UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 14 BY SHATU UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 14 BY SHATU Www.bankinhausanovels.com.ng Har me napep din ya fara kokarin ja, ta tsayar dashi tunawa da tayi Babu kudi hannunta, a hannun Amira da har lokacin take tsaye ta karba kudin sannan ya nufi race course da ita, tunda Suka nufi gidan ta hango motar Ismail Yana reverse da alamar zai bar gidanne, ta rufe fuskar ta yadda bazai ganta ba, shima dake Kai ya dauka caji Bai ma lura da ita ba. A kofar gidan ta fito hannunta rike da sabuwar halittar da ya kamata ace a killace take Amma se gata ana yawo da ita cikin napep. Ta sallameshi sannan ta nufi cikin gidan, tun daga kan security Suka fara gaida ta saboda sanin matsayin ta, kowanne mamakin me ya fito da ita itada aka ce ta haihu Daren jiya, straight parlor ta wuce sede dama tun a compound din gidan ta lura da motoci uku baki tana Kuma saka ran cewar barka suka fara zuwa se kace ba ita ta haihu ba.+ ” Kaya sunyi kyau sosae Hajiya Furaira, ni se Naga kamar nata sunfi na matar tashi kyau” Abinda ta fara ji ken…