RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 10 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 10 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 3  CHAPTER 10 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO                 WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG  MUN TSAYA  Sultan ne zaune a Katon dakin taron gabansa kudadene masu yawa, a cikin wata ‘yar akwati. Ya kafe kudin da kallo yana sauraren jawabin manya-manyan mutanen da suke son a kashe wani Case wanda shi yake jagoranta, haka yaga da damar da zai iya kashe Case din, Ogansa da kansa da suka shaKa masa kudi, ya amince za su wargaza Case din musamman yadda yake shirin taba mutuncin su. Yanzu Sultan ne ya rage, duk da suna tunanin Ogansa ya isa ya gaya masa ya ji, amma da Ogan ya yi masu bayanin wanene Sultan sai suka tsorata ainun, don haka suka yi shiri sosai, sannan suka tunkare shi. Kalaman Nasreen sun taimaka masa Kwarai wajen sake cusa masa tsanar damin kudaden da suke gabansa, “Allah ya makantar da kai daga haramun.” A bayyane ya ce, “Ameen Nasreen.” Ya dube su sosai yana nazarin su, “Gaskiya ba zan karbi kudinku ba, wai don kawai ina son in faranta maku in Kuntatawa wasu. …