ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 10 KARSHE END by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 10 KARSHE END by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN  BOOK 4  CHAPTER 10 KARSHE END by Sumayyah Abdul-kadir                 Www.bankinhausanovels.com.ng  Fa’iz ya ce, “Hajjah me ya sami wayarki ne? In an bugo bata shigowa”. Ta ce, “Kai don Allah rabani da wayar nan, kubi ku ishi mutum da kararraki, ko sallah yake ba zaku barshi yayi ta cikin nutsuwa ba. Ku dai ku kira mutum kiranma maras dalili. Na bude na cire batirin don ku kyaleni na huta ku da ubanninku da uwayenku”. Yayi dariya ya ce, “Haba Hajjah, ai muna jin muryarki cikin koshin lafiya dadi muke ji musamman in muna nesa. Hankalin mu na kwanciya mu cigaba da fafutukar rayuwa cikin kwanciyar hankali Hajjah”. Hajjah ta ce, “Idan ta zama dole ku kira Barau, sai ya kawo min muyi maganar a tashi amma ni ba zan iya ba. Tunda na cire batirin nan na jefa bayan gado kunnuwana suka huta na samu nutsuwar gabatar da ibadu na”. Ya ce, “Talbijin fa? Don me ba’a kunnawa alhalin abar taya hira ce? Kina kallon mutane koyaushe suna gilmawa kina kuma jin muryoyin su yafi zama shiru”. Ta ce, “R…