RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 9 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 9 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 9 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Hafsat ta yi murmushi tana ci gaba da ninke kaya, “Umma sai you kika kula’? Ai hatta idanun Nasreen irin naki ne. Ki dubi Naufal da kyau ki dubi Yaya Haidar kamanninsu ya baci. Abin ya .dade yana bani mamaki, amma da yake zama wuri daya yana sauya kamanni sai ban damu ba.” Umma ta dafe kirji da karfi tana cewa, “Ko dai Abbanku ne yayi cikin yaran nan? Wallahi ban yarda da shi ba.” Hafsat ta dubeta da mamaki, tace, “Umma me ya kawo irin maganar nan kuma? Ai ba da zuri’ar Abba suke kama ba, da zuri’arki suke kama.- Umma ta zazzaro mata manyan idanunta tana dubanta, “Kaf zuri’ata basu san komai ba, in banda Alqur’ani da Hadisai, me yasa za ki ce da zuri’ata suke kama? Kai bana son maganar nan abarta kawai.” Umma ta fada zuciyarta cike da tunani. Washcgari suka tattara suka koma Abuja, suka bar Umma cikin tunani da tarin damuwa. Kwanaki biyar ta dauka tana amfani da magungunan ta ji sauki…