RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 7 BY Fateeyzah mbs✍️ RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 7 BY Fateeyzah mbs✍️ *RAYUWAR CAMPUS* _(Rayuwar ‘yanci)_ *_Na Fateeyzah mbs_✍️* http://Fzahmbs.blogspot.com *_Fateeyzah@wattpad_* *_Marubuciyar_* *_Gidan nagoggo_* *_Doctor zahrah_* *_Yakin Mata (aure)_* *_Kuda wurin kwadayi_* _Tukwicine ga daukacin matan jami’a_ *_ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ_* _Ina mai baku hakurin rashin ci gaba da posting din *K’UDA WURIN KWAD’YI*, Hakan ya faru saboda busy dana shiga, sannan kuma rashin comment dinku shi yake sagar muni da gwiwar typing, don haka na dakatar dashi har zuwa lokacin da zai samu karbuwa._ *_Page 07_* Ganin Amatullah cikin shigar black abaya itama, yasa Hibba kwala mata kira, nufosu tayi tana yauki, fuskarnan tata taci uban makeup, ko da ta karaso tana duba agogon hannunta tare da cewa “ya akayi ne Hibba kika kwala mini kira haka, bayan kuma kinga fita zanyi”. “Dalla can, don zaki fita kuma ba zan kira ki ba, kawai naga mata nata fita ne sanye da Abaya, kuma kema na ganki da ita, shi yasa na kira ki don in tambayek…