ZUMA CHAPTER 1 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 1 BY SHATUUU
ZUMA CHAPTER 1 BY SHATUUU Www.bankinhausanovels.com.ng  Sunana Fadima amma a gidan mu ana kirana Nanah, nakan manta cewar suna na Fadima saboda hatta a school Nanah ake kirana dashi. Gidan mu na kanyi murmushi duk lokacin da zan bawa wani labarin gidan. Kuma kuma a hankali zaku fahimci daga gidan dana fito. Mahaifina dan asalin hadejia ne ta jihar jigawa, mahaifiyata mutuniyar bidda ce dake jahar niger so you can imagine yadda aure yake kaika ko ina. Mamata banufiya ce wadda idan ka kalle ni zaka ga traces na nufawa a jikina most especially idanuna, inada ido shiyasa mutane suke ganin inada kyau to amma nasan ba komai ke rudar su ba illa maganai da nake dasu. Ni baka ce kamar yadda aka sani idan ka fiya baki a jigawa akan ce ko kai din dan hadejia ne?  To nima haka nake ban bar wannan gidan ba nayi musu kara sosae, saboda mahaifina baki ne kuma a gidan mu ina daya daga ciki top 3 blacks. Yayan Daddy mu goma sha uku ne amma ina tabbatar muku tara daga cikin mu kowa da mahaifiyar shi, sau…