SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 3 BY Xayyeesherthul-humaerath

SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 3 BY Xayyeesherthul-humaerath
SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 3 BY Xayyeesherthul-humaerath                   Www.bankinhausanovels.com.ng  Karatun tai hankali kwance sunfito ke nan dai,dai gate din makaranta zasu fita wata  Yarinya da zata kai shekara ashirinne ta dumfarota da sauri, bangaje Nafeesa tai har sai da glass dinta ya fadi kasa, “Maga tayi ai,ke har kin isa ki tabamin Mutansir a makarantarnan,yar matsiyata, ko me kika masa ma ya nace miki oho, da alama dai ba a barsa haka ba, anga ‘Ya’yan masu dukiya ana Neman hanyar shige masu Amman tsoro ya hana,to wallahi ahir dinki, ko da gaske ko da wasa naji cewa kina son Mutansir kin Riga kin kade yarinya ba ma ke kadai ba hatta Shi wannan driban da wannan ma’aikaciyar asibitin,makauniyar banza da wofi,wata yar shila da ke ,ko inama abun so ajikinnan ? Mtsww.” Cewar Fatima tare da cigaba da yiwa Nafeesa wani mummunan kallo. Tunda Nafeesa ta durkusar da kanta bata dago ba,ban da hawaye ba abunda ke zuba daga idanunta, Magana ta farayi cikin ruwan Sanyi, “Habibbty Bani G…