaji wani mugun sanyi, a dai-dai lokacin har sarkin ruwa yazo amma neman duniya babu Md Adnan gaba Ι—aya suka rankaya zuwa gidan Baffa, suna zuwa Malam yace “Rabi maza haΙ—u min gaushi” babu jimawa ta dawo Ι—auke da gaushi MiΖ™ewa yay yana fita yace “maza sauya mata kaya Wannan na jikinta yay sanyi da yawa” Murmushi kawai Baba Rabi tayi yana fita ta miΖ™e tsaye tare da kunce bakin zani wata Ζ™aramar (Laya) ta Ι—auko tare da samun kan Akeela wajan tsakiyar kanta ta haΙ—a da Layar ta rufke gashin wajan layar da shige ciki.
Wani Murmushin ta sakeyi ita kaΙ—an tasan abinda take kafin ta sauyawa Akeela kaya ta rufe ta da zani jikinta yay sanyi sosai kamar Ζ™anΖ™ara.
Har lokacin Akeem bai shigo gidan ba, yana cikin mota sallah kawai ke fito dashi.
Wajejen Magrib Abbu ya Ζ™arasu daga kano da Wudil, har lokacin kuma Akeela bata farka ba, jiki a sanyaye Abbu yace “Baka da laifi, infact Adnan taimako yaje yi, Allah kaΙ—ai yasan abinda ya samu Adnan, yana ruwan? Mutuwa yay? Tafiya ruwan yay dashi no one’s know! Tabbas idan nace banji zafi da baΖ™in cikin abinda ya faru ba nayi Ζ™arya, amma ni musulmi ne waman Ζ™addararllahu haΖ™Ζ™a Ζ™adrihi, kuma Innallaha ba’assabirin  zanyi addu’a zan saka ai idan har Adnan n raye Tabbas zai dawo gare ni”
Jinjina kai Malam yay kafin yace “haka ne, Ubangiji yasa Adnanu yana raye yaron Ζ™warai” MiΖ™ewa Abbu yay yace “Ina ita yarinyar ya farka ne?” Girgiza kai Malam yay yace “A’a muje ka ganta” gaba Malam yay Abbu ya bisa a baya cikin tafiyar nan nashi irin na Akeem yana sanye da wata bugaggiyar shadda dark Ash sai jaddara sai Ζ™amshi yake.
Malam ne ya fara shiga sai Abbu yana shiga idanunsa ya sauka akan Akeela gaba Ι—aya tunaninsa ne ya tsaya cak, zuciyarsa na wani irin harbawa Kallonta yake tamkar zai cinyeta ko ya mayar da ita ciki, wani irin kallo ne mai kama da wanda ya kamo da soyayya! “Bukar! Bukar!” Da sauri yaja numfashi yana shafa Ζ™irjinsa kafin ya kalli Malam da sauri kuma ya juya yana kallon Akeela dafe Ζ™irjinsa yay ji yay wani mugun so da Ζ™aunar Akeela ya sauka a zuciyarsa har yana jin idan bai aureta ba zai iya mutu….
? Alhaji ka taro match, mata biyu? Eh? Yara sama da biyar kaga Ι—anya sabuwar nona kace kana so? Jama’a me kukace anya Abbu bai so zuciyarsa ba????

Post a Comment for "TSINTACCIYA CHAPTER 2 BY NIMCY LUV"