WALIJAAM CHAPTER 1 BY MAMAN TEDDY

WALIJAAM CHAPTER 1 BY MAMAN TEDDY
WALIJAAM CHAPTER 1 BY MAMAN TEDDY  Www.bankinhausanovels.com.ng  *?WALIJAAM?*            _Maman teddy?_               _page 1_2_ _Da sunan allah mai rahma mai jink’ai” dukkan godiya ya tabbata ga allah uban gijin talikai Allah ina rokan ka yanda na fara wannan littafi lafiya allah kabani ikon kammala shi lafiya ameen ._ _*Wannan littafin tun daga farkon shi har karshen WALIJAAM sadaukar ne ga dukanin  fulani?*_ Alheri writers asso.? ****** “Wani irin iska ne yake tashi daga sararin samaniya ,wanda in badon yanayin da ake ciki na Rani ba da tabbas ka alamta cewa wannan goguwar ruwan sama ne yake dab da tsinkewa. Wata yar budurwan bafullatana ce na hango wacce a shekaru bazata haura 13 ba tana sanye da kayan ta na sak’i ,da ka gane ta kaga bafullatana ta usul ,sanye take da kayan fulani farar sake da akayi masa ado da blue din abawa hannun ta dauke da dan madaidaicin sanda ,wanda yayi dai dai da tsawon wannan yarinyar bafullatanan . Gyefe guda ta juya da idanun ta tana mai bin shanayen ta da kall…